Page 17

395 44 2
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story''' _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

Book2
            '''Page 17'''

Da kanshi ya ɗauki lemo ya zuba a glass cup, sannan ya miƙa mata. Karɓa tayi babu musu, har a lokacin bata ɗauke idanunta daga kallonshi ba.
   Kallonta yayi, ya ɗanyi murmushi tare da cewa "Bari naje gurin Mom na dawo, ki saki jikinki fa"
  Kai kawai ta gyaɗa, sannan ya tashi ya bar gurin.

A parlour'nta ya sameta ita da Nadiya suna kallo. Zama yayi kan ɗaya daga cikin kujerun parlour'n kafin ya ce "Mommy ina fatan tayi miki?" Ya furta idanunsa a kanta.

Mayar da kallonta tayi gareshi sannan ta ce "Da dukkan alamu yarinyar bata da matsala, sai dai na fahimci kamar akwai damuwa a tare da ita"
   "A'a Mom bata da wata damuwa, kawai dai kunya ce"
  "Okay tunda haka kace, na yarda."
   "Zanje na mayar da ita school, bara muje"
   "Ai na ɗauka ka kawota nan tayi mana kwana biyu"
  "Mom ai ba zata iya kwana gidan nan ba, tana da kunya ne sosai
   "To ka kawota nan muyi sallama ko, Nadiya tashi ki ɗebo min turaruka da mayuka"
   "Ai kuwa ba lallai ta karɓa ba"
  "Meyasa?"
"Ɗabi'arta ce a hakan"
   "Ni dai kyautata kam dole ta karɓa"
  "Bara na kirata"

Yana shiga parlour'n ta ɗaga kai ta kalleshi. Har gabanta ya ƙaraso tare da cewa "Tashi muje gurin Mommy" Kai ta gyaɗa sannan ta ce "Naga yamma tana ƙara yi, gara na tafi school"
  "Za kuyi sallama ne, sai na mayar dake hostel"
  "Okay." Ta faɗa sannan ta miƙe a ɗarare tabi bayanshi.

Suna zaune a parlour'n Mom, Nadiya ta fito hannunta riƙe da leda.
   "Miƙawa ɗiyata" Mom ta faɗa tare da sake cewa "Ɗiyata ga wannan, nagode da ziyara" Karɓa tayi sannan tayi godiya, har a lokacin kanta yana ƙasa.

Sultan miƙewa yayi tare da faɗin "Muje ko?"
  Tashi tayi, ta ɗan ƙara russinawa tayiwa Mommy godiya.
   "Ba komai ƴata, next time ki taho da kayanki ki kwanar mana ko biyu ne kinji"
   Murmushi kawai tayi.

A kusa da gate ɗin hostel ɗin yayi parking, sannan ya kalleta ya ce "Ƴam matana mun ƙaraso"
  Kallonshi tayi, bata da alamar fita ma. "Wacece Amnah?"
  Dafe hannayenshi yayi a jikin sitiyari, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.
  "Ka faɗa min please"
"Amatul'ahad ita Amnah budurwata ce, kuma cousin sister ɗina, munyi soyayya da ita kuma har an saka mana rana, ana saura sati biyu bikinmu ta rasu"
  "Allah yajiƙanta da rahama"
  "Amin." Ya faɗa a raunane.
   "Meyasa kake son lalata rayuwarka da ta wasu akanta? Mene mata sukayi mata?"
    "Yanzu lokacin sallah yayi, ya kamata muyi sallah ko?"
  Kallonshi kawai take, bata sake magana ba.
  "Muje muyi sallah, sai na baki labarin Amnah"
  Murmushi kawai tayi, dan jikinta ya bata ba zai dawo ba.

Sallama sukayi, ya kuma tabbatar mata a cikin school zai yi sallah kuma yana idarwa zai dawo, idan ya dawo zai kirata a waya.

Tana saka ƙafarta a ɗakinsu Azizat taja tsaki.
  Kallonta tayi, sannan ta ƙarasa gabanta "Ni na rasa gane kanki, ita Minal da suka taɓa soyayya ma bata ɗaga hankali kamarki ba"
   "Wai ke kin waye kinyi baki ko? To wallahi a juri zuwa rafi..."
  Kallon Minal tayi da take zaune a gaban gas tana girki.
    "Aikin banza, kun saka min ido, a cikinku babu uwata, ba ubana, babu wadda nake da dangantaka da ita, soyayya da Sultan kuma yanzu na fara, dan haka babu wanda ya isa ya rabamu, ku daina shiga harkata kuyi rayuwarku inyi tawa, in ba haka ba zan kaiku student affairs a shiga tsakaninmu" Ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsaki.
   Dukkansu ba wanda ya ƙara cewa komai.
 
Amatul'ahad kuwa tayi ta jiran Sultan amma shiru, da ta ga goma har ta wuce, kawai ta zura kayan bacci ta kwanta.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now