Page 29

404 56 11
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like our page on facebook👉🏻 https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow my group on facebook👇🏻 https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Please SUBSCRIBE our youtube channel 👉🏻https://youtube.com/c/KARAMCITV
Book2
            '''Page 29'''

*_Washe Gari_*

Tun da wuri suka shirya, wajen ƙarfe sha ɗaya na safe suka fito zuwa ɗakin Umma.
  Da sallama suka shiga bedroom ɗin Umma, Minal har ƙasa ta durƙusa ta gaidata.
Cikin girmamawa ta ce "Aminatu ya kika tashi?"
"Lafiya lau Umma"
Kallon Azizat tayi ta ce "Kun karya dai ko?"
"Eh mun karya. Umma dama akwai wata ƙawarmu, yanzu gidansu zamuje zan raka Minal"
"Okay to kar dai ku daɗe"
"Insha Allah ba zamu daɗe ba."

Suna fita ƙofar gida ta kalleta ta ce "Amma Azizat meyasa baki faɗa mata gaskiyar inda zamuje ba?"
Murmushi tayi sannan ta ce "Ai idan na faɗa mata gaskiya wallahi ba zata barmu ba, ita da tayi ta tsinewa mahaifin Amatul'ahad, ki duba duk wahalar registration fee, amma haka aka daure aka riƙa biya min, haka nake fama da daɗi babu daɗi na tafi makaranta, na hana idona nayi karatu amma rana ɗaya kwatsam saura shekara da bata kai biyu ba in gama aka koreni, ya iyayena ba za su ji haushi ba"
  Ajiyar zuciya Minal tayi sannan ta ce "Wallahi ni kuma laifina suka gani, kuma nima ina ganin laifin namu, sai dai mu ba a tsaurara mana kamar Salma ba, kin san babansu yana da zafi sosai, shi da kansa ya ce ta gama karatu, kuma aure zai mata, sannan kuma yanzu ko nan da can bata zuwa wallahi, da kanshi fa ya ce ta gama karatun boko kuma ko mijin da za ta aura idan ya ce yana son tayi karatu zai hana"
  "Taɓ, dama fa shi babanta yana da zafi wallahi, amma hukuncin yayi tsauri da yawa"
  "Ni ɗinma ba wani fita ake barina ba, ba dan bikinki bane, wallahi ba'a barina nazo."

Suna ta hira dai har suka tari mai napep suka shiga.
Kai tsaye suka wuce Nassarawa GRA. Har ƙofar gidan su Amatul'ahad.

                           ******

Napep na tsayawa ƙofar gidan ta sauka, tare da janyo trolley'n da Amatul'ahad ta saya mata. Kