Shafi na 8

510 38 0
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Written by SaNaz deeyah_👄

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
   _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

_Comments ɗinku shine abinda ke ƙara ƙarfafani wajen sambaɗo page mai tsayi, ku cigaba da gashi, ina godiya._

            '''Shafi na Takwas'''

Kallonshi tayi tare da cije leɓe.
  "Kin ga Malama da Allah ɓace min da gani, domin bana son ganinki, kije duk inda za ki samu kuɗin tafiya ki samu, ina kwaratan naki suke?"
     Bata ce komai ba kawai ta wuce, har ta kai ƙofa ya yi mata magana "Keee!" Da sauri ta juyo ta kalleshi.
   Tasowa yayi ya zo inda take tare da zura hannunsa a pocket. Kuɗi ya ciro ya ƙirga ya watsa mata sannan ya juya ya tafi.
  Kallonshi kawai take rai a ɓace, har ya ɓacewa ganinta, sannan ta sunkuya ta ɗauka.

                ******

Yana kwance kan gadonshi hannunsa riƙe da waya manne a kunnensa, da alama wayar mai muhimmanci ce yadda ya nutsu yake amsa wayar.
    Bayan ta shigo, gefen gado ta samu ta zauna tare da ɗora hannunta bisa haɓa, duniyar tunani ta lula wanda har ya ƙarasa wayar bata ma sani ba.
   Kafaɗarta ya dafa, tayi saurin ɗagowa ta kalleshi "Ya kamata ki rage damuwa."  Murmushi kawai tayi tare da cewa "Yaya wallahi ina matuƙar tausayin Zayyan har cikin raina."
   "Na san da haka, amma ya kamata ki daina wannan tunanin, kiyi ta addu'a Allah ya zaɓa miki wanda ya fishi zama alkhairi"
   "Amin, insha Allah zan cigaba da addu'a"
  "Yauwa haka nake son ji"
  Murmushin yaƙe kawai tayi, sannan ta gyara zama ta ce "Yaya dama nace maka zamuyi magana akan Aunty Sumayya gashi har ta kusa dawowa."
     "Indai maganar ba zata kaimu awa guda ba, ai har ma gama kafin ta dawo"
  "Okay.  Yaya wallahi Aunty Sumayya tana matuƙar ƙaunarka, kai kana ɗaukar abin a matsayin shaƙuwa amma ita a matsayin soyayya ta ɗauke shi"
     Tashi yayi ya dawo gefen gadon kusa da Ramlat ya zauna "Meyasa kika ce haka?"
   "Jiya bayan ka ce budurwarka zaka fara zanawa, tun a lokacin na fahimci yanayinta ya canza, so bayan na shiga ɗakina nayi wanka, har na zura kayan bacci, kawai zuciyata ta raya min inje ɗakinta, ina tura ƙofar na tarar da ita tana kuka, amma sai ta maze ta ce min ba kuka take ba, kuma hoton dake hannunta nakane, frame ɗin dake ajiye a side drawer nata. Wannan abu dana gani ya tabbatar min da batayi bacci ba a daren jiya"
   Ajiyar zuciya Fauwaz ya sauke tare da faɗin "Ramlat nima na fara tunanin haka, amma ina ƙara jaddada miki cewa Sumayya ba tsarana bace, kuma ma ni har ga Allah bana sonta, ban taɓa jin sonta a raina ba, akwai wadda nake so kuma ni bani da ra'ayin auren mata biyu, fara soyayya da ita bashi da amfani"
    "Amma Yaya dan Allah ka duba lamarin nan, ni na san zafin so da kuma ɗacin sa, muddin aka rabu da masoyi"
    "Ai ni bamuyi soyayya ba, kin ga ɗacin da zataji kaɗan ne, ba kamar in ce ina sonta, kuma inzo in fasa ba, kin ga na cutar da ita kenan, sannan zan lalata zumunci. Tunda har bata faɗa ba, ki ƙyaleta a haka kada ma ki nuna kin  gane hakan"
   Shiru tayi na wasu lokutan kafin ta ce "To shikenan, amma ina fatan a gaba ka sota"
  "Za ta samu wanda ya fini komai"
     Murmushi iya na kan leɓe shi Ramlat tayi.

