Page 10

423 55 9
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story''' _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

*Daga ɓangaren wattpad:- BintaMuhamnad8, Ambee117, Ummufaruq0,  Sszd00 wannan shafin sadaukarwa ne gareku, ina matuƙar godiya.*

Book2
            '''Page 10'''

"Aunty nace masa duk abinda ya sameki zan sanar masa"
  "Zaliha ba komai ya kamata ki sanarwa da Fauwaz ba..."
    Jin ƙarar tashin motar Zayyan ya saka ta saurin zuwa jikin window ta leƙa, gani tayi har an buɗe masa gate ya fita.
    
Juyawa tayi ta koma inda Zaliha take a tsaye.
   "Dan Fauwaz ya ce miki ki sanar dashi duk abinda ya sameni, ke bai kamata kiyi hakan ba. Zaliha bana so ace Fauwaz da Zayyan sun samu wata matsala a dalilina, dole Fauwaz yayi haƙuri da duk abubuwan da ake min, domin bashi da wata alaƙa dani a yanzu, kin ga idan ya ce zai yi fighting dan an taɓani, to za a iya zarginsa kan abinda bai aikata ba, dan haka ki kirashi yanzu ki sanar dashi babu komai kar yazo."

Kai kawai ta gyaɗa sannan ta zaro wayarta a jikin zane ta kira Fauwaz.    Tana kira kuwa ya katse, sannan ya biyota.
    "Dama cewa zanyi dam..dama babu abinda ya faru, ga Auntyn ma"

Ta miƙawa Amatul'ahad wayar.
   "Babu abinda ya faru dan Allah kar ka zo a samu matsala" Shine abinda ta faɗa cikin sanyin muryarta.

"Idan har babu matsala ya naji muryarki da damuwa"
  Ji tayi hawaye sun sake sauka a idanunta.
Bayan mahaifinta Fauwaz ne mutum na biyu da yake karantar yanayinta, kuma ya damu da ita, shiyasa itama a lokaci ɗaya taji kawai ya kwanta mata a rai, ashe ƙaddara ba zata haɗasu a inuwa ɗaya ba, ta san da Fauwaz ta aura da ta huta.

"Amatul'ahad alƙawari na ɗauka cewar zan zame miki uwa, idan har kika cutu ba zan yafewa kaina ba, a baya ma kuskurena ne, dan Allah kada ki ɓoye damuwarki gareni." Janye wayar kawai tayi daga kunnenta, sannan ta miƙawa Zaliha.

Juyawa tayi ta fita tana goge hawayen da hannunta.

                 ******

A sanyaye ta shiga parlourn gidan su Zayyan, dan daga yanda aka amsa mata sallama ma, ta san bata da wani muhimmanci a garesu.

Zayyan ɗin yana zaune ya kame a kujera, da wata baby a hannunsa da ba zata wuce shekara biyu a duniya ba.
   Mameey na zaune a three seater, yayinda wata mace ke zaune kusa da ita, sai kuma wasu yara biyu maza suna zaune kan rug suna wasa.

Ko kallon arziƙi bata samu ba, a haka ta ƙarasa parlourn.
   Har ƙasa ta tsugunna ta gaida Mameey, amma tayi shiru kamar ma bata san ana gaidata ba.
   Sake gaidata tayi a karo na biyu, shima shiru.

Matar dake gefen Mameey ta gaida, ita kuma ta amsa amma a ciki-ciki.
  Miƙewa tayi daga gabansu ta koma gefe ta zauna kan rug ɗin.

Yaran dake wasa ɗaya ya juyo yana dariya ya kalli Amatul'ahad ya ce "Aunty kinji Aman ya ce kina da kyau" Sai sukayi dariya suna rufe fuska.

Ɗayan wanda bai yi maganar ba ya taso yazo kusa da ita ya zauna "Aunty shine ya fara faɗa, nima na faɗa"

"Kai Aman dan ubanka taso kar a goga maka annoba" Matar ta faɗa tana tsawatar masa.
   Ko ma bai fahimci me take nufi ba, to tsawar ta tsawata shi, shiyasa da gudu ya tashi daga gaban Amatul'ahad.

Hannu ta saka tana goge hawayen da ba zata iya riƙewa ba

"Allah ya isa tsakanina dake, dubi yadda kika mayar min da ɗa, ɗa ɗaya tilo da nake dashi a duniya, amma sai da kika gama yawon barbaɗancinki sannan kika asirce ubansa kika sa yayi masa dole akan aurenki"

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now