03

288 18 1
                                    



Ta na zaune tsakar gida ta na tankaɗe garin tuwon da Baba ya shigo masu da shi. Ta saka zane da vest saboda zafin da ake fama da shi a kwanakin nan.

"Fatima"

Ta jiyo muryar Zainabu tun daga zaure. Ta juyo ta na washe baki sai kuma ta hade rai ta juya

"Tun jiya na dawo da safe amman sai yanzun za ki shigo"

"Yi hakuri wallahi bani nan lokacin da kika dawo mama ce ma ta ke faɗa mini kin ƙwalo mun kira da safe, ina gidan Yaya Mero"

"Ohoo to yanzu na ji batu"

Zainabu ta ja wata tsohuwar kula da a yanzun suka maida kujerar zama ta zauna. Murya ƙasa ƙasa ta ce

"Yanzu nan na gamu da mutunenki fa"

"Ki ce Allah"

Fatima ta faɗi ta na sakin rariyar hannunta garin da bata tankade ba ya zube a cikin tankadadden.

"Uban me ke damun ki kuma Fati?"

Inna da ke fitowa ɗaki ta faɗi cikin faɗa. Ta cigaba da faɗin

"Ɗan garin da za a yi tuwon kuma kike son zubarwa kowa ya huta ko? Daman dai da yaya aka kawo mana shi.."

"Innarmu..ban zubar ba fa, kuma ma ai ba laifi da yawa"

Ta fadi cikin son Innar ta yi shiru haka, amman sai ta wuce ta na cigaba da sababinta wanda duk ya koma kan Baba ne shi da ya kawo garin.

Zainabu ta tayata ta gyara garin suka ida tankaɗewa sannan ta ja Zainabu ɗakinsu.

"Gaya mani ya tambayi ko na dawo?"

"Eh mana, ai na faɗa miki kullum ma sai ya tambaya. Na faɗa mashi kin dawo har ya ce ma zai zo yai miki murna anjima kaɗan"

Hakan ba ƙaramin faranta yayi ba, su ka sha firar su rabi duk a kan shi ne kafin Zainabu ta wuce gida.

Bayan magriba suna zaune su duka tsakar gida suna cin tuwo Baba na ta sauraren rediyo yayinda Inna kuma ke faman ƙilga kuɗin daddawarta ta na mitar yadda ba zasu isheta zubin adashe ba wanda a zahiri da baba ta ke saboda ya ce ta bashi bashin daddawar da aka kaɗa miyar dare.

"Yanzu idan na fidda kudin adashen nan to ba zasu ishe ni sayo wata daddawar ba kuma idan na ki zubin nan tun da farar safiya zan ga tashin aike."

Baba ya kalleta ya ce

"Inshaa Allah kuɗin ki ba za su wuce gobe ba, a kwai aikin da nike saka ran zan samu in yi.."

"Saka rai dai..saka rai kullum zancenka ya na a sa rai ga wasu ba wai kai a saka a kanka ba"

Innar ta katse shi. Ta buɗe baki za ta cigaba da magana ya tari lumfashinta

"Tun da dai halak mu ke nema ai dole mu sa rai Innarsu, in dai kudinki ne zan bada gobe shikenan ko?"

Ba tace komai ba ta ƙulle yan kudin a haɓar zani ta na shirin tashi yaro ya kwaɗo sallama.

"Wai ana kiran Fatima in ji Safwan"

Inna ta dakata ta na son sanin da ga in da aka samu Safwan amman ta kasa tunawa. Sai kawai ta ce

"Ki tashi ki fita mana ki kai zaune"

Fatima da daman ta riga ta tsame hannunta a kwanon ta kalli in da Baba ya ke shi kuma ya gyaɗa mata sannan ta miƙe.

Tsaye ta iske shi a ƙofar gidansu ya jingina da bangon.

"Kaga yan makaranta..wai ashe yan candy zan ce"

Ya faɗi cikin barkwanci. Ta saka dariya ta na jawo ƙasan hijab ɗinta ta rike cikin rashin sabo da fitowa zance.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now