Shafi na 14

493 46 3
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_👄

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Visit to like our page on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Book1
            '''Shafi na sha-huɗu'''

Hannunshi ta riƙe, dan haka da sauri ya cire hannunshi daga wuyanta.
   Lalube ya fara a motar, ta rasa me yake nema, da bai gani ba kawai ya taka motar ya cigaba da sheƙa gudu.
  Kwanciya tayi kan kujera ta rufe ido tana ta addu'a tare da dana sanin fitowa, har ta bishi.

Take motar yayi ya tsaya, har sai data hantsila, ɗagowa tayi tare da dafe ƙirji. Buɗe ido tayi ta ganta a ƙofar gate ɗin hostel.
     "Sai da safe." Ya furta ba tare daya kalleta ba.
    Za tayi magana kawai ya ɗaga mata hannu, tare da faɗin "Ki fita kawai kiyi addu'a ki kwanta."
   Jikinta a sanyaye ta sauka. Ta fara tafiya har taje ƙofar gate, ta juyo ta kalli motarshi  taga yana nan babu alamar tafiya, security na buɗe mata ƙofa, taji ya tashi motarsa.

Ranar a zaune ta kwana bata runtsa ba, tana ta tunanin mene alaƙarsa da wannan yarinyar da har ya shiga tashin hankali har haka, ita ta san wannan ba sabon abu bane a gurin Hausawa ƴan Nigeria da suke karatu a waje, akwai wanda silar rashin mafaɗi sai su lalace, domin acan babu wanda zai saka musu ido, shiyasa ita sam bata da ƙawa a wannan ƙasa, saboda ita ta san cewa ita take bawa kanta tarbiyya, babu wanda yake zama yayi mata nasiha, sai mahaifinta a faɗin duniyarta, shine kaɗai mai ƙaunarta dan haka ta ɗauki alƙawarin duk runtsi zata kare mutuncinta.

Ranar da wuri ta shirya saboda tana lecture da safe, kafin ta ƙarasa school sai da ta kirashi har sau biyu amma bai ɗaga ba, sai ta haƙura bata sake kira ba, tayi tunanin ko bai tashi daga bacci bane.
   Bayan sun gama lecture ta ɗauko waya taga ko ya kirata amma taga wayam babu missed call ko ɗaya nashi, sai guda biyu na Daddynta.
  Tana shiga ɗaki ta cire ƙaramin mayafin da tayi rolling sannan ta zauna gefen gadonta, room mates ɗinta suna zaune a gado ɗaya suna kallo a system sai sheƙa dariya suke.
    "Hello Daddy, ka kirani lokacin na shiga lecture, so wayan kuma na sakashi a silent."

Daga ɗayan ɓagaren Daddy ya amsa da faɗin "Babu komai Amatul-ahad nima nayi tunanin haka shiyasa ma ban takureki ba, ya karatun?"

Tashi tayi ta bar ɗakin da wayar a kunnenta.
   "Alhamdulillah, komai anayi mana yadda zamu fahimta."

"To masha Allah, muhalli fa, kina jindaɗin zaman wurin?"

"Eh Daddy yayi ba matsala insha Allah, ina zama da wanda ba musulmai ba, so na san duk inda zan koma ma hakane, tunda bana son zama ni ɗaya"

"Ki dai kula sosai, kiyi abinda ya kawoki, karki biyewa zugar kowa, banda fita yawo mara amfani, kiyi karatu dan Allah Amatul-ahad kinji"

"Daddy nayi alƙawarin insha Allahu, ba zan taɓa baka kunya ba"

"Allah yayi miki albarka"

"Amin Daddy, addu'arka a gareni ita take ɗaga darajata, nagode."

                  ******

Suhail dariya kawai yake, shi kuma Fauwaz ya kafeshi da ido rai a ɓace.
    "Ni fa da kaina na faɗa maka na ganta, amma cewa kayi ƙarya ne ita bata zuwa irin wannan guraren, to yanzu gashi ka kamata da gwarto."

Lumshe ido Fauwaz yayi sannan ya buɗe a hankali, yana kallon Suhail da har lokacin dariya yake. "Ya isa haka" Ya faɗa rai a ɓace.
    Kallonshi Suhail yayi sannan ya ce "Kayi haƙuri Fauwaz haka Hausawa suke, musamman wanda suke karatu a ƙasar da ba tasu ba"
     "Kana nufin duk haka suke?"
   "Ƙwarai kuwa"
    "Har ƙanwata?"
  "No ni ban faɗa ba"
"Duk Hausawa kace"
"Eh amma ita wataƙila saboda kai za ta iya ƙin yin wani abu"
   "Zata iya,  ba ƙanwata bace kamar yadda na faɗa maka, a jirgi muka haɗu, naga tana da damuwa shiyasa naso na taimaka mata, amma tunda har Manal za ta iya yin haka, to itama wannan yarinyar zata iya yi, tunda tafi Manal diri da komai. Amma ta ce min shekarunta 15"
    "Taɓ tun anan tayi maka ƙarya, ka kalleta sosai ka gani, ace wai 15 haba dai"
      "Nima sai yanzu na tabbatar da maganarka"
    "Fauwaz shi fa mutum yanzu baya so a shige masa rayuwa, dan haka ka ƙyale kowa yayi yanda yake so kamar yadda ka ƙyaleni."
     "Kaga itama tayi min 2missed calls, Manal kuwa ba adadi"
     "Muga wayar, zanyi maka maganinsu"
   Miƙa masa wayar yayi, number Amatul-ahad ya kalla yayi haddarta da yake yana da saurin ɗaukar abu, sannan ya goge numbers ɗin.

Na goge maka numbers ɗin nasu, in kaga new number kada ka ɗaga "To nagode sosai ka kawo mafita, idan sun gaji kam sai su daina kiran."

*Bayan Kwana Biyu*

A wannan kwanaki biyun kuwa Amatul-ahad ta gaji da kiran Fauwaz dan ta san ba ɗagawa zai yi ba, gashi ita bama zata iya gane estate da yake ba.
      Yau tana zaune a saman gadonta tana chatting kawai kira ya shigo mata. Ganin number da bata sani bane yasa ta ɗaga, tare da karawa a kunne.
    "Hello"
  "Hi! Fatan ina magana da Amatul-ahad"
   "Eh itace"
  "Ya kike?"
  "Lafiya lau, sai dai ban gane mai magana ba"
  "Suhail ne" Jin haka ya saka ta tashi tsaye tare da faɗin "Suhail abokin Fauwaz?"
   "Eh, shine"
  "Lafiya kuwa? Idan na kirashi bana samu Allah yasa yana lafiya"
   "Eh to bashi da lafiya gaskiya"
   "Subhanallah, mene ya sameshi?"
    "To gashi nan dai, damuwa tayi masa yawa, yanzu ma shine ya ce na kiraki dan ya baki haƙuri"
    "Haƙuri kuma, a'a ni bai min laifin komai ba, Allah ya bashi lafiya"
     "Amin, amma ya kamata kizo ki dubashi"
      "Amma....."
  "Babu amma, shi fa ya damu dake sosai, kuma idan kika zo zaiji daɗi"
   "To shikenan, amma yana gida ne?"
  "Eh acan yake jinya"
  "Amma kuma gaskiya ba zan gane gidan ba, ka turo min address"
    "Yanzu kuwa."

                    ******

A dai-dai ƙofar gate ɗin estate ɗin ya ajjeta. Sauka tayi tanawa gurin kallon mamaki, duk da zuwanta ɗaya amma sai taga kamar ba gurin ba.

Kiranshi tayi ta faɗa masa inda take ya ce eh nan ne ta shigo, ya faɗa mata flat ɗin da yake.

A bakin ƙofar ta danna door bell, ta tsaya tana jira, bai ɗau lokaci ba ya buɗe ƙofar. Tana shiga ya rufe yana murmushi.
   Tun a parlour ta gane ba gidan Fauwaz bane.
   Juyowa tayi ta kalli Suhail ta ce "Amma nan ai ba gidan Fauwaz bane"
    "Eh kin ga ai bai kamata ya zauna shi kaɗai ba, wannan dalili ne ya saka na dawo dashi gidana. Ya shiga wanka ki zauna kafin ya fito"
    "Okay" Ta furta sannan ta zauna, shi kuma yayi kitchen.

Yana shiga yayi ɗan tsalle tare da faɗin "Yes, wannan na san zazzafa ce" ya furta sannan ya buɗe fridge ya ɗauko lemon kwali, allura ya tsira a saman kwalin, sannan ya ɗauki cup ya fita.

Tana zaune a inda ya barta duk ta takure guri ɗaya "Sorry, kin san wankan mara lafiya"
   "Ba damuwa zan jira har ya gama"
  Ajje kwalin yayi a gabanta sannan ya tsiyaya a cup ya miƙa mata.
    "Nagode" Ta faɗa lokacin data karɓi cup ɗin.

Fara kurɓa tayi a hankali, shi kuma yana murmushin mugunta, ya zauna kenan yaji an danna door bell.

"Amatul-ahad minti biyu, bara na duba naga waye a ƙofa"
    "Okay ba damuwa"
  Tashi yayi ya nufi ƙofa, ita dai da ido kawai ta bishi.

Yana buɗe ƙofar yaga Fauwaz, gabanshi ba ƙaramin faɗuwa yayi ba.
   "Am..am..amm...Fau...Fauwaz kaine da yamma haka?"
   Kallo ɗaya Fauwaz yayi masa ya gane bashi da gaskiya.
  "Ya ka tokareni, ka bani guri na wuce"
    "A'a ka san wallahi" Ya ɗan fara sosa kai.
   "Wato da alamu ka kawo mace ko, to wallahi ba zan yarda ka cigaba da wannan banzar ɗabi'a ba, dan ita ta rabani da Manal" Ƙoƙarin shiga yake Suhail ya hanashi.
   "Au wai ba zaka barni na shiga ba"
   "Kai dai kawai kaje zamuyi waya"
    "To shikenan, bari na koma" Fauwaz ya faɗa sannan ya juya kamar zai tafi, da sauri ya koma ya ture  Suhail ya shige.

Da sauri Suhail ya biyoshi "Haba Fauwaz"
   Tsayawa Suhail yayi saboda abinda yake ɓoyewa Fauwaz ɗin ya riga ya gani.

Amatul-ahad miƙewa tsaye tayi, ta kalli Fauwaz ta kalli Suhail, abin ya matuƙar bata mamaki.
    "Kace min yana ciki bashi da lafiya ashe dama ƙarya kake min, ka kawoni ne dan ka lalata min rayuwa?"
      "Ƙarya kike, ke kika kawo kanki, ina cewa banayi kina dagewa"
   Juyawa yayi ya kalli Fauwaz "Wallahi haƙuri nake bata ta tafi kar ta ɓata min suna, sai gashi kazo"

Hamma ta fara, tana lumshe ido, a hankali ta buɗe baki za tayi magana taji ya mata nauyi, a kujerar ta zube, lokaci guda bacci mai nauyi ya ɗauketa.
   Kallon Suhail yayi ya ce "Wannan ma duk itace tayi?:
   "Fauw...." Bai ƙarasa ba ya wankeshi da mari tare da cakumoshi.
    "Amanata za kaci? Ka kawota nan ne dan kayi mata fyaɗe?"
    "Fauwaz ka saurareni" Ai bai tsaya jin komai ba ya fara kai masa naushi.

_Kuyi searching *KARAMCI TV* a Youtube channel, ku danna mana *SUBSCRIBE*_
https://youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

Sadeey S Adam✍️

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Où les histoires vivent. Découvrez maintenant