Page 5

460 49 1
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Book2
            '''Page 5'''

Kwanan Amatul'ahad huɗu a asibiti kafin ta samu ta warware sosai.  Tafiya ma a dudduƙe take, amma yanzu kam tana iya miƙewa tsaye, sai dai har yanzu tafiyar ta ta bata dai-daita ba.

Fauwaz na zaune suka fito ita da Zaliha daga toilet, tayi alwallar sallar azahar, lokacin shi kam tuni yayi sallah a masallaci.
    Shi ya shimfiɗa abin sallah, Zaliha ta zura mata hijab.

Tana idar da sallah ta miƙe a hankali daga kan abin sallah, ta koma gefen gadon ta zauna.
    Kallon Fauwaz tayi taga har lokacin ya ƙi ɗauke kansa daga gareta.

"Ki hau kan gadon ki kwanta"
"Na gaji da kwanciya wallahi" Ta furta a hankali.
"Okay, Zaliha saka mata pillow a kan rug ɗin, ta zauna ta miƙe ƙafafunta"

Kallonshi tayi ta cune fuska. Yayi murmushi ya ce "Ai bana son ɗinkin ya samu matsala, am sorry, dole sai kin kula sosai ba ko wane irin zama za kiyi ba"

Zaliha kuwa ta ɗauki pillow da yake yana da laushi ta ajje mata a ƙasa. Ita kuma ta koma ta zauna.

"Aunty bara na ɗan fita"
"Meyasa?"
"Ba komai kawai zan ɗan ga waje"
"Okay to shikenan karki jima fa"
"To."

Shi kuwa Fauwaz daɗin haka yaji, dan haka tana fita ya ce "Meyasa idan kin idar da sallah ba ki yin addu'a?"
"Ina yi mana"
"Ni ban ga alama ba, ko a sujjada ma ya kamata ki faɗawa Allah buƙatunki, sannan idan kin idar da sallah ma ki tsaya kiyi addu'o'i sosai, amma bakya yi, na daɗe da lura da hakan"

Shiru tayi bata ce komai ba.
  "Amatul'ahad idan kina cikin matsala, ba wai kawai kice ‘Allah ka yaye min’ shine addu'a ba. Ki riƙa ma Allah kirari musamman ‘Ya Wadud’ ki yawaita faɗarta. Sannan sunayen Allah guda 99 ki roƙeshi dasu zai amsa miki, musamman addu'a a cikin sujjada ki yawaita yi kinji. Amma muddin ba ki addu'a to ba za ki ga dai-dai ba"

"Insha Allah zan gyara, kenan shiyasa ma abubuwa suka caɓe min saboda bana addu'a?"

"Ta yuwu hakane, domin ita addu'a ita ce maganin komai, kuma ki riƙa sadaka kinji ko?"

"Insha Allahu" Ta faɗa tana wasa da hannayenta.

"Sai kuma abu na biyu" Ya furta gami da tashi ya koma kusa da ita ya zauna.

Da ido kawai ta bishi har sai daya zauna sannan ta ɗauke idanun.
"Ki cire tsoro a duk al'amuranki, muddin da wannan tsoron a ranki, tofa ba zaki taɓa cimma nasara ba. Lokaci yayi da zakiyi yaƙi da abubuwan da suke tunkaroki, kuma wannan ne lokacin da za ki ƙwatowa kanki ƴanci daga gurin Zayyan, domin idan kika bari ya lalata rayuwarki to abinda kike gudu ne zai faru"

Kallonshi tayi a ɗan tsorace.

"Ina nufin daga zarar ya gama lalataki, to zai kaiki gidanku ya watsar dake, kuma sakin da kike gudu shi zai miki, amma a yanzu idan kika ƙwatowa kanki ƴanci, to ko da ya sakeki kina da damar ƙara auren wani, duk da kina da HIV ba zaki rasa wanda zai aureki ba, ko a gurin karɓar magani"

Wasu zafafan hawayene suka zubo daga idanunta, ta kalleshi ta ce "Kai ma ka yarda cewar ina da HIV?"

"Ba wannan maganar nake so muyi ba, dan Allah ki daina kuka, ban son ganin hawayenki, ina so ne mu samu solution na matsalarki"

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now