shafi na 11

528 43 0
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Written by SaNaz deeyah_👄

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Saudat macece da tun tasowarta tana da son gayu, duk da iyayenta ba masu hali bane, amma hakan bai hanata gayu da cancarewa da ƴan kayan da Allah ya hore mata, irin na talakawa.
    Family ɗin mahaifinta akwai masu kuɗi sosai a cikinsu, sai dai irin mutanen nan ne da basu ɗauki talakawa a bakin komai ba, basu so su Saudat su raɓesu, hakan ya sa ko da Saudat taje gidansu da ita da masu aikin gidan babu bambanci.
     Tana son ɗaya daga cikin ƴaƴan masu kuɗin family ɗinsu wato Nazir, sai dai shi a duniya ma babu wadda ya tsana face ita.
    Ta ɓangaren Rafiq kuwa ya kamu da sonta tun ranar daya fara ganinta, kasancewar yana son mace mai dark skin color, ya fara sonta ba tare da ta sani ba, har zuwa lokacin data sani, sai dai ita sam bashi take so ba, sannan kuma ƙanwar Nazir tana matuƙar son Rafiq, hakan ya saka Saudat a tsaka mai wuya.

Tsohon ciki ne da ita, amma hakan bai hanata yawo kwararo-kwararo tare da wani gurgu tana tura keken guragunsa, mutumin da bata da alaƙa dashi, bashi da alaƙa da cikin jikinta, ba muharramai bane, amma ta zaɓi hakan ta kuma daure irin cin mutuncin da yake mata duk dan da wannan kuɗin barar take samun abinda zata ci, da kuma kuɗin da zata biya na ɗakin kwana a ko wace rana.
    Shin ya akayi rayuwar Saudat ta koma haka? Ina iyayen Saudat? Cikin yana da uba ko shege ne? Ina Nazir da Rafiq? Me ya kai Saudat lagos tun daga kano?
    Amsar tana cikin littafin RA'AYI NA na marubuciya Nafsal KZ

Kada ku bari a baku labari, labarine da yake ƙunshe da faɗakarwa gami da nishaɗantarwa, ku garzaya ku nemi naku, zaku iya tuntuɓatar ta WhatsApp da wannan number 07038363997 domin shiga group ɗin RA'AYI NA FANS CLUB ku garzawa ku karanta sannan ku min godiya😊

*Duk wanda yayi comment in har ina group ɗin ina gani, kuma ina godiya, abubuwane suka caɓe min shiyasa bana samu inbi ko wanne inyi reply, ku sani comment shine ƙarfin gwiwar ko wane/ce marubuci/ya, dan haka ina jindaɗin comments ɗinku kuma ina yinku sosai🥰*

Book1
            '''Shafi na sha-ɗaya'''

Hannu ta saka ta murje idanunta sannan ta kalli Zaliha ta ce "Miƙo min wayata, tana kan mirrow"
   "To Aunty" Zaliha ta nufi jikin mirrow ta ɗauko wayar, sannan ta dawo ta miƙa mata.
    "Idan ba damuwa ina so na tambayeki"
   "Kiyi tambayarki." Amatul-ahad ta bata amsa a taƙaice.
     "Wannan baƙon da yazo gidan nan, kamar na taɓa ganin hotonshi a cikin wayarki, to tun ɗazu ina ta tunanin ina na sanshi, sai yanzu na tuna"
     Yunƙurawa tayi zata tashi, Zaliha tayi saurin tahowa zata ɗagota, da hannu Amatul-ahad ta dakatar da ita "Barshi kawai."
      Tsayawa tayi tare da matsawa baya kaɗan, kanta a ƙasa ta furta "Kiyi haƙuri Aunty, Allah ya huci zuciyarki"
    "Ina buƙatar hutu." Amatul-ahad ta faɗa tana kallon Zaliha. Juyawa Zaliha tayi a sanyaye ta fita, tare da ja mata ƙofa.
   A bakin ƙofar ta tsaya tana kallon ƙofar a ranta ta furta _Duk yadda akayi sun san juna, to amma wace alaƙa ce tsakaninsu? Naga Aunty tana masa kallon banza, ita tana da zurfin ciki, ba yadda za ai kaji cikinta, bare ka bata shawara ko wani taimako._

Zaliha na fita Amatul-ahad ta fashe da kuka mara sauti, zuciyarta zafi kawai take "Inda na san Fauwaz zan gani, wallahi da ba zan fita ba, gara in zauna anan Zayyan yayi min duka na rashin fita da nayi. Lallai Fauwaz har yana da ƙarfin halin bani haƙuri." Ta furta a fili tana  ƙara jin saukar wasu hawayen.

_Wannan baƙon da yazo gidan nan, kamar na taɓa ganin hotonshi a cikin wayarki, to tun ɗazu ina ta tunanin ina na sanshi, sai yanzu na tuna._  Furucin Zaliha ne ya dawo mata, da sauri ta ɗauki wayarta  ta fara bincike dan ta rasa a ina hotunan Fauwaz suke da har Zaliha ta gani.
    Bata ga komai ba, dan haka gaba ɗaya tayi deleting gallery nata, ita dama ba hoto take ba a yanzu, sannan wanda take dasu a wayar ma ba kalla take ba, wayar ma ba da ita take amfani ba, keypad ɗinta da ita take komai, waccan kuwa ko sim card babu.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now