27

257 16 0
                                    

I may never be able yo express my heart to you, you may have to understand my feeling your own.
 
Arjit singh

~~~~~
"Zan iya yarda da ke?"

Ya sake maimaitawa. Wani kalar tashin hankalin da bata san da zaman shi ba ya taso mata, coffeen da ta kurɓa da ke tsakanin makoshinta ya sarke ta harta hanci ta fara tari ba kakkautawa.

Amsar kofin ya yi ya na dakko mata ruwa ta sha da kyar ta na ci gaba da tarin. Kwantar da kanta yayi a kafadunsa ya na bubbuga bayanta. Lamo ta yi bayan tarin ya lafa ta na kasa ɗagowa. Jin ta yi shiru kuma ba ta ɗago ba ya kyaleta ya na ganin bata jin dadi ne. Sun dade sosai a haka kafin ya leka fuskarta ya ga bacci ta ke. Ya dauketa ya maida a gado ya lulluɓeta. Fita ya yi idan ruwan ya daga ya samo mata maganin tari, ya na tunanin sanyi ne ya kamata.

Ya na fita ta buɗe idanunta tana sakin ajiyar zuciya. Ta saka hannu ta dafe saitin da zuciyarta ke harbawa. Tayaya zai fara yi mata wannan tambayar? Yarda? Ita ɗin har abun yarda ce? Tambayar ta mata girma sosai. Za ta fi kowa jin daɗi idan ya yarda da ita, amman ta yaya? Da karyar da take lulluɓe da rayuwarta? 'Ya Allah' ta faɗi ta na runtse idon ta da karfi zuciyarta ba daɗi ko kaɗan. Ita sam ba ta san ina zata tsoma rayuwarta ta ji daɗi ba. To wai duk ba wannan ba, a lokacin da ta contract ɗin ya ƙare me zai faru?
     **************

"Me zai faru?"

Ta saki yar dariya.

"Wannan duk ba matsalata bace Ƙawa, matsalata in samu abin da nike so. Ƙarewar contract ɗin mu na nufin biyan bukata ta zo, idan kuwa haka ne me zan yi da wata Fatima? Wannan duk .ai sauki ne tsigeta a rayuwa ta."

Hajiya Hauwa ta jijjiga kai cike da gamsuwa.

"Komai ma ai ya zo gargara tun da har gashi zai je aiki da Alhaji ya ke ta muradi."

"Ya zo mana. Bari dai su dawo ai shima ya dawo ɗin, ai ya ce yana son ganin cigaban da aka samu a tsakanin su da idon shi tukunna. Wannan ba damuwa bane ni kai na na yarda Naseer ya fara son yarinyar tun da har zai iya zuwa aiki don ita, kuma ya kwashi jiki har wani gari su tafi. Idan bai son ta ko zamu mutu ba zai yarda zuwa Abujar nan ba ina faɗa miki."

"Yaushe Alhajin zai dawo ne?"

"Wannan karon ba zai daɗe ba ya ce, balle ma maganar poison din nan da nake fada miki da aka bata, ya daga hankalinshi sosai don dai ba yadda zai yi ya taho ne saboda bai kammala  abin da zai yi ba, sai dai ya rage yawan watannin. Zai yi uku a madadin shida. Sannan ban so ma ya dawo ba tare da Yaseer ba wallahi, zaman shi a cen ya isan har ga Allah"

Ta ida maganar yanayin fuskar ta na sauyawa.

"Zai dawo ki kwantar da hankin ki. Wai ya batun Yaseerah kin ce za a kawo gaisuwar aure ko?"

"Ban ko faɗa mashi ba, sai ya dawo ko idan ya kusa dawowa. Ai diyar ki tayi babban kamu in faɗa miki in ga karshen daga hanci wajen mutunniyar. Babu wanda ya san maganar ma sai Abbun nasu ya dawo tukun"

Suka cafke hannu tare da shekewa da dariya. Nan ta shiga labarta mata halin da Amina take ciki.

Suka ci gaba da tattauna kanun maganganun su, da yadda za su samu mafita.
******

"Wai Baaba yaushe tsoho zai waske Nigeria ne?"

Muryar JMan ta fito a cikin wayar. Yaseer ya yi dariya

"Ban son wulakanci Abbun ne tsoho? Kai dai ka cigaba da zama Busan kafin ya koma ka san ba yadda za ai ka zo ko garin nan, bare ka dawo gida yana kasar nan zaku iya jamewa."

"Ai duk kai ka ja min bala'in nan, da wani cen aka saka ma ya zama surikin na shi da ba a barni da boyo a yanzu ba. Yanzu meye abin yi yaushe za ka shigo Busan din?"

HAYAR SOWo Geschichten leben. Entdecke jetzt