Page 24

455 55 10
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

*Ina mai bawa makaranta haƙuri kan jinkirin da aka samu, abubuwane sun min yawa sosai, amma daga wannan page ɗin insha Allah zaku riƙa samun update akai-akai*

Book2
            '''Page 24'''

Suna tsaye a waje. Sultan ya kalli Marwan ya ce "Ba zan taɓa mantawa da Amatul'ahad ba, amma duk yanda na kai da jin mutuwarta sai gashi naga wanda ya fini"
     "Fauwaz ko?" Marwan yayi maganar a sanyaye.
   "Eh mana, gani nayi yanda yaji mutuwar ko mijinta bai fi shi ba"
   "Naga alamar hakan"
  "Allah yajiƙanta da rahama"
  "Amin."

*Bayan kwana uku*

A kwanaki uku da rasuwar Amatul'ahad kuwa, kullum sai Fauwaz ya ziyarci kabarinta yasha kukansa, shi kusan ma acan yake nashi zaman makokin.

                        ******

Tana hawaye ta kalli Daddy ta ce "Ya kamata kayi wani abu akai, kar ɗana ya haukace dan Allah"
   "Babu abinda ya samu Fauwaz, yana cikin hankalinsa, damuwa ce kawai tayi masa yawa, amma a hankali zai warware"
   "Mutum mai hankali yana tafiya cikin kabari ya zauna, wannan wane irin abu ne, ko mijinta bai damu har haka ba."
    "Shi ai yafi mijinta ma, domin kuwa..." Bai ƙarasa maganar ba Fauwaz ɗin ya turo ƙofa ya shigo.

Har zai wuce su, Daddy ya kirasa. Dawowa yayi ya zauna a ƙasa, tare da tanƙwashe ƙafafunsa.
 
Cikin tausayawa Daddy ya kalleshi, ya wani rame yayi baƙi. Kana kallonsa zaka san damuwa tayi masa yawa.
   "Fauwaz...! Na san kana jin rasuwar Amatul'ahad har cikin ranka, amma ya kamata ka daure kayi haƙuri, gashi yanzu har an shafe makoki amma kai kaƙi ka dawo cikin hayyacinka, a yanzu addu'a take buƙata ba zuwa kabarinta kullum ba."
   Hawaye na zuba a idonsa ya kalli Daddy ya ce "Daddy inaji ina gani kuka binneta, kuma yanzu ma kana ƙoƙarin hanani zuwa gareta? A can ma da anyi magrib masu gadi suke koroni ko bana so"

Kuka Momma ta fashe dashi, tare da saka hannu tana goge hawayen.
   "Ba kuka za ki masa ba, addua da kuma nasiha"
  "Fauwaz kaje kayi wanka ka fito na baka abinci da kaina"
   "Ni bana jin yunwa, Daddy Amatul'ahad bata ci komai ba, me kake tunanin ni zanci" Tashi yayi ya nufi ɗakinsa, yana tafiya kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki.

"Gaskiya ba zan yarda in bar Fauwaz anan ya samu taɓin hankali ba, zan ɗaukeshi mu tafi Nijar a nemo masa maganin hausa, tunda na asibitin yaƙi yi"
   "Ni ma nayi tunanin hakan, to amma sai naga gara mu ɗan tsaya mu gani zuwa wani lokacin"
  "Kana nufin na tsaya har zuwa lokacin da zai fara hauka tuburan? Gaskiya ni kam zan nema masa magani tun kafin abin yayi tsanani."
   "Yau kwana takwas da rasuwarta, dole sai a hankali zai samu nutsuwa, kar mu fara ɗorasa a kan maganin da ba na ciwon shi ba."
    "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

                    *******

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda Fauwaz ya furta tare da miƙewa tsaye.
   Mutane biyu ne suka riƙesa, suna ƙoƙarin maidashi inda ya tashi, ya fara nuna jikin ƙofar da hannu.
   "Daddy gata nan ta shigo, tana faɗin wai mu tafi"
  Daddy kallon Malam yayi sannan ya ce "Tun ranar da yarinyar nan ta rasu, bai ƙara samun kwanciyar hankali ba, kullum cikin zuwa kabarinta yake, yanzu kuma da muka hanashi, wai ta fara masa gizo"
   Ƴan addu'o'i Malamin yayi a cikin ruwa, sannan ya miƙawa Fauwaz ya ce ya sha.
  Har ya gama shan ruwan bai buɗe ido ba.
 
"A wane yanayi kake ganinta?"
  Sai lokacin ya buɗe idonshi da tun ranar da Amatul'ahad ta rasu basu ƙara dawowa yanda suke ba. Ya kalli Malam ya ce "Malam na san Amatul'ahad ta rasu, kuma ba zata taɓa dawowa ba, na san kuna kallon abinda nake a matsayin zaucewa, amma a zahirin gaskiya na sakata a rai, shiyasa har nake ganin kamar tana yi min gizo"
   "To amma ya kamata ka cire abin a rai, kayi mata addu'a"
   "Nayiwa Amatul'ahad laifuka da dama, ban sani ba ta yafe min ko bata yafe min ba, ta ina zan sameta in roƙeta gafara" Sai kuma ya fashe da kuka sannan ya riƙe Daddy "Duk wani hali da ta shiga ni dai nake zama sanadi, ta ya ya zan samu kwanciyar hankali, ban mata adalci ba, Daddy shikenan ta rasu fa, babu wani buri da ta cika, alfarmar da nake son kayi min, dan Allah ina so ka barni in cigaba da zuwa kabarinta" Kanshi ya kifa da gwiwa ya cigaba da kuka.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now