               ******

Tana tsaye bakin titi tana jiran Napep, sai ƴan kalle-kallen titi take.
   Wata walfefiyar mota ce tazo ta wuceta, a hankali ta fara dawowa, ganin bata ganin na ciki ya saka ta kauda kai kamar ma bata ga motar ba. "Amatul-ahad..." jin an ambaci sunanta ne ya saka ta juya tana kallon cikin motar, lokacin ta ƙarasa zuge glass ɗin.
   Mamaki ne ya cikata ganin wadda ke zaune a gefen driver. "Nashwa!" Amatul-ahad ta furta cike da mamakin ganinta.
    "Kin ɓata ɓat"
"Ke dai kika ɓata, kin yi kuɗi kin mantani"
  "Haba wace ni na manta dake, ina zuwa haka?"
  "Wallahi zan je unguwa ne"
  Juyawa Nashwa tayi ta kalli wanda ke driving ɗin "Itace Amatul-ahad da nake baka labari." Sai a lokacin ya ce "Sannu fa"
"Yauwa sannu" ta bashi amsa.
   Nashwa cikin murmushi ta ce "To shigo mu rage miki hanya mana"
   "A'a ku barshi Nashwa, zan hau Napep"
   "Dan Allah ki shigo mana"
  "Mijina ya hanani hawa motar wani"
  "Ai dama na san tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi."
  "To kin gane ashe, ku tafi kawai na gode"
  "A'a ba ayi haka ba, bari ni na sauka, saboda dama akwai maganar da zamuyi."
  Kallon saurayin tayi ta ce "Baby dan Allah zan ɗan ga ƙawata, daga nan zan wuce gida, sai kazo ko"
  "Okay Baby take care"
  Sauka tayi daga motar shi kuma ya wuce ya tafi, a dai-dai lokacin Amatul-ahad ta tari Napep.
   Tare suka shiga da Nashwa, sai da ya tambayi ina za'a kaisu ta faɗa sannan ya fara tafiya.
  "Amma fa drop ne, kada ka ɗauki kowa, sannan ka riƙa tafiya very slow saboda magana zamuyi kafin mu isa wajen" Cewar Nashwa.
   "Gidan surukaina zanje fa"
   "Babbar magana, lafiya dai ko?"
  "Eh to ban sani ba, ni dai kawai ya ce min Daddynshi na kira"
  "To da sauƙi tunda Daddynshi ne, amma kuma Amatul-ahad ke da zan ga kina driving sai na ganki a ƙasa tafe, ina motar taki?"
   "Daddy ya ƙwace, kema kin san ba zai bar min ba"
   "Amma duk kuɗin mijinki ya kasa saya miki mota, kuma ma ai akwai motoci a gidanki meyasa ba zaki ɗauki ɗaya ba, ba girmanki bane, kin ga yadda kika rame kuwa, ga wasu ƙuraje kamar na cizon sauro a fuskarki, da fuskarki very smooth abin sha'awa amma yanzu kin ganki kuwa."
    "Haba Nashwa, kefa mai bawa wani labarin yadda rayuwata ta koma ne."
   "Na ɗauka zuwa yanzu komai ya lafa"
  "Ina fa, kin manta fa washe garin ranar da aka kaini gidan Zayyan ba kinzo keda Zee ba, amma kiga irin korar da Zayyan yayi muku, to wallahi Nashwa irin baƙar wuyar da nake sha a gidan Zayyan, sai naji  wuyar dana sha a gidanmu ma ba komai bace"
   "Taɓ lallai kin shiga tsaka mai wuya, to ni wallahi ina mamakin yadda kika samu wannan ciwon, dan ana ce mana kina da HIV ƴan clique ɗinmu duk munje an gwada mu, amma mu bamu da ita, Amatul-ahad garin ya? Ni duk fa samarina sai da suka gujeni saboda ke, shiyasa na nutsu na tuba domin ke darasi ce a gareni, kinga wanda muke tare dashi, shine wanda zan aura, har ma an saka bikinmu wata shidda"
    "Allah ya kaimu ya kuma sanya alkhairi"
  "Amin Amatul-ahad, bari na karɓi numberki ma riƙa gaisawa ko?"
    "Amma sai dai ni na kiraki, domin idan kika kirani Zayyan na nan akwai matsala fa"
   "Sai mu riƙa haɗuwa ta WhatsApp ko?"
    "Ai bani da babbar waya, keypad ce a hannuna"
   "Taɓ haba ƙawata, shikenan duk wani jindaɗi ya ƙare miki kuma kike zaune, to ai gara ki koma rayuwarki ta baya ga babbar waya ga mota"
    "Nashwa kenan, ni bana so a riƙa ma tuna min irin rayuwar da nayi a baya bare har inyi sha'awar komawa, a yanzu haka ma ina roƙon Allah ya yafe min"
   "To Amin, sai kiyi ta zama a haka ai" Nashwa ta faɗa tana taɓe baki. Amatul-ahad kuwa girgiza kai kawai take, tana mamakin yadda Nashwa yanzu bata ko kunyar furta tsauraran kalamai a kanta.
  "Kin ga bari ni na sauka anan, dan kin san ba zan bi ki gidan surukai ba"
   "Okay to ba damuwa, ki bani number"
   "Barta kawai" ta sauka tana faɗin "Mai Napep nawane kuɗin"
    "No ki barshi kawai zan biya"
   "To shikenan, ki gaida maigidanki" Bata ce komai ba har Napep ya figa suka tafi.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now