06

247 19 0
                                    

Ba ta ga alaman tsoro a idanunta ba. Za ta yi koma meye kai tsaye kamar dai yadda ta ke buƙata, wuyar abun amincewarta ne bata hango hakan da sauƙi ba,amman me? Ita ce Rahma! Za ta yi komai don cimma buƙatunta.

Ta yi murmushi ta amsa gaisuwar sannan ta juya ga Inna

"Na ga kamar a gajiye ku ke? Ku bar aikin kawai zai fi zan baku sallamarku"

"Ki ka ce mubar aikin?"

Inna ta faɗi rai a dagule. Ita fa a ƙagare ta ke ta shiga wannan ƙaton gidan, wannan ɗakin da aka saka su shara jiya ta ke son komawa, daki ne kamar kana Aljanna(a nata tunanin) wannan kalar sanyi da ya ke fiddawa kaɗai ya isa ya saka mutum kare rayuwarshi a ciki batare da ya bukaci komai ba. Ta tusa shara ya fi a kirga duk don karta baro ɗakin har sai da aka ce ta barshi haka nan ayi mopping, shi ma ta so yi don dai bata iya ba ne ta hakura. Yanzun sai ace wani abu kar ta shiga? To kudin aikinta ma da sauran duk ganimar da za ta kwasa fa ta bayan biki? Ta kalli Mom da ke tsaye ta na nazarinta.

"Kar ki damu na ce zan baki sallamarki, yanzun akwai in da za muje mu yi magana kin ga ba a hanya ba ko?"

Inna ta kara kallonta. Da ganin matar ai ko ba'a fada ba tasan za a samu kalar sanyin dakin nan a nata dakin, kuma ma tun da za ta biyata aikinta ai shike nan, in ya so daga baya koma zuwa anjima sai ta kara dawowa ta ce abata sallamar ta yi riba biyu kenan in ji sauro.

"Mu je?"

Mom ta tamabaya.

"Eh. Su Fatima fa?"

"Sai mu sauke su a gida. Kin ga gidana a bayan gidan cen amman sai kin zagaya ta baya"

Inna ta gwale ido ta na kallon gidan duk da ya zagaya baya amman zaka shaida kalar haɗuwa da girman gidan.

"Zan dakko mota ta sai mu kaisu gida ku jira ni a nan"

Inna ta kaɗa kai ta na fatan shiga gidan. Anan Mom ta barsu ta nufi gida ranta fes! Ganin ta ɗanyi nisa ya saka Inna lallaɓawa ta bi ta a baya. Gara ta tabbatar In ba ƙarya ta ke ba kuma ta na son ganin gaban gidan ma.

Mom ta na jin alamun Innar biyo ta ta yi amman sai ta nuna kamar bata sani ba ta ci gaba da tafiya ta na murmushi a ranta. ' irinsu basu da wuyar kamu' ta ayyana a ranta.

Inna ta ƙara gwale ido da ta ga Mom ta tsaya a gaban tamfatsetsen Baƙin gate ɗin gidan, ga securities da kallo ɗaya ta basu shaidar rashin mutunci, suna russunawa gaisheta cike da girmamawa.

"Lallai wannan ai ta ci uwar uwar bikin ma, ohh ni Mariya da zan jawa kaina asara."

Ta ɗaga hannuwanta sama ta na faɗin

"Allah na gode maka da ka ke ta buda mini hanyar samu, yau naga amfanin addu'a"

Haka ta dinga sambatu har si da ta ga ana buɗe gaea alamun za a fito da mota kafin ta zabura har ta na shirin faduwa ta bar wurin. Ta na haki ta koma in da su Fatima ke tsaye ta tsaya ta na mazurai. Ba ta daɗe da tsayuwa ba motar Mom ta iso wurin. Ita da kanta ta tuko dan bata son ko ɓeran da ke cikin Dikko mansion ya gansu. Ta buɗe masu su ka shiga Inna a gaba sai yage baki take ta na hamdala jin kalar sanyin da ta ji a falon Haj. Khulsum kalar sanyin ya riga ya karu cikin burikan jin daɗinta.

Kamar yarda Caske ya fasalta mata unguwar haka ta ganta. Kasancewar mota ba zata iya shiga ɗan tsukun lungun ba ya saka ta tsaya a bakin lungun su Fatima su ka sauka, su na kallo Mom ta juya da Inna a motar.
**

Horn ta yi daidai lokacin ta tsaya gaban gate ɗin gidan Haj. Hauwa mai gadi ya bude ta shiga, ita dai Inna ta ware ido ta na kallon ikon Allah da zuwa yanzu ta ke jin kamar mafarki ta ke wai ita ce a irin wannan motar ta alfarma zaune a gidan gaba kusa da mata mai ji da dukiya kuma har za ta taka kafafuwanta inda a mafarkanta ne kawai ta ke kaita, a zahiri kuwa dai gani sai hange.

HAYAR SOWhere stories live. Discover now