Page 16

396 40 7
                                    


*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

*Jiya bana jindaɗi sosai shiyasa ban ma rubuta note ba, tunda aka fara book2 ban taɓa ganin comments kamar na jiya ba, page 14, wato tun ina reply har na gaji, ansha challenge masha Allah, babu comment ɗin da ban karanta ba, gaskiya Zafin Hawayena Fans page kun sakani a nishaɗi sosai, kuma na fahimci cewa kuna fahimtar labarin, Allah ya bamu ikon yin amfani da darussan cikin labarin, Allah yasa mu faɗakantu dashi. Na sadaukar da wannan shafin gareku.*

Book2
            '''Page 16'''

Sabrina ɓata rai tayi, sannan ta ce "Ni ba za ayi wannan ɗanyen aikin dani ba, haka ka saka naje na tsara Salma, tana ganina da mutunci amma yanzu ko hanya bata so mu haɗa."

"Haba Sabrina, yanzu dan zakiyi mana wannan ɗan ƙaramin aikin shine kike ta fizgewa"
  Kallon Marwan tayi wanda shine yayi maganar. "Yaya Marwan gaskiya ba zan iya ba, ni fa wallahi ban ma so aka san ni ƙanwarku bace, dan wallahi gaba ɗaya kun ja min baƙin jini a school ɗin nan, wasu fa a gaban idona suke zaginku ko su bani saƙon zagi gareku, haba wallahi nayi regretting yin karatu a school ɗin nan"

"Kin ga nifa ba cewa nayi kizo nan ki dameni da surutu mara amfani ba."
   "To shikenan bara na tafi"
Da sauri Sultan ya fuzgo hannunta tare da cewa "Kin san hours ɗin da muka ɗauka muna jiran fitowarki daga lecture kuwa?"
Ƙara haɗe rai tayi tare da juya idanunta gefe.
  "Sabrina ke kaɗai ce ƙanwata da za ki iyayi min wannan taimako"
  "A'a akwai Nadiya, Habiba, Sabir da Khausar duk za su iya"
   "Amma ai kece a school ɗin nan, please Sabrina, baki so na canza halina?"
  "Hakan ce ma ta saka ba zan iya ganganci ba, domin bana son abinda kake yi akan Amnah da ta riga da manta da kai"
     "Amnah bata manta dani ba, kuma na san tana jindaɗin abinda nakeyi, a yanzu ne na shirya samun madadin Amnah, dan Allah ki shige min gaba"
    "Wai dan Allah ga Yaya Marwan shima fa zai iya hakan"
   "Shima yayi abinda yayi, yanzu turn ɗinki ne please My Little Princess"
   Murmushi tayi wanda iyakarshi leɓe, sannan ta ce "Shikenan, amma da sharaɗi"
  "Mene sharaɗin naki?"
"Idan har na gano yaudararta zakayi to wallahi zan zame hannuna, kuma ba zan ƙara kulaka ba har a gida, ka amince?"
   "Na amince, ai wannan Babe ɗin ma ni da gaske nake sonta kuma aurenta zanyi da iznin Allah"
Murmushi tayi tare da miƙa masa wayarta "Saka min numberta"
  Karɓa yayi ya saka tare da cewa "Sunanta Amatul'ahad"
  "Okay, yau zanje in ga surukar Mommy ta gobe"
  Murmushin yaƙe kawai yayi, ita kuma ta juya tana faɗin "Bye-bye mun kusa shiga lecture."

Sai data bar gurin Marwan ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Akwai matsala fa"
    "Tame?"
"Ka san muddin Sabrina ta gane ƙarya kayi mata zata iya tayar da fitina sosai? Kuma gaskiya ni bana son ku samu saɓani da ita, kaga case na Salma sai da ƙyar ta sauka"
   "Wannan ɗin ma zata sauka."
   "Ai gani nayi na Salma ma baka ce aure ba, kawai soyayya kace, amma ta hau sosai"
   "Ka bar ta, ita sakarai ce bata san ta taimaki ɗan uwanta ba, ita burinta kawai shine ta shiga cikin mutane ayi ta hauka, a school ɗin nan kuwa saboda ni gashi ta zama mujiya, kuma ni wallahi nafi son hakan, ina amfanin tara tarkacen ƙawaye tana da ajinta amma ta barshi ya tsinke"
    "Allah yasa muyi nasara kar wannan itama ta kubce mana, kamar yadda Fa'iza ta kubce"
    "Ai idan ka lura ita Fa'iza bayan mun fara soyayya kawai sai aurenta naji, kuma shegiyar taƙi yarda ta dawo school ɗin nan, ai da ta gane shayi ruwa ne"
    "Kuma bata zurfafa a soyayyarka ba, da ba zata taɓa yarda tayi auren ba, dan gani zatayi gaka, kaga sai anyi game over tazo tana dana sani. Allah dai ya kuɓutar da ita daga sharrinka"
    Dariya Sultan yayi tare da faɗin "Shiyasa this time ba zan bari damata ta kubce min ba."

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now