Shafi na 6-7

585 37 0
                                    

[9/6, 9:37 PM] Didi~👸🏻: *ZAFIN HAWAYENA*
     '''A True Life Story'''
    _Written by SaNaz deeyah_👄

*K.W.A📚*

            '''Shafi na Shidda'''

"Wace irin magana ce kake faɗa haka ba daɗin ji Zayyan.?"

Lumshe ido Zayyan yayi, zuciyarshi na raɗaɗi da ƙuna, tsawon mintuna biyu ya ɗauka idanun a rufe, kafin ya buɗesu ya kai kallonsa ga Fauwaz
     "Fauwaz auren dole Daddy yayi min, kuma ya san yarinyar tana ɗauke da wannan ciwon, amma ya aura min ita a haka, da ya san cewa bana son aurenta, sai ya ce min idan har ban bata haƙƙin aure ba bai yafe min ba, kaga ya ɗaureni da jijiyoyin jikina."
    "Gaskiya da mamaki, taya ya san tana da wannan cutar kuma zai ce ka aureta, kaine ɗa ɗaya tilo a gurinsa, taya ya zai maka wannan abin?"
    "Saboda yanzu ya daina sona, kuma baya son ɗorewar farin cikina"
    "Wallahi gaba ɗaya ɗaya ka sakani a duhu, ka fitar dani mana."

Zayyan ya miƙe tsaye, sannan ya ɗan jingina jikinshi da table ɗin dake girke a office ɗin, kallon Fauwaz yayi ya ce "Mahaifinta da nawa aminai ne tun suna yara, har girmansu, sai dai mu ƴaƴa bamuyi wannan zumuncin ba, kaga ni kaɗaine ɗa a gurin mahaifana, ita kuma a nata ɓangaren su huɗu ne, uku mata ɗaya namiji, to yarinyar irin an nuna mata so, an sangartata, sai ta lalace, zuwa club, kwana ɗakin saurayi da sauransu, ƙarshe dai ta kwaso cutar ƙanjamau(HIV) so a wannan lokacin mahaifinta ya fusata, ya koreta daga gidanshi, sai tazo gidanmu tana kuka ta sanarwa da mahaifina, shi kuma buɗar bakinsa sai ya ce zai share mata hawaye, zai kuma kaita inda za taji daɗi, anan gidanmu ta zauna tsawon sati ɗaya, wallahi
ban taɓa tunanin abinda Daddy zai yi ba kenan, amma kawai sai kirana yayi ya ce min in shirya, ya saka bikina da ita wata ɗaya kacal."
    "Tirƙashi!" Fauwaz ya furta yana mai jinjina labarin da Zayyan ya bashi.
    "To amma kuma are you sure Daddy ya san yarinyar tana da HIV?"
    "Wallahi tun kafin ta samu HIV ya san tana da yawan banza, domin ni dashi mun sha yi mata faɗa, ashe ni za ta kwasowa bala'i."
    "Mameey fa? Ba tayi yunƙurin hanawa ba?"
   "Fauwaz kenan, abin fa ba ƙarami bane, duk wanda ka san ya isa da Daddy yayi masa magana amma ya toshe kunne, kai hatta mahaifin ita yarinyar. Shiyasa kaf dangi kowa ya tsaneta babu mai zuwa gidana, haka itama bata isa taje wajensu ba."
     Fauwaz zai ɗan dafe kai, sannan ya ƙara da faɗin "Ni fa nafi ganin laifinka Zayyan, taya za ai na san yarinya na da cutar ƙanjamau in yi kwanciyar aure da ita, beside bai ma kamata ka aureta ba, da mutumcinka da kimarka, baka taɓa neman mata ba, baka shaye-shaye, taya wannan abu zai faru da kai"
      "Ƙaddarata ce, Fauwaz wallahi duk yadda zan faɗa maka ba zaka fahimta ba, ina son Daddy kuma ka san yana da hawan jini, so ba zan iya masa musu ba, dan naso yin haka naga ciwon shi na neman tashi wai shi tausayi"
      "Yana tausayinta amma kai meyasa ba zai tausaya maka ba, kuma meyasa bai nemo mata mai cuta irin tata ta aura ba, ai suna auren masu ciwo irin nasu"
    "Hmmm to Daddy duk wanda yazo yi masa faɗa ko nasiha, wallahi cewa yake idan tana da cutar nima in ɗauka, kuma ka san ma babban takaicin?"
  Fauwaz ya girgiza kai alamar a'a.
   "Shine yayi mata komai da ya kamata iyayenta suyi mata, a gidanmu ya saka ayi mata hidimar biki, gaba ɗaya shine ya zama waliyin amarya da ango, saboda mahaifinta ya ce babu shi babu ita. Kuma ranar da zan ɗauketa mu tare ya ce idan ban bata haƙƙin aure ba bai yafe min ba, kuma idan tana da cutar nima in ɗauka. Kaga hakan na nufin kar na ƙara wani auren, waye zai aureni da cutar nan? Babu, wallahi gani nake kamar asiri aka yi wa Daddy"
    "Ka da ka kawo wannan, amma kai kana da tabbacin tana da cutar?"
    "Wallahi tana da ita, saboda Family doctor ɗinsu ne ya gwadata ya tabbatar da hakan, kuma da mahaifinta bai yarda ba, sai suka ƙara zuwa wani asibitin, still da akayi gwaji positive ya nuna"
    "Taɓ! Gaskiya na tayaka takaici, wasu ƙattin banza su lalata mace, sannan basu aureta ba azo a liƙa maka ita"
   "Wallahi kuwa, wannan dalilin ne ya saka na kasa zuwa gidanku, Fauwaz wallahi har yanzu ina son Ramlat amma na san na rasata har abada, kuma ko da naje na sanar dasu abinda ke faruwa, Ramlat za tace na faɗa ne saboda bana son aurenta. Dan Allah ina so ka bawa Daddy da Momma haƙuri da ita kanta Ramlat, wadda har yanzu na kasa mantawa da ita a rayuwa."
    Fauwaz buɗe wayarshi yayi kamar yana duba wani abin. Saving na recording ɗin yayi, sannan ya ajje wayar a gefe yana kallon Zayyan da idanunsa, wanda tuni sun fara canza launi saboda damuwa.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now