Shafi na 16

413 45 0
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

*Masoya makaranta wannan littafi ina ta ganin saƙonninku nagode sosai.*

Book1
            '''Shafi na sha-shidda'''

Idanunshi sun kaɗa sun yi jajir, yayinda ita kuma ta kafeshi da ido tana jiran amsa. Ganin bashi da niyyar bata amsa ya saka ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sannan ta kalleshi ta ce "Ashe ni nan ina ta zagin matar Zayyan data cutar dashi, ashe kaine babban macuci, kaine wanda ka ruguza farin cikin ƙanwarka da kuma amininka, Yaya dama kaine kake ɗauke da HIV da...." Kuka ta fashe dashi sannan ta juya da sauri ta bar ɗakin cikin kuka.
     Kallonta kawai yake zuciyarsa na ƙuna, ji yake ina ma ya dawo da baya, domin gyara kuskuren daya tafka.

Ramlat kuwa na shiga parlour da gudu ta ƙarasa jikin Momma ta kwanta ta ƙara fashewa da kuka "Momma...." Shine abinda ta faɗa cikin shashsheƙar kuka.
      "Mene ke faruwa? Ko wani abin ne ya samu Fauwaz ɗin?"
   Girgiza kai kawai tayi, sannan ta tashi tayi ɗakinta da gudu.
   Da mamaki Sumayya ta kalli Momma ta ce "Momma na kasa fahimtar abinda yake faruwa, ko dai na kira Daddy?"
    "A'a Sumayya ki barsu kawai"
   "Momma amma naga daga ɗakin Yaya ta fito tana kuka fa"
     "Ki kwantar da hankalinki kinji ko, komai zai wuce, karki saka damuwa a ranki"
   Kai kawai ta gyaɗa, amma fa hankalinta a tashe yake.

                       ******

A fusace ya shigo parlour. Zaliha dake zaune tayi saurin  miƙewa tsaye saboda tsananin firgici.
    "Ina Amatul-ahad?" Yayi tambayar cikin faɗa.
   "Taaaa...ta...tana ɗaki" Zaliha tayi maganar murya a sarƙe.
  Wucewa yayi kai tsaye ya tura ƙofar bedroom ɗin. Amatul-ahad tana zaune jikin mirrow, fitowarta daga wanka kenan. Ta tsorata ainun yadda ta ganshi a fusace.
  "Baki da gaskiya shiyasa duk sanda na shigo kike tsorata"
    Kallon shi kawai take, ta kasa furta koda kalma ɗaya.
    "Mene tsakaninki da Fauwaz?"
   Ɗan zaro ido tayi, sai da ta haɗiyi yawu saboda tsoro, sannan a hankali ta fara girgiza kai.
    "Za ki ce min baki san shi ba?"
   Girgiza kai ta sake yi sannan ta ce "Ni ban san shi ba"
    "Ƙarya kike" Ya faɗa cikin tsawa yana haki.
   Sai da ta zabura tsabar tsoro, ta runtse ido kuwa saboda tayi famu. Da yatsa ya nunata sannan ya cigaba ta faɗin. "Tun kafin Fauwaz ya ganki ya tsaneki, da shine a situation ɗina ma zai iya illataki fiye da haka, amma kuma abin mamaki yana ganinki sai ya sauko, har yana faɗin in miki sassauci"
   Ajiyar zuciya kawai take saukewa tana kallonshi.
    "Kinyi karatu a New York, shima kuma yayi karatu da aiki a New York. To wallahi muddin na binciko na gano cewa kina da alaƙa dashi" Kaɗa hannu kawai yayi sannan ya fita ya bar ɗakin.
    Kuka ta saki, ta rufe fuska da hannu tana faɗin "Fauwaz ba zan tona maka asiri ba, ni nasan waye Zayyan, na san irin zuciyarsa ta mararsa imani da tausayi, dan haka zan rufe sirrin, zan shafe babin alaƙar da mukayi da kai, ba zan taɓa zama sanadin rugujewar abotarku ba, da izinin Allah, ba zan raba  abotar da ta daɗe da ƙulluwa." Kuka ta cigaba dayi cikin ƙunar zuciya.

*Kuyi haƙuri na zama busy*

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz