Page 25

427 51 4
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

*_Assalamu Alaikum, ina bawa ɗumbin masoyana kuma makaranta wannan littafi haƙuri, a bisa jinkiri da aka samu, amma insha Allah daga yanzu zaku cigaba da jina_*
 
_Wannan shafin sadaukarwane ga duk wani masoyin littafin ZAFIN HAWAYENA._

Book2
            '''Page 25'''

Sai daya sha kuka sosai sannan ya goge hawayenshi, idanunsa gaba ɗaya sun zama jajir, saboda kukan da yayi, da kuma tsawon lokacin daya ɗauka yana yi.
   
Motarsa ya shiga, sannan yayi mata key.
Yaquba ya buɗe masa gate ya fita a guje.

"Rayuwa kenan, kai duniya abar tsoro" Yaquba ya faɗa lokacin daya dawo kan benci ya zauna.
  Sani kallonsa yayi, sannan ya ce "Baiwar Allah'nan tana da maƙiya da yawa, wallahi naji mutuwarta har cikin raina, ji nake kamar ƴar uwata ce ta rasu, ni Zaliha ma nake tunani ko ya zataji?"
   "Bata san anyi rasuwar ba?"
    "Bata sani ba, ai tana garinsu, da muna waya da ita, amma yanzu ko na kira a kashe"
   "Aikuwa duk ranar da taji sai tasha kuka, dan na lura tana ƙaunarta"
  "Sosaima, ni ai na sani, tunda tare muke zaryar zuwa asibiti, amma fa Yallaɓai yayi babban rashi, dan zai yi wuya ya samu mace mai haƙurin marigayiya"
  "To ai baya sonta, gashi ta tafi"
  "Yaquba kaima fa baka sonta"
  "Me tayi min da zan tsaneta?"
  "Ranar nan wallahi naji haushinka sosai, da ka nuna wannan bawan Allahn, dan ya cece ta"
   "Ni fa akan aikina nake, tambayata akayi, kuma na faɗi abinda na sani"
   "Ko nan gaba karka ƙara, wanda ya rufa asirin wani, shima Allah zai rufa nasa"
   "Nagode da shawarar da ka bani, ita kuma Allah ya kyautata makwancinta"
  "Amin ya rabbi."

                       ******

Kallonshi ya sakeyi a karo na biyu, sannan ya ce "Yanzu me kake so nayi maka?"

Shiru Zayyan yayi yana mai sauke jiyar zuciya, zuciya kafin ya ce "Tun ranar da Amatul'ahad ta rasu, har yau banyi baccin awa biyar ba, na kasa bacci saboda tarin damuwa, gaba ɗaya gidana ya fara bani tsoro,   idan na fito sai na riƙa ganin kamar zan ganta, naje asibiti an duba BP ɗina, likita ya ce jinina yana hawa yana sauka."

"To ka godewa Allah ma,  tunda yana sauka idan ya hau ɗin" Daddy ya faɗa, lokacin kuma ya jawo wayarsa yana latsawa.

Sai lokacin Mameey ta ce "Zayyan fa ɗanka ne gudan jininka, ɗanka ɗaya tilo, amma kake masa irin wannan muzgunawar, yarinyar nan fa ta rasu, amma ko jiya munyi waya ya ce min ko ɗakin ya shiga wani lokacin sai ya ganta, ko a parlour yana zaune yaga giccinta, ya kamata ka san abinyi, ayi masa sauka a gidan ko kuma a canza masa."

Kallon Mameey yayi sannan ya ce "Ba yana da wani gidan ba? To ai yana da damar komawa, batun sauka kuma, zai iya ɗaukowa ayi masa, ba dole sai ya sameni ba"

"Haba Alhaji, wannan wace irin magana ce kakeyi akan ɗanka. Ni ban san laifina ko laifin Zayyan ba da har baka son farin cikinmu, haka ka aura masa yarinyar da ta gama gantali har da cutar HIV, sannan kace muddin bai bata haƙƙin aure ba, baka yafe masa ba, yanaji yana gani yayi maka biyayya, yanzu kuma ta rasu, tazo tana masa gizo, amma sam ka kasa ɗaukar wani mataki akai."

Ajje wayar yayi, sannan ya ce "Anzo dai-dai gurin da nake so azo, dama jira nake sai ranar da kuka yi magana in zayyane muku komai kuji."
  Gyara zama yayi, sannan ya cigaba da cewa "Ba ni ne na dawo da Amatul'ahad gidan nan ba, ita da kanta ta dawo, ta kuma sameni tana kuka ta ce min mahaifinta ya koreta, saboda abubuwan da takeyi a ɓoye, yanzu kuma ƴan gidan suka tona mata asiri, ta sanar min cewa step mom ɗinta ita take bata key ta buɗe ƙofar baya ta fita. Sai ta ce min ‘Daddy na san abinda nakeyi babu kyau, amma idan banyi ba, ji nake kamar zan mutu, kuma ita Mommy ita take goya min baya, Daddy dan Allah ka kulleni anan, ta yadda ba zan iya fita ba, sai kuma ka nemo koma waye ka aura min, saboda ni kaina bana son abinda nake yi, amma na san idan nayi aure mijina ya san halin da nake ciki, zai riƙa kulleni a gida ya hanani fita.’ Kunji yadda mukayi da ita, kuma baku taɓa sani ba sai yau.
    Bayan ta zauna a gidan nan, sai naga to waye zan ce ya aureta? Wanda zai iya da halinta, kafin kai, sai dana samu mutum uku amma suka ƙi yarda, kowa faɗa yake ai ina da ɗa namiji, in aura mata shi mana, ganin haka ne ya saka na  sameka kuma na maka dole a kanta.
   Na san akwai wacce kake so a lokacin, shiyasa ban maka maganar ba, amma dana ga babu wanda na isa dashi sai kai, shiyasa na kiraka na haɗaku, kuma nace umarni ne ba shawara ba.

Bayan kunje anyi gwajin cutar ka dawo min da result cewa Amatul'ahad tana da HIV, sai hankalina ya tashi. Na tuntuɓi mahaifinta, sai ya ce ai kaima ka je ka karɓi wanda family doctor ɗinsu yayi mata, wanda shima result ɗin ya bada possitive.

Duk da haka hankalina bai kwanta ba, na saka ta shirya na ɗauketa, na kaita asibitoci har uku, wanda ban san kowa a cikin asibitin ba, haka itama. Anan aka mata test, washe gari da kaina na karɓo results ɗin, kuma duka ukun negative ne. Na duba sosai, na kuma ɗauka a wayata na turawa mahaifinta dan ya gani cewar ƴarsa bata da HIV, mun dawo gida na kiraka gaka ga Amatul'ahad ga kuma Mahaifiyarka, na miƙa maka result na farko nace ka duba. Kana dubawa sai kace ai possitive ne, na karɓa na duba sai kawai naga possitive, na ɗauko wayata na duba wanda na ɗauka naga shi kuma negative, hankalina ya tashi sosai, kawai sai na fasa nuna maka sauran.
      Sai da nayi kwana biyu ina nazari, daga nan na gano lallai anyi maka asiri ne saboda anji zaka aureta.
   Lokacin da Amatul'ahad ta faɗa min cewa ita ta san step mom ɗinta ce tayi mata asiri har faɗa nayi mata, amma lokacin dana ga result ya canza sai na gaskata zancenta, domin ni da kaina naje gidansu, kuma daga step mom ɗinta, sai mahaifinta su kaɗai ne suka san zata aureka, dan har a lokacin ina cewa mahaifinta dole wata rana zai gane gaskiya.

Sai na lura lallai so take Amatul'ahad ta shiga duniya, hakan ta saka nayi maka dole ka aureta, kuma na san baka son ta, shiyasa nace maka ban yafe ba idan har baka bata haƙƙin aure ba.

Zayyan ni mahaifinka ne, ba zan taɓa yin, ko son abinda zai cutar da kai. In Amatul'ahad na da cutar HIV, to ba zan taɓa aura maka ita ba. Amma sai ka kasa ganewa, bayan aurenku ma ai ta shiryu bata fita yawan banza, domin munyi waya tana hamdala ta faɗa min cewa ai yanzu ko sha'awar yawon batayi, nace mata ta cigaba da addu'a.
  Amma ashe kai muzguna mata kayi tayi, ita kuma zurfin ciki yasa taƙi faɗa min.

Zayyan taya ya kake ganin zaka daina ganin gizo, ai ka cutar da baiwar Allah shiyasa ka kasa zaman lafiya, amma a zahirin gaskiya ba ita kake gani ba, kawai imagination ne. Ni ban san abinda zan ce maka akan Amatul'ahad ba, amma dai abinda na sani shine, kayi rashin mace mai haƙuri, sai bayan data rasu kake faɗar abinda kayi mata. To ni me kake so nayi? Kuma ga uwarka nan zaune na tabbatar ita take zuga ka, amma ni da na san abubuwan da kayi mata har sun kai haka, da tuni na raba aurenku dan babu wani amfani.

Ni a haka ma ban ga wani jimami da kake ba, kaje kaga Fauwaz yanda yake neman haukacewa a kanta, matarka, amma wani ya fika damuwa."

Daddy na gama maganar ya miƙe, tare da ɗaukar wayarsa yayi side ɗinsa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda Zayyan ya faɗa, wasu zafafan hawaye suka samu damar zubowa daga cikin idanunsa.
   Mameey kuwa ta narke a gurin, ta kasa cewa komai.

                       ******

"Idan kika dawo gareni, nayi alƙawarin cika miki duk wani burinki, zan saka ko ta halin ƙaƙa Zayyan ya sakeki, ni na aureki, domin ni kaɗai na fi dacewa dake, kuma nine wanda zan baki duk kulawar da kike buƙata."
Fauwaz yayi maganar idanunsa a lumshe suke, yana kwance a makeken gadonsa.

"Irin waɗan nan surutan sune kullum yake yi, mun samu wani Malami yazo nan har gida ya duba shi, kuma ya bada wasu magunguna, so sai nayi deciding bari na kiraka ka duba shi ko kai zaka gane abinda ke damunsa." Daddy ya ƙarasa maganar yana kallon Likita.
   "Depression ne, kuma yana da buƙatar kulawa, idan akayi wasa zai iya zaucewa"
  "To Doctor me kake tunanin zamuyi a halin yanzu?"
   "Eh zamu kaishi can asibitina, dan gaskiya barinsa a gida da akwai haɗari, acan kuma zamu ɗorashi kan magunguna da kuma wasu ƴan dabaru in Allah ya yarda zai samu sauƙi."

Sai lokacin Momma ta taso daga ina take ta koma kan gado ta zauna, tare da dafe goshi.
   "Ta damu sosai, dan itama jininta har hawa yake akan wannan ciwo na Fauwaz" Daddy ya sake maganar.

Likita ya kalli Momma cikin murya ta kwantar da  hankali ya ce "Karki damu Hajiya, da yardar Allah zai warke garas, ku cigaba da masa addu'a"
  Kai kawai ta gyaɗa.
    
*Bayan kwana huɗu*

Horn da kuma ƙarar buɗe gate ne ya ɗagawa Mommy hankali.
  Daga kan gadonta da take zaune ta miƙe, da sauri tare da buɗe labulen window.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda ta faɗa tare da yin zaman dirshan akan tiles.

*_Ku shiga youtube kuyi subscribe na channel ɗinmu KARAMCI TV_*

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now