Page 4

456 48 4
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Book2
            '''Page 4'''

Yana shiga parlour Momma da Ramlat suka miƙe tsaye.
 
"Subhanallahi! Me nake gani haka a jikinka kamar jini?" Momma ta tambaya tana ƙara dubansa.

"Am...dama wasu ne suka samu hatsari a machine, so sai na taimaka musu na kai su asibiti" Ya samu kan shi da yin wannan ƙaryar.

"Wallahi Yaya ka bamu tsoro, ai sai mu yi tunanin ko wani abu ne ya sameka"

"Babu komai fa, yanzu ma zanyi wanka na fita masallaci"

"Kai da baka da lafiya ma, ina kaje?"

"Momma abokina ne ya kirani, so shine naje"

"Zayyan...?" Ta yi tambayar tana kallonsa.

Kallon Ramlat yayi ya ga mood ɗinta har ya canza, Momma ya kalla sannan ya ce "Ba Zayyan ba, wani friend ɗina ne da ban"

"Ni dai a iya sanina baka da wasu friends a nan, Zayyan ne kawai friend ɗinka, so ban san yaushe  kayi sabbi ba"

"Momma sai dai kice Zayyan shine intimate, amma dai ina da friends a garin nan"

"Oh Allah, ni kam Fauwaz Allah ya yaye maka. Maza je kayi wankan" Ta faɗa tana zama, itama Ramlat zama tayi ta cigaba da yankan farce.

Yana shiga bedroom ɗinsa ya tarar da Sumayya kwance a kan gadon na shi tayi ruf-da-ciki. Shigowarsa ta saka ta saurin tashi zaune ta tsura masa ido.

"Jini...!" Ta furta da mamaki.

Bai ma kulata ba, kawai buɗe closet yayi ya ɗauki wata jallabiyar ya shige bathroom abinsa, dan ya ga bata da niyyar fita kuma shi wanka yake son yi.

Yana fitowa ya tarar da ita bakin gado ta rufe fuska da hannayenta tana shashsheƙar kuka.

"Kin ga Sumayya dan Allah kada ki saka su Momma su shigo su yi tunanin wani abu nayi miki, dan basa jin ma kina nan ɗakina."

Cire hannayen ta yi idanunta sun kaɗa sun yi jajir ta kalleshi ta ce "Oh kenan ba wani abu kayi min ba, barina kai fa a ɗakin nan tamkar ba mutum ba, ka tafi wajen wata banza"

"Amatul'ahad ɗin ce banza?"

"Eh itace, ni banza ma ta fita a gurina, kuma ka sani wallahi ko mene zai faru ba zan dubata ba muddin asibitin da nake aiki ka kaita, wallahi na gwammace ma a koreni daga aiki ya fi min dubata"

"Kenan dama ba dan taimakon al'umma kike aikin ba"

"Koma mene za ka faɗa ka faɗa Fauwaz, yau ni dai na fito fili na faɗa maka sirrin zuciyata, ina sonka Fauwaz kuma na san kaima ka daɗe da gane hakan, amma sam kaƙi tsayawa ka saurareni"

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Sumayya..."  "Dakata Fauwaz! Muddin ba cewa za kayi kana sona ba dan Allah karka faɗi wata maganar."

Kallon-kallo suka tsaya yi kafin ta miƙe ta sake faɗin "Daga nan har zuwa sati guda na baka damar kayi tunani, idan kuma kaƙi fidda gamsashshiyar amsa, to ni da kaina zan je in faɗawa Daddy cewar idan baka aureni ba sai dai na kashe kaina"
Tana gama maganar ta miƙe ta bar ɗakin. Da ido kawai ya bita.

Tana jan ƙofar yayi sauri ya je ya sakawa ƙofar key.

Dawowa yayi ya zauna kan sofa tare da dafe goshi.
   _Ƴammatan da suka ce suna sona basu da adadi, amma cikinsu waɗan da naso nayi soyayya dasu Manal da Amatul'ahad ne, ita Manal a yanzu tana can tana modeling, ga bin maza, yayin da Amatul'ahad tana nan tana shan wahalar rayuwa, meyasa sai ni? Meyasa mata suke fitowa su faɗa min ƙarara cewar suna sona? Ya kamata nima dai ko sau ɗaya ne in ga wata in  fara furta mata kalmar so, hakan zai sa Sumayya ta rabu dani idan taga na samu wadda zan aura._

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now