Page 19

415 46 2
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

*_Ayi min uzuri kwana biyu banyi posting ba, saboda hutu ya ƙare na koma school, so abubuwan sai a hankali_*
#Banyi Editing ba.

Book2
            '''Page 19'''

"Amma t....!"
Da sauri ta tari numfashinsa ta hanyar faɗin "Kada kayi musu dan Allah"
  "Ba musu zanyi ba, amma fa ni aka zalunta, da yanzu ina da ƴaƴana"
  Ɗan murmushi tayi tare da faɗin "Amnah aka zalunta ba kai ba, kuma Allah ne zai saka mata, Allah zai kaɗai zai kwstar mata haƙƙinta, sai kuma shari'a, amma kai abinda ka aikata to ɗaya ne da abinda ƙawayen Amnah suka aikata, har ma naka zunubin yafi nasu domin kai har da mutanen da basu tsare maka komai ba, dan haka ni zan rakaka gurinsu gaba ɗaya, har su wanda suka zalunci Amnah, ka nemi yafoyarsu, ka fita haƙƙin kowa, su kuma da suka zalunci Amnah akwai sakayya acan, Allah zai saka mata, dan Allah Sultan ka daina wannan halayyar" Ta faɗa tare da haɗe hannayenta biyu alamar roƙo.
     Kallonta yake yana mai jaddada kalamanta a cikin zuciyarsa.
    "Ban taɓa samun soyayya ba, sai a dalilinka, kai ka fara nuna kana sona, kuma ka nuna kulawarka sosai a gareni,  hakan ya sa naji kawai bani son ka zama mai laifi a gurin ubangiji, bana jindaɗin yadda ake maganarka a cikin school ɗin nan, ni dai nafi son inji ana yabonka ba kusheka ba, ina sonka sosai, kuma na shirya zama abokiyar rayuwarka, amma kafin nan nima zan faɗa maka asalina da kuma abinda ya shafi rayuwata, amma sai mun gama zuwa gurin wannan ƴan matan daka ɓata rayuwarsu, zamu fara da wanda suke cikin school ɗin nan"

Shiru ne ya biyo baya na kusa mintuna uku, kafin Sultan ya ce "Gaskiya ban taɓa ganin mace kamarki ba, na godewa Allah daya sa kika shigo cikin rayuwata, mutane da dama suna cewa abinda nakeyi haramun, amma ba wanda ya taɓa zaunawa yayi min nasiha akan hakan. Duk abinda kika faɗa haka ne, amma  kuma idona ya rufe ne kawai ta yadda bana ganin gaskiyar kowa sai abinda nake aikatawa. Amatul'ahad..." Ya ambaci sunan a hankali, ita kuma ta juyo ta kalleshi.
  "Na san mutane da dama ba zasu yafe min ba"
   "Eh hakane, amma na san wasu daga ciki zasu yafe maka, sai dai akwai waɗanda ba zasu iya yafe maka ba kai tsaye. Amma idan muka cigaba da bibiyarsu to zasu yafe."

Motar ya tayar, sannan suka fara tafiya, shiya jagorancesu zuwa gurin ƴammata uku da suke a department ɗaya, sai dai dukkansu babu wacce ma ta tsaya ta sauraresu, sai dai Allsh ya isa da biyu daga cikin ƴammatan suka ja.
  
Bayan sun koma mota kuwa, kasa tayarwa yayi, yayi zaune shiru, ya kasa cewa koma "Kada ka damu da hakan, dama dole ka san hakan sai ta faru, kai dai mu cigaba da nacin zuwa, kada mu karaya, har sai sun haƙura"
   "Akwai waɗanda ko shekara zamuyi muna zuwa ba zasu yafe ba, Amatul'ahad na tafka babban kuskure, sam ban fahimci haka ba sai da kika shigo rayuwata."
      "Kada ka damu, insha Allah za su yafe, ka daina ɗaga hankali"
   Kai ya gyaɗa, sannan ya ja motar.

Department ɗin su Minal suka je, kawai ɓacin rai taji, dan bata son haɗuwa da su, saboda abinda suke mata, amma sai da daure, ta kuma danne zuciyarta.
     
Salma suka fara nema, tana zuwa ta tsaya sororo tana mamaki, ita a tunaninta Amatul'ahad ta kaiwa Sultan ƙararsu shiyasa yazo yaci mutumcinta shiyasa sam  taƙi ƙarasawa.
   "Salma ba wani abu bane, ko zamu ɗan koma gefe muyi magana" Cewar Sultan.
   "Taɓ! Na sani ko wani abu zaku min"
    "Haba Salma, to me kika yi mana, dan Allah kizo, wallahi alkhairi ne ya kawo mu gurinki" Amatul'ahad ta faɗa tana kallon Salma.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now