Shafi na 10

478 37 2
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Written by SaNaz deeyah_👄

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

_Ina ganin Comments ɗinku gaskiya ina jindaɗi kuna farantamin nagode sosai._

Book1
            '''Shafi na Goma'''

Da sauri Fauwaz ya sunkuya ya ɗauki wayarsa, gaba ɗaya screen ɗin ya fashe, amma bai damu ba saboda yadda yake cikin tashin hankali. A lokacin kuma Zayyan ya ƙaraso gurin.

"Ya na ganka a tsaye, ka zauna please" Sai kuma ya kalli Amatul-ahad da Zaliha da suke tsaye.
     Fauwaz kuwa zama yayi domin dama ji yayi ƙafafunsa suna neman gagarar ɗaukarsa.
   "Fauwaz ka ganta ko, sai fuskar salihai amma munafuka ce, wannan da kake gani ita ta ruguza duk farin cikina"
   Amatul-ahad kallon ƙasa tayi, tana jujjuya idanunta kafin ta sake ɗagosu ta kalli Zayyan lokacin da yake faɗin "Mazinaciya ce, amma ance mahaifiyarta ma haka tayi, kaga kuma ita jijiya naso take"
     "Karka sake aibata mahaifiyata, domin ba ita tayi maka laifi ba."  Hannu ta saka ta rufe fuska tare da fashewa da kuka. Zaliha kuwa ƙara riƙeta tayi tana mai jin haushin furucin Zayyan.

"Zayyan bai kamata ka haɗa da mahaifiyarta ba, komai za kayi a rayuwa na cin fuska karka haɗa da uwa"
     "Fauwaz na tsaneta, duk wani furucina da zai fito a kanta gaskiya ne, yarinyar nan har kuɗi na bata nace ta gudu amma sam taƙi, muguwa ce, wallahi ba zan taɓa raga mata"
    "Ka ga ni in har maganar nan ba za ta wuce ba zan tafi kawai in barka"
   "Ina zuwa" Zayyan ya furta tare da komawa side ɗinsa.

"Bata da lafiya ne?" Fauwaz ya faɗa lokacin da Zayyan ya bar gurin.
    "Eh" Shine abinda Zaliha ta furta, ita kuma Amatul-ahad ɗagowa tayi ta kalleshi, tana son magana amma ta kasa kama kalma ɗaya da zata faɗa masa.
     Juyawa kawai tayi tana tafiya da ƙyar za su koma upstairs.
   "Kiyi haƙuri Amatul-ahad" Juyowa tayi ta kalleshi, a wannan karon kallon banza ta wurga masa sannan ta juya.

Key ɗin mota Fauwaz ya ɗauka, da sauri ya fita ya nufi inda motarshi take.
   Yana buɗewa ya saka ƙafa ɗaya kenan, ya jiyo ihu daga cikin gidan.
  Da sauri ya rufe ƙofa ya koma ciki.

Sani dake tsaye ya kalli Yaquba "Yau fa babu lafiya a cikin gidan nan"
    "Nima gaskiya nayi tunanin haka dan da alama kam."
   "Ni ban taɓa ganin azzalumin mutum kamar maigidan nan ba" Yaquba juyawa yayi ya kalli ko ina sannan ya ce "Kada ka ƙara wannan furuci, domin zaka iya jawa kanka kora."
   Tsaki kawai Sani yayi.

Fauwaz na shiga ya tarar da Zayyan ɗin yana zabga mata belt. Da gudu ya ƙarasa ga Zayyan ya riƙe.
   "Haba Zayyan dukan mace ba naka bane, babu wani amfani"
     "Fauwaz ganin idonka ne ya saka ta samu damar faɗa min magana, ita ta isa, bata san dama a wuyana take ba"
     "Gaskiya bai kamata ba, kuma abin naka is getting much, haba"

Zaliha da sauri ta ƙarasa gaban Amatul-ahad ta ɗagota daga kwance.
    Fauwaz kallonta yayi yaji zuciyarsa tamkar zata fito daga ƙirjinsa. Huci kawai yake mai zafi.

_Idan ban janye shi ba, zai iya illatata._
   Jan shi yayi suka fita sai banbami yake. Shi dai bai ce komai ba, ya buɗe masa mota ya shiga sannan shima ya zagaya ya shiga ya jata.
     "Ikon Allah" Sani ya furta, Yaquba kuwa da sauri yaje ya buɗe gate.

Zaliha ƙoƙarin ɗaga Amatul-ahad take, amma taƙi tashi.
   "Aunty ki tashi na kaiki ɗaki"
   "A'a ki barni anan mutuwa zanyi" ta faɗa lokacin wasu sabbin hawayen sun fito daga cikin idanunta.
   "Aunty ki sani ita wuya bata kisa, ni kaina na taso cikin maraici da kuma tsangwama gurin matan uba, amma dai dana ga rayuwarki, da irin wuyar da kike sha sai naga wuyar dana sha ba komai bace, ki sani ba zaki taɓa mutuwa ba sai lokacinki yayi, kuma nayi imani da Allah a gaba komai zai dai-daita, kuma komai zai zama tarihi, duk tsanani maganinsa Allah, na san kina addu'a kuma Allah bai manta dake ba, na san zai duba lamuranki kiyi haƙuri."
      Hannu ta saka ta goge hawaye tare da cire hijabin jikinta.
     "Zaliha jini bina yake, ina tabbatar da cewa ɗinki da aka yi min ya katse, ban san ya zanyi ba?"
   "Ya kamata mu koma asibiti Aunty"
   "Kai a'a gaskiya ina tsoro, wannan karon za su iya wulaƙantani"
    "Larura tana kan kowa fa, kuma wane wulaƙanci bayan haƙƙinsu ne kula da mara lafiya"
     "A'a Zaliha, ki bari kawai zuwa jibi sai muje dama ranar zan koma, ki kamani na koma ɗaki"
  Hannu Zaliha ta saka ta goge ƙwalla sannan ta kama Amatul-ahad a hankali.

                   ******

Driving yake zuciyarshi a cunkushe, Zayyan dake gefe kuma sai jan tsaki yake.
    "Haba Zayyan wai mene hakan?"
    "Kana gani fa yarinyar nan dan taga a gaban idonka ne ya saka ta faɗa min magana"
     "Zayyan ban san abin har ya kai haka ba, kuma matarka tana da ƙuruciya dan Allah ka sassauta mata"
   "Sassauci, haba Fauwaz ni banyi tunanin zaka faɗi haka ba, bai kamata ta fara baka tausayi ba"
   "Kaga idan wannan maganar zaka min dan Allah ka barta bana so"
   "Ni ba zan daina maka magana akan haka ba, yanzu dai ina mukayi?"
     "A'ah za muje gidan girlfriend ɗinka mana"
    "No ai zuwa gidan ya fasu"
   "Meyasa?"
  "Na kira ashe sunyi tafiya"
  "Meyasa tuntuni bata faɗa maka ba"
   "Sai yanzu ina gidanka ta kirani, amma kuma ta ce ba daɗewa za tayi ba, so idan ta dawo sai muje ko?"
    "To yanzu dai kawai ka saukeni a gidan Mameey dan ba zan koma gida ba"
     "Okay to shikenan."

*Kuyi manage please*

Wattpad @SaNaz_deeyah

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now