Page 11

418 49 9
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

*_Wannan shafin sadaukarwa ne ga duk wani masoyin littafin ZAFIN HAWAYENA🥰_*

Book1
            '''Page 11'''

*Bayan kwana biyu*

A wannan kwanakin kuwa, Amatul'ahad ta samu ƴanci, domin kuwa Zayyan ya shafa mata lafiya.

Yau tana zaune gaban mirror tana taje gashin kanta. Wayarta da ta fara ringing ta kalla.
  _Brother_ Shine sunan dake yawo kan screen ɗin wayar.

Ɗaukar wayar tayi, tare da karawa a kunne "Hello"
"Ya kike?"
"Lafiya lau"
"To ki fara shirye-shirye komai ya kammala, na gama miki har registration, sai dai sauran abubuwan da ba'ayi ba sai munje school ɗin, domin har accommodation kin samu."

"Alhamdulillah! Naji daɗi sosai, ban ma san da wane kalma zanyi amfani in gode maka, Allah ya biya maka buƙatunka na alkhairi"

"Amin Amatul'ahad, yanzu ke za ki saka ranar tafiya"
   "Ai ni kawai ka saka Fauwaz, ni ko yaushe ma a shirye nake"
  "To ki bari sai next week, ranar monday zan kaiki"
  "To shikenan nagode sosai."

                     ******

Yana zane ita kuma ta ƙura masa ido tana kallonsa.

Hankalin Fauwaz sam ba a kanta yake ba, domin shi gaba ɗaya ya mayar da hankalinsa ga zanen ƙawarta da yake yi.

_Masha Allah, gaskiya gayen nan ya haɗu, yanzu kam na shirya yin soyayya._ Ta faɗa tana ƙara murmusa bakinta.

"Amma gaskiya ka iya zane sosai, amma na san manyan ƴan siyasa, da masu kuɗi basu barinka ka huta."

Sai lokacin ya kalleta yayi murmushi.

   "Nima za a zana ni, amma ni hotona zan bayar a zana"
    "Baki da matsala."

Haka tayi ta janshi da surutu, shi kuma da yake ba mutum bane mai son mu'amula da mata, dan haka baya amsa mata sosai.

Bayan ya gama dasu, ya kalleta ya ce "To idan nayi paint, zuwa jibi sai ki karɓa"

"Wow! Ai wallahi ko a haka aka barshi ma yayi kyau"

Ikram ta juyo ta kalleta ta ce "Kinji ki da wata magana, kinga malama ni dai kiyi min shiru." Ta kalli Fauwaz ta ce "Idan ka gama, sai muyi waya na zo na karɓa"
"To shikenan."
 
Jakarta ta ɗauka tare da faɗin "Ke kuma aku muje ko?"
   "Ke kuma ƙawar aku ba" Ta faɗa tana dariya.

Kallonshi tayi ta ce "Sunana Amatur-rahman"
  Ƙara kallonta yayi da mamaki.

"Ya naga kamar mamaki a fuskarka?"
  Murmushin dole yayi, sannan ya ce "A'a babu komai, kawai da kika faɗi sunan, sai naga kamar na sanki"
   "Maybe zaka iya sani na, ni dai ka burgeni, ba zan ɓoye maka ba, ina so mu zama friends"
   "O...o..okay"
"Ko zan iya samun numberka?"
  "Ki karɓa a wurin Ikram"
"A'a gaskiya, salon tayi min gori, ni kam nafi so ka bani da kanka."
  Karɓar wayarta yayi ya saka mata number, sannan ya miƙa mata.
  "Nagode My Beauty" Ta furta tana murmushi.

Bayan tafiyarsu kuwa zama yayi, yana tunanin anya itace ƴar uwar Amatul'ahad. Ya kasa tabbatarwa duk da cewar yaga kamar tasu ta ɓaci sosai. Ganin tunanin bashi da amfani ya saka ya share maganar kawai.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now