Page 8

439 48 3
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

*Jama'a ina cigiyar Anty Maijidda Musa, Allah yasa dai ba hijira tayi ta bar Nigeria ba😅*

_*Naga comments akan last page wato page 7, so a gaskiya har ban ma san ta yanda zan amsa wasu ba, a gaskiya labarin Amatul'ahad ni kaina lokacin da aka kawo min shi, sai da naji kamar kada na rubuta, dan tun lokacin ina rubutun littafin Jalila ne, amma bayan Jalila nayi littattafai ku san huɗu ma, sai naga ya kamata na rubuta labarin Amatul'ahad, domin akwai darasi sosai a cikinsa, ina fatan ba iya tausayi kaɗai ba, ku duba darasin cikin labari, kun san cewa tunda har asiri ya ci manzo(SAW) to babu wanda yafi ƙarfin ya ci sa, kunga kenan addu'a tana da babban tasiri sosai musamman a wannan zamani namu da ya lalace, akwai wanda kwantan ɓauna zai maka, ba sai wanda ya fito ƙarara ya nuna maka tsana shine maƙiyinka ba, akwai wanda zai nuna maka so amma kuma babban maƙiyinka ne, Allahu ya datar damu ya kauda mana hassada da fitina da ƙyashi da kuma son zuciya. Ameen*_

Book2
            '''Page 8'''

Zaliha goge hawaye take dan kar Amatul'ahad ta fahimci cewa tana sauraronsu. Yayinda ita kuma Amatul'ahad kanta yana ƙasa sam ta kasa ɗagowa ta kalli Fauwaz, idanunta babu abinda ke fita sai hawaye masu zafi.

Shi kansa Fauwaz yayi mutuwar zaune, ya kasa cewa komai, ya rasa wane irin tunani zai yi.

An ɗauki ku san mintuna goma kafin Fauwaz ɗin ya ɗan motsa kujerar da yake akai.
    A tsorace Amatul'ahad ta ɗago ta kalleshi, idanun nan nata sun kaɗa sunyi jajir, haka fuskarta duk ta canza kala saboda kuka.

Ganin har a lokacin yana zaune kan kujerar ya saka ta mayar da kanta ƙasa tana mai sauke numfashi.

Har a lokacin babu wanda yayi magana.
   "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shine abinda Zaliha ta faɗa a fili tare da haɗe kanta da gwiwa. Sam ta kasa jurewa shiyasa har tayi wannan salatin.

Sai lokacin Fauwaz ya miƙe tsaye ya fita kawai ba tare da ya iya furta komai ba.
   Tare da nurse suka dawo ɗakin.

"Ke kuma kina jinya instead of ki rarrasheta sai ki riƙa kuka, wannan ai sai ki ɗaga mata hankali." Nurse ɗin ta faɗa, tare da ƙarasawa jikin gadon, ta buɗe drawer ta fito da allura.

"Patient tashi ki koma gado za muyi miki allura, mu kuma jona drip, lokaci yayi"
   Bata ma san da ita ake ba, dan ta lula duniyar tunani.

Nurse ta kalli Fauwaz ta ce "Gaskiya sai ta rage wannan tunani, domin zai iya haifar mata babbar matsala"
    "Insha Allah za ta rage" Ya furta a sanyaye.

Nurse ɗin da kanta taje ta dafa Amatul'ahad.
   A tsorace ta ɗago ta kalleta.
  "Ki hau kan gado zamu saka miki drip"

Bata yi magana ba, ta fara ƙoƙarin tashi, nurse ɗin da kuma Zaliha su suka taimaka mata ta koma kan gado ta kwanta.
   Sam taƙi yarda ta haɗa ido da kowa, shi kuwa Fauwaz gaba ɗaya ya mayar da hankalinsa da kuma tunaninsa kacokan  a kanta.

Bayan nurse ɗin ta fita, Zaliha ta zauna gefen Amatul'ahad tare da riƙo hannun da aka saka wa drip ɗin.
   "Ki daina kuka Aunty, ƙaddararki ce ta zo a haka, amma na miki alƙawarin ba zan taɓa gudunki, zan zauna dake koda kowa zai gujeki" Bata ce komai ba, sai hawaye dake ta bin gefen idanunta.
    Zaliha kuwa kuka ta fara, shashsheƙarta na fitowa fili.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now