Page 14

404 49 6
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Not Edited⚠️

Book2
            '''Page 14'''

Lumshe idanu tayi, tare kwanciya kan katifarta.
  _Ya ubangiji ka zaɓa min abu mafi alkhairi a rayuwata, ina son in samu soyayyar gaskiya, daga ranar dana samu to zanyi ƙoƙarin kashe aurena in auri wanda yake sona, wataƙila dalilin haka Daddy ya gane gaskiyar lamari ya kuma yafe min._

Minal ce ta turo ƙofar bakinta ɗauke da sallama ta shigo ɗakin a kiɗime.
  Amatul'ahad tashi zaune tayi tare da cewa "Lafiya na ganki a wannan yanayi?"
   "Ina fa lafiya, makaranta ta karaɗe da sunanki, Sultan wai sonki yake a ganki dashi"
   Ɗan waro ido Amatul'ahad tayi tare da cewa "Tofah! Yanzu har an fara maganata, na shiga uku"
"Hmmm! Ai wallahi Amatul'ahad kin faɗa tarkon Sultan, Allah kaɗai zai fitar dake, ina dai baki shawara kada ki yarda kalamansa su ruɗeki"
   "Na ga alama kam akwai kalamai a bakinsa."

Sallamar da akayi ne ya dakatar dasu.
   Budurwar da ta shigo ɗakin, dukkansu basu santa ba.
  "Amatul'ahad ko?" Ta faɗa tare da zama kan ledar dake tsakar ɗakin, sannan ta ajje ƙatuwar fancy bag a gaban Amatul'ahad ɗin.
    "Saƙone daga Sultan"
"Kuma ya ce ni za ki bawa?"
  "Eh mana, ya ce na kawo miki, akwai letter a ciki." Tana gama faɗa ta miƙe tana shirin tafiya Minal ta ce "Kuma wacece?"
  "Ba damuwarki bane tunda ba gurinki aka aikoni ba" Ta faɗa tana aikawa Minal kallon banza.
   "Kin..." Da sauri Amatul'ahad ta katse Minal da faɗin "Rabu da ita Minal"
  Tsaki taja, ita kuma ta ƙara da faɗin "Ai gama yayinki Hajiya sai abi wani sarkin"
  Wucewa tayi ta bar ɗakin, Minal ta kalli Amatul'ahad ta ce "Da kin barni na mata duka ai"
   "Ki ƙyaleta, ba girmanki bane"
  "Ta ya ya zata shigo har ɗakinmu ta nemi faɗa min magana"
   "Bari dai mu ga me yazo dashi"
  Ɗaga Fancy bag ɗin tayi, ta zazzage kayan dake ciki.

Turarukane kala-kala, sun  fi kala goma, sai kuma wata envelope a ciki.
  Fitowa da ita tayi ta miƙawa Minal ta ce "Karanta mana muji"
  Karɓa Minal tayi ta fiddo da takardar ciki ta fara karantawa a fili.
   _Sunanki kaɗai idan na faɗa sai naji nishaɗi, haƙiƙa sai yanzu na gane  cewa duk matan dana so a baya basu dace dani ba, Amatul'ahad ina haɗuwa dake ƙamshin turaren dake jikinki ya tabbatar min da ke ma'abociyar turarukane shiyasa na zaɓi turaruka a matsayin kyauta ta farko da zan baki, ina sonki...kada ki biyewa surutun mutane, kedai ki zauna kiyi tunani idan har kinga na dace dake to zaki iya sona, ni dai ina sonki kuma yanzu na fara sonki._

"Kan bala'i, lallai Sultan ya cika babban mayaudari, sak irin saƙonnin da yake tura min, har cewa yake idan ya rabu dani ba zai iya rayuwa ba, najimi ƙanin ajali, wallahi kada ki yarda kalamansa su ruɗeki"
    Murmushi Amatul'ahad tayi sannan ta ce "Kin san inda suke lectures?"
   "Farin sani ma kuwa"
  "Za ki rakani gobe, kuma wallahi zan nuna masa ni ba matsiyaciya bace, zan mayar masa da tsiyarsa"
   "Kin min dai-dai" Minal ta furta tana murmushi.

Suna cikin wannan jimamin Azizat ta shigo. Labarin abinda ya faru suka bata, ta karɓi letter ta ƙara dubawa.
   "Taɓ, nagodewa Allah da bai yi min kyau irin naku da har za a yaudareku, ni babu ruwana, saurayina ɗaya tal, bani da wata damuwa"
    Dariya Amatul'ahad tayi tare da cewa "Aikuwa kema da kyaunki wallahi"
    "Amma baya ɗaukar ido kamar naku"
   "Haka dai kike gani"
"Ni dai zan baki shawara kada ki yarda da Sultan"
  Murmushi Amatul'ahad tayi ba tare da ta ce komai ba.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora