Page 26

425 48 13
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like our page on facebook👉🏻 https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow my group on facebook👇🏻 https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Please SUBSCRIBE our youtube channel 👉🏻https://youtube.com/c/KARAMCITV

Book2
            '''Page 26'''

Driver yayi parking motar a parking lot.
   "To gamu a gida, sai ki fito mu ƙarasa ciki ko?"
Murmushi tayi tare da cewa "To Daddy."
Har ta kama murfin motar za ta buɗe, ya ce mata "Tsaya...!"
Sakin murfin tayi, sannan ta mayar da kallonta gareshi.

"Zamu shiga ciki dake, ki gaisa da kowa, amma kada ki tsaya hira da kowa, har Mommynki, ki wuce bedroom ɗinki kiyi wanka, zan saka a kawo miki abinci har ɗakinki, sai ki kwanta kiyi bacci ki huta dan ki samu nutsuwa a ƙwaƙwalwarki"
   "Amma Daddy lafiya?"
   "Lafiya lau, karki damu kinji"
  Kai ta gyaɗa gami da yin murmushi.

Tare suka shiga babban parlour na gidan.
  Amatur-rahman da Salim ne kaɗai a zaune, duk sun tsura mata ido, ba wanda ya yi mata ko sannu.
  Bata wani damu ba, domin kuwa dama ta san basu jituwa a lokacin da tayi tafiya.

"Islaha wuce ɗakinki, zan saka mai aiki ta kawo maki trolley ɗinki ciki" Cewar Daddy.
  Tana ƙoƙarin wucewa sai ga Mommy ta fito. Har ta buɗe baki za tayi magana sai ta tuna abinda Daddy ya ce.
  Kallon Mommy ta ƙarayi taga fuskarta ɗauke da tashin hankali, ga idanunta sun yi jajir.
 
Juyawa tayi ta kalli Salim da Amatur-rahman, taga suma ɗin fuskarsu da damuwa. Sai a lokacin ta gane kowa na gidan fuskarshi ɗauke take da damuwa, har Daddy.

"Daddy meke faruwa?" Ta furta muryarta kamar za tayi kuka.
"Babu komai kije kiyi wanka ki shirya, su da kika gansu haka, dukkansu basu so dawowarki bane"
Duk da dai bata wani gamsu da furucin Daddy ba, amma dai ta ɗauki handbag ɗinta ta wuce side ɗinta.

Wanka ta fara yi. Tana fitowa taga an kawo mata abinci an ajje kan table dake gefen gadonta.
 
Riga da wando ta zura a jikinta, sannan ta nufi gurin cin abinci. Sai data fara buɗe fridge, taga an cika mata shi da drinks.
  Gorar ruwa kawai ta ɗauka, sannan ta ɗauki cup a saman fridge taje ta zauna.

Hankali kwance ta gama cin abinci, a lokacin taji bacci mai ƙarfi yazo mata, ta tashi ta koma saman gado ta kwanta abinta.

Ta ɓangaren Daddy kuwa yana ganin Islaha ta bar gurin ya ce "Duk wanda yaje yayi mata magana a cikinku Allah ya isa ban yafe ba" Sannan ya juya kan Mommy ya ce "Ke kuma idan har kika je kika mata magana, to a bakin aurenki"

Yana gama faɗa ya juya ya fita. Amatur-rahman ta dafe goshi tare da faɗin "Mun shiga uku, ina ma ana dawo da baya, ina ma Amatul'ahad ta dawo, wallahi tunda nake ban taɓa dana sani irin na yau ba."

Tashi tayi kawai ta bar parlour ta nufi ɗakinta. Ɗakinta na kallon ɗakin Islaha, sai da ta tsaya ta ƙurawa ɗakin Islaha ido kafin ta juya ta shiga na ta ɗakin.

Mommy na zaune kan gadonta tana waya ƙasa-ƙasa "Ta dawo fa, wallahi na san sai ta faɗi komai babu abinda za ta ɓoye, yanzu ban san ya zanyi ba"

Daga ɗayan ɓangaren ƙawarta ke faɗin "Ki ɗauki allurar da na aiko miki kiyi mata, kinga kin kashe bakin tsanya"

"To matsalar ya ce kar a shiga ɗakin, kinga idan nace sai na shiga nayi mata, ya kuma gani to kashina ya bushe"

"Ba kince ya fita ba, ki shiga kawai, abin ai ba zai kaiki minti uku zuwa biyar ba, kuma allurar quick action ce."

"Amma kina ganin babu matsala, ƴata ce fa, kar nayi mata allurar da zata kashe ta"

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now