Page 2

468 39 0
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Book2
            '''Page 2'''

Tafi mintuna biyu a zaune, idanunta a rufe tana mayar da numfashi. A hankali ta buɗe rinannun idanunta  ta sauke a jikin plazman dake manne a bangon ɗakin.

Miƙewa tsaye tayi tana kallon film ɗin da ake haskawa a Zeeworld. _Wasu suna shan soyayya ni kam ina tare da wahala a ko da yaushe, ko ya ya daɗin soyayya yake? Ko ya ya masoya suke ji idan suna tare da juna?_

Gefen gado ta ƙarasa ta zauna tare da saka hannunta a haɓa. 

                 ******

A falo ya tsaya yana gyara links ɗinsa, Momma da ido take binsa, har sai da ya gama sannan ya ƙarasa inda take.

"Momma sannu da hutawa"
"Ya jikin naka? Meya fito da kai? Naga kamar da alamu fita za kayi?"
"Eh Momma ina so na fita saboda bana son na zauna a gida ciwo ya danne ni"
"To da za ka fita yanzu ina zakaje?"
"Zan je gidan friends ɗina ne"
"To ka kula dan Allah"
"Insha Allahu Momma."

A farfajiyar gidan ya ci karo da Ramlat tana ƙoƙarin shigowa.
"Ɗan uwana ya jikin naka?" Ta furta tana ƙare masa kallo.
"Da sauƙi Ramlat"
"Amma ina za kaje?"
"Zan ɗan fita ne saboda bana son na zauna haka"
"To ko dai nazo na rakaka?"
"A'a karki damu zan je ba zan   jima ba"
"To sai ka dawo"

Wuce wa yayi ita kuma ta shiga ciki.

Jikin mota ya ƙarasa ya buɗe ya shiga, ya fi mintuna biyar a cikin mota a zauna kafin ya tayar da ita ya bar gidan.

               ******

Amatur-rahman ta tura ƙofar ɗakin Islaha ta shiga da sallama.
  A ciki Islaha ta amsa mata sannan ta cigaba da kallon da take a cikin system ɗinta.

A hankali Amatur-rahman ta ƙarasa gabanta tare da harɗe hannayenta.
     "Ina miki albishir cewa kwana kaɗan ya rage miki a Nigeria, dan Daddy ya ce zai fara neman miki Visa ya tura ki Umra, kafin ki dawo kuma ya gama nema miki admission da visa zuwa ƙasar Amurka, kin ga burinki na gab da cika saura nawa"

Ɗagowa Islaha tayi tare da taɓe baki "Ke kike murna da hakan, amma ni zuciyata tafasa take da jin wannan labarin, ni a yanzu bani da buri daya wuce in zauna a ƙasar nan inyi karatuna anan"

"Amma ban taɓa sanin ke sauna bace sai yanzu, Islaha ko dai kema ta asirce ki?"

"Wa kenan?" Islaha ta faɗa a kufule tana kallon Amatur-rahman.

"Amatul-ahad mana?" Amatur-rahman ta faɗa tana ƙare harɗe hannuwa a ƙirji.

"Hmmm to ai ni ina gani da Amatul-ahad tana asiri to da tuni ta dawo da farin ciki a cikin rayuwarta, ke ksnki da sai yadda tayi dake"

"God forbid, ai ni kin san asiri ba zai taɓa cina ba, tayi ta gaji, wanda tayi wa Daddy ma karyewa yayi sannan kuma ya koma mata"

"Ke yanzu zaki iya shaida a lahira kan cewa asiri tayiwa Daddy?"

"Ƙwarai kuwa, ga zahiri nan kin gani"
"Kin ga ni bani da lokacin da zamu tsaya tattauna wannan maganar"
"Ai dama ba za ki samu lokacin ba"
Tsaki tayi sannan ta juya ta bar ɗakin.
  Da harara Islaha ta bi ƙofar tana mai jin haushin Amatur-rahman.

*Mid-night*

Kamar a mafarki taji an buɗe ƙofa. A hankali ta ɗan ja blanket da ta rufe jikinta dashi, sannan ta buɗe ido a dai-dai lokacin daya kunna light ɗin ɗakin.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now