INTRODUCTION

1.3K 52 5
                                    

'''Something big is coming...'''
    *ZAFIN HAWAYENA*
        Release on 1st September 2021

Assalamu Alaikum, sunana Sadiya S Adam wadda aka fi sani da SaNaz_deeyah.
   Ni marubuciyace, dana shafe shekaru ina rubutu, kuma Alhamdulillah ina godiya ga rabbil izzati daya bani baiwar da zan isar da wani saƙo ga al'umma ta hanyar rubutu.

Duk wanda yake bin littattafaina ya san mafi yawa daga labaran da nake rubutawa masu taɓa zuciya ne, da kuma ƙalubale a fannin soyayya ga wanda basu sani ba kuma yanzu sun sani.
  So a wannan karon kuwa kunji sunan littafin *ZAFIN HAWAYENA* Labari ne daya faru a gaskiya, labari ne mai cike da faɗakarwa, labarin ya faru ne akan wata marainiyar Allah shiyasa littafin na sadaukar dashi ga *MARAYU.*
    Wato zazzafan labari ne mai tafe da sabon salo, naso ace na sammaku ɗan kaɗan daga labarin, sai dai bana son in ɗanɗana muku garɗin labarin😄 Na fi so ku bi labarin tiryan-tiryan.

  Ku kasance dani a cikin group ɗina ta hanyar bin wannam link ɗin, ga kuma wanda suke Wattpad sai su yi searching SaNaz_deeyah, ku danna follow sannan ku riƙa Voting. Ga masu yin facebook kuma za ku iya samu a KARAMCI WRITERS ASSOCIATION, kuyi liking page namu sannan kuyi comment.

Ku kasance dani gobe idan Allah ya kaimu, domin labari ne da idan an fara ba tsayawa, kullum za ayi posting da yardar Allah a wannan karon babu delay. Labarin da idan kun fara karantawa ba zaku so ku daina ba, ba wai ina kuri bane😆 Na tabbatar ne, salom da tsarin rubutun na da ban ne.

*Wanda suka san SaNaz sun san cewa muddin na buɗewa novel group akwai dokokin dana ke shinfiɗawa*

1- Sallama da amsa sallama wajibine muddin kina online.

2- Mutunta junanmu, ban yarda ayi min faɗa a group ba, duk wanda yayi to tabbas zai tsinci kanshi a waje.

3- Ban yarda a turo min ko wane littafi ba inda bai ZAFIN HAWAYENA ba.

4- Na yarda a turo Link, Document na novel, amma ban yarda da duk waniabu daya danganji batsa ba, link ko Doc na littafin batsa duk wacce tayi hakan zan fiddata.

5- Ban yarda da hotunan talla ba, ban yarda da Audio barkatai ba, duk abinda bai shafi novel ba bana son shi a group ɗina.

Mu mutunta junanmu, banda cin zarafin mutum ko yana ciki ko baya ciki.

*Abu na ƙarshe kada wadda ta turo min sticker idan nayi posting, idan zakiyi comment kiyi idan ba zakiyi ba bana buƙatar wata sticker*

Ina maraba da kowa.
#MataZallah

SaNaz deeyah👄

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now