35

247 19 6
                                    


In a fake world we call home,
the pain i feel is real.
  O beloved,thisrelationship of ours,
is like a delusion like mirage.
                  
                                 Arjit singh lyrics

~~~~

Kamar yadda ta gina kungiyarta cikin sirrin da babu wanda ya san fuskarta har a cikin yaran kungiyar, idan an fidda Yusuf da kusan tare suka faro. Zuly ma da suke ji da ita  saboda iya aikinta bata taɓa sanin wacece ko waye asalin shugaban ba, babu ma wanda ya san mace ce ko namiji i su dai kawai suna karbar umarni a wajen fearless kuma a biyasu. To a yanzu ma bata shirya tonuwar asiri ta kowace siga ba, duk da tasan kalar rainon da ta basu na ko za a kashe su sun riga sun sadaukar ga Black shadow. Meeting din su na cikin dare yanzu yana mata wahala saboda tsaro na gasken gaske da Naseer ya bazawa cikin  gidan har waje don haka ne basu fitar daren daga ita har Yusuf, gara shi tun da namiji ne ansan zai iya yawo ya kai dare, shiyasa duk wasu ayyukan dare take turashi tun da kusa da ita yake.

Tana sallamar shi ya fito ɗakin suka haɗa ido da Mum da ta fito daga dakin Abbu. Cikin mamaki ta tsaya kallon shi har ya iso inda take

"Me ya kai ka cen ɗakin?"

"Haba Mom ki saki ranki don Allah"

Ya faɗi da murmushin tsokana.

Ta sake haɗe rai

"Uhmm?"

"Mummy gaidata nayi fa, don Allah kar ki fara 'yan maganganun nan"

"Kai dai baka san ciwon kanka ba wallahi"

Ta fadi tana wuce shi, yadda take cikin farincikin nan bata fatan abin da zai bata mata shi sam. Ya yi murmushi a hankali yace

"Na san abin da nake yi Mom"
*********

Tun daga in da motarsu ta tsayà zuwa  cikin wajen cin abincin a kwace yake da jan kafet da kananun flowers farare a sama. Haka ya kama hannunta suna tafiya a hankali kamar ya ruko kwai har suka shiga ciki. Babu kowa duk kujerun ma an kwashe sai kala ɗaya a tsakiya da aka jera kayan abinci da na sha iri-iri sai kuma mai hotin dake binsu yana dallara masu hotuna da kananun videos. Wajen kawai take bi da kallo yadda fitulun ke haska kalar ja da blue   na birgeta. Tsayawa su kayi akai masu hotuna sosai kafin mai hoton ya juya ya tafi.

"Tun da bamu da hotunan biki"

Ya rada mata a kunnai. Ta yi murmushi, sai kuma ta dagula fuska ta kalli hannayenta

"Ba ayi min lalle ba"

Ya dafe bakin shi irin mamaki

"Na mance"

Ya riƙe kunnuwanshi alamun ban haƙuri. Mika hannu tayi ta sauke mashi hannun tana girgiza kai. Idanun su sarke da juna ta ce
"Ina da abin da zan faɗa ma"
"Koma meye zai iya jiranmu?"
Ta gyaɗa kai.
Ya rike hannuwanta ya kai saitin bakin shi yai missing, ya tallabo fuskarta yai missing gishinta, sannan yai mata ɗaya a kumatun dama daya a na hagu. Ya ɗago ya na kallon cikin idon ta, ta lumshe ido ta kuma budesu a cikin nashi. Ta ɗage kafafunta sai ta kasa taddo goshin shi. Ta aje kafar tana bata rai. Yai murmushi ya sunkuyo sannan ta yi mishi kiss a goshi ta dawo ta tsaya. Sai ya nuna mata labban bakin shi, ta maƙe kafaɗa ta juya. Yai dariya mai dan sauti ya na kamo hannunta. Wayarshi da bai saka silent ba tayi karar shigowar sako, sanin case din Zuly kawai ya saka fiddo wayar da dayan hannun shi da bai rike ta ba.

"Ka san wacece asalin Zahra da kake tare da ita?"

Ya yamutsa fuska. Duk yadda akayi anyi kuskuren lamba ne. Har zai kashe ya kunna wani sakon ya shigo.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now