A cikin sati ɗayan da ta yi a gidan Dikko ta fahimci abubuwa daban daban daga yara zuwa manyan gidan, babban abin da ta lura da shi akwai ƙarancin yarda a tsakanin su duk da a zahiri akasin hakan ne. Duk wani abu da halayen su a baibai su ke. Shi yasa duk zaman ya gundure ta, ba za ta iya gane na kirkin ba duk kuwa da Mom ta saba gwada mata na ta yaran ne kawai na ƙwarai sauran ba yadda ta ke kallon su bane, to ita kan ta Mom ɗin ma abun tambaya ce ga Fatima bare yaranta.
Wani abu da ya tsorata Fatima a dan zamanta da Naseer yadda ta fahimci bai son ƙarya ko min ƙanƙantarta. Ba za ta mance ranar da suka haɗu falo da Yusuf ba a lokacin zai tafi masallaci, Yusuf ɗin yai mashi magana yai banza da shi da ya cigaba da maganar, yadda ya juyo ya kalla Yusuf ɗin sai da ya tsora ta ta wani kalar ɓacin rai ta gani kwance a fuskar shi. Duk akan lokacin da ya kira shi a waya ne sadda ya kulle ta a waje"Ka san na tsani karya, kuma ka zaɓi yi mani ita ko? Tun da har ka sani kuma ka yi hakan na nufin nesan ta kan ka daga gare ni"
Yusuf din ya ce
"Ba haka na ke nufi ba ka sani, na san ai za ka fito kuma ka tarar ba Mom ɗin bace kaga bawai don in yi ƙarya bane.."
"Then, are you trying to blackmailed me?"
Yusuf ya dafe kansa. Shi Naseer ba ya ansar uzuri akan ƙarya ko da ta wasa ce, ya na mata wani kallo na daban ne da mutanen da ke kewaye da shi su ka kasa fahimta har gobe. Ba zata manta ba ko a jiya ta ga Yusuf ɗin na ƙara bashi haƙuri kuma har yau a kwai tabon wannan abun a ranshi.
Ita tsakaninta da shi babu komai za a ce idan za ta shekara tsokanar shi banza ya ke da ita, idan ya mata magana to a kan ta shiga toilet ba ta wanke ba ne ko idan ta shafa turare sai ya bar ɗakin tun bata fahimta ba sai a jiya ya ce mata
"Ban son duk wani sauyi a ɗakin nan a ciki har da turaren yan borin nan da ki ke shafawa"
Bai jira cewarta ba kuma ya bar ɗakin. Ita dai ba ta san dalili ba. Yanzun ma wanka ta fito ta shirya cikin riga da wando da a yanzu ta fara sabawa, sai idan za ta je wurin Hajja ne sai ta ɗaura abaya bisa. Yauma su ta saka wandon dogo ne amman bai dira har ƙasa ba. Turaren ta ɗakko sai da ta shafa biyu ta tuna kashedin da yai mata jiya. Kamar an jefo shi kuma ya shigo da filet din abincin shi da zuwa yanzu ta fahimci baya cin abincin gidan.
Ya mutse fuska ya yi yana kallon ta.
"Yi haƙuri mantawa na yi"
Ta faɗi ta na ɗaga hannuwa sama. Wani kallo ya watsa mata ya juya ya fita.
'ko dai Aljanu garai?' ta tambayi kanta. A farko ta aza yana shaye-shaye ne yanzu da ta ga bata taɓa ganin shi a buge ba ko da jan idon ranar sai ta fahimci ba haka bane, amman da wahala idan babu aljani ko ɗaya ne akan rusheshen kan nan na shi. Ta na gamawa ta ɗaura a baya ta sauko, cen ta hango shi a dining ya na cin abinci ta shiga ɗakin Hajja. Ta na shiga Ikram ta ruga ta maƙale Hajja.
"Duk ki gama gudun yarinya"
Ta faɗi ta na dariya. Hajjar ma dariya ta yi. Ta samu wuri a ƙasan kafet ta zauna.
"Oh ni Sa'ade na ce ki bar zama ƙasan nan ko"
Ta yi dariya.
"Ba komai Hajja taya ki jiyyar ƙafa ni ke"
"Au kuma sai a ka ce maki kullum kafar ke ciwo ko? Idan ina son miƙeta ne da kyau ai na ke zama a ƙasan. Kun shanye ruwanku kuwa?"
"Ai ruwan nan duk ni na shanye shi Hajja, ko na bashi ba sha ya ke ba."
"Kin ga ɗan tusar ko? Je maza ki izo mani ƙeyarsa nan. Yara basu san ciwon kansu ba, boko kawai su ka tusa gaba. Idan ban da maganin nan da yadda ido na bai ganin bacci sabida addu'ar tsari ai uban su da yanzu wata maganar ake, Allah dai ya kyauta kin ji. Yi maza kira mani shi"
YOU ARE READING
HAYAR SO
General FictionBa komai a ke gani da ido ya zama gaskiya ba, wani zai iya zama ƙarya, wani kuma zallar yaudara ce da ido kawai bai isa ya tantance ba idan ya rasa taimakon zuciya!