Page 15

429 47 9
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

Book2
            '''Page 15'''

Idanunta ta lumshe tare da dafe saitin zuciyarta da hannu. Ɗan murmushi kaɗan take, wanda hakan ne ya bayyanar da sirrin zuciyarta.

"Ina fatan na samu karɓuwa a gurinki" Ya faɗa idanunsa a kanta.
  Da sauri ta ɗago ta kalleshi, ta ma manta cewa tana tare dashi ne.

Ɗan taɓe baki tayi sannan ta ce "Sai ka bari inyi tunanin akan maganganun da ka faɗa"
   "Na baki damar yin hakan, amma kafin nan ina roƙon alfarmarki da ki bani contact ɗinki, kuma ina son zama makusancinki ma'ana aboki, kafin ki yarje min"
   "Zaka iya samun contact kaɗai, amma ɗayan batun ban maka alƙawari ba"
   "Hakan ma yayi"
Hannu ta miƙa, shi kuma ya bata wayarshi.
    Juya wayar tayi a hannunta tana murmushi, kafin ta rubuta masa phone number ɗinta.

                    ******

Juya baya tayi, gami da harɗe hannayenta a ƙirji.
   "Kin ce kina son magana dani, kuma nazo kin juya baya.
   "Wacece Amatur-rahman kuma?"
 
Gabanshi ba ƙaramin faɗuwa yayi ba. Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa "Kai nake sauraro"
  "Sumayya ni babu abinda ke tsakanina da ita, kawai sunzo nayi masu zane amma ba..."
  "Kada ka ɓoye min komai Fauwaz, idan ba budurwarka bace zatayi maka ƙarya ne"
    "Taya kike faɗar magana haka"
  "Dole in faɗa, duk da an saka mana rana amma bana samun wata kulawa daga gareka, bani da muhimmanci, da ka nuna kulawarka a kaina, da babu wacce ta isa tazo har tayi min rashin kunya tana faɗa min ita budurwarka ce, kuma dole in rabu da kai"
   "Ta ce tana sona, na ce mata ina da wadda aka saka min rana da ita, impact, ni na sanar da ita cewa ta daina bibiyata ma, saboda..." Shiru ya ɗanyi yana kallon fuskar Sumayya da take zubda hawaye.

"Sumayya ni nace ina sonki, ba zan taɓa wulaƙantaki ba"
  "Ai nina fara cewa ina sonka, kafin kace kana sona, wannan daliline ya sa ko wace banza sai tayi min rashin ɗa'a a kanka"
   "To kiyi haƙuri, zan ɗauki mataki akan Amatur-rahman, in Allah ya yarda hakan ba zata ƙara faruwa ba"
   Juyawa tayi ta shige cikin gidan tana matsar hawaye.
     Rai a ɓace ya nufi inda motarsa take.

  Yana fara driving ya kira Amatur-rahman a waya, ya sanar mata cewa yana hanyar zuwa gidansu.

Ta ɓangaren Amatur-rahman kuwa suna gama waya ta miƙe, dama tayi wanka, dan haka kawai cire kaya tayi ta sake zura wasu. Jikin mirror ta tsaya ta fara tsara kwalliya a fuskarta.

Islaha ce ta turo ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama. Tsayawa tayi daga bakin ƙofar, yayinda Amatur-rahman ta juyo tana kallonta.
    "Gobe zan bar muku gidan, ƙasar ma gaba ɗaya ma zan bari, sai ki kwaɗa ki cinye" Islaha tayi maganar tana bin Amatur-rahman da kallon banza.
  "Ni kike faɗawa baƙar magana?"
"To wacece ke da ba zan faɗa miki ba? Shin ke kina bawa Amatul'ahad girmane da har kike tunanin zan baki?"
  Ɗan murmushi Amatur-rahman tayi tare da cewa "Ai gobe zan ga wanda zaki yiwa tsiwa"
  "Ai zan dawo ba acan zan dawwama ba, kuma ki sani wallahi duk abinda akawa Amatul'ahad sai Allah ya saka mata cikin gaggawa"
   "Wannan kuma in kin isa ki samu Mommy ko Daddy ki faɗa musu"
  Tsaki Islaha taja sannan ta fita daga ɗakin taja ƙofar da ƙarfi.

*Few Minutes Later*

Suna tsaye a farfajiyar gidan, sai kwarkwasa da iyeyi take, ita a dole tana gaban saurayi.
   Shi kuwa har a lokacin babu walwala a fuskarsa.
  "Dan Allah mu shiga daga ciki"
   "Ba zama ya kawoni ba, shin a ina kika samu number Sumayya kika kirata?"
    Murmushi tayi sannan ta ce "Oh shine naga ranka a ɓace? Mu shiga ciki to, sai nayi maka bayani"
   "Ba buƙatar haka, Amatur-rahman ki sani cewa Sumayya an riga an  saka ranar aurena da ita, ke ko babu maganar auren Sumayya a kaina, to ba zan iya soyayya dake ba, saboda ke ƙanwar Amatul'ahad ce"
    "Amatul'ahad kuma...? Dama ka santa ne?"
  "Na santa kuma ni masoyinta ne a baya, kuma babu yadda za ayi in zauna kina tsarani bayan muzgunawar da kukayi mata, dan haka kada ki sake nemana, domin ba zaki taɓa samun soyayyata ba, ki daina shirmen kiran wadda zan aura."
  Wucewa yayi ya shiga motarsa, ita kuma ta tsaya cak kamar bishiya.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz