Page 23

451 58 16
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

*_Assalamu Alaikum, naga comments sosai wanda ni kaina ban san adadinsu ba, masu kuka sai haƙuri, dama haka mutuwa take bata maka sallama sai dai kullum ka zauna da shirinka. Mungode sosai da addu'oinku Allah ya amsa, Amatul'ahad na da masoya muna matuƙar godiya._*

Book2
            '''Page 23'''

Cikin tashin hankali Mommy ta kalli ƙawar ta-ta ta ce "Idan har sai Amatul'ahad bata raye sannan asirin da aka ma mahaifinta zai karye, kina nufin yanzu bata raye?"
      "Gaskiya tunda kika ga haka to yarinyar nan ta mutu, amma ki ƙara bincikawa"
   "Na shiga uku" Mommy ta faɗa cikin tashin hankali.
   "Ke da ya kamata kiyi murna, kuɗinki sun huta zuwa gurin Malam"
   "Ba'a nan gizo ki saƙar ba, ya zanyi da mahaifinta?"
    "Taɓ! Kuma hakane tunda ya dawo hayyacinsa, to amma karki wani damu, kema ki nuna baki san komai ba"
     "Da kamar wuya fa"
"Wallahi ki gwada za ayi nasara"
   "To Allah yasa."

                      ******

"Kayi kyau sosai kamar wani sabon ango" Sumayya ta furta tana murmushi, idanunta akan Fauwaz ɗin.
     "To ai angon ne, kwana nawa ya rage?" Ya bata amsa lokacin yana gyara links ɗin hannunsa.
  Itama murmushi tayi, tana shirin yin wata magana, wayarsa ta fara ringing.
    "Am sorry bari na ɗaga kira"
   "Okay."
Ta furta idanunta a kanshi ko ƙiftawa batayi.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda ya furta tare da sakin wayar tashi ta faɗi ƙasa.
   "Lafiya...?" Sumayya ta furta tana kallonshi, ko motsawa daga gurin ya kasa.

Hannu ta saka ta ɗauki wayar data faɗi, Allah ya sa kan rug ne, dan haka bata fashe ba, a dai-dai lokacin wani kiran ya ƙara shigowa.
     Karɓa yayi sannan ya kara wayar a kunne bayan ya ɗaga.
   "Gani nan zuwa insha Allah" Shine abinda ya faɗa, sannan ya kalli Sumayya.
  "Ina Daddy?"
  "Yana bedroom ɗinsa, amma yanzu yake son tafiya gurin aiki..." Bai ma bari ta ƙarasa ba ya fita da sauri.

Kai tsaye ɗakin Daddy ya nufa, yana ƙoƙarin shiga, Momma na fitowa "Meke faruwa naga ka taho haka rai a ɓace"
   Bai tankata ba, ya kutsa kai ciki, dai-dai lokacin Sumayya ta ƙaraso.
   "Lafiya...?" Momma ta tambaya.
   "Wallahi ban sani ba, naga ya amsa waya sai ya ce ina Daddy"
  
Momma tare da Sumayya suka shige ɗakin Daddy.
   A tsugunne suka tarar da Fauwaz ɗin yana kallon Daddy yaƙi magana, Daddy na ta tambayarsa.

Momma guri ta samu ta zauna, ta kalli Fauwaz ɗin da lokaci ɗaya idanunsa sun rine sunyi jajir sai dai kuma babu ko ƙwalla a cikinsu.
    "Wai mene ke faruwa? ka faɗa mana" Daddy yayi tambayar ranshi ɓace.

"Yanzu aka kirani daga makarantar su Amatul'ahad, wai ta rasu muje mu ɗauketa"
    Sai kuma ya miƙe rai a ɓace, ya lumshe ido sannan ya buɗe ya kalli Daddy ya ce "Zan kashe duk wanda ya ƙara danganta Amatul'ahad da mutuwa" Ya faɗa lokacin jikinsa gaba ɗaya ya fara ɓari.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Daddy ya furta hankali a tashe.
   "Taya za suce ta mutu, meyasa zasu mata sharri"
   "Waye ya kiraka? muga number" Daddy ya furta yana ƙara ruƙo Fauwaz.
   Wayar ya miƙa masa, sai a lokacin ya fashe da kuka a fili, tare da zubewa a gurin ya dafe kai.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" suke ta nanatawa har lokacin da Daddy ya kira number kuma aka tabbatar masa da number Fauwaz ita ce a file ɗin Amatul'ahad shiyasa aka kira.
   "Gamu nan insha Allah, amma daga Kano ne zamu taho, so zamu iya ɗaukar lokaci bamu iso ba"

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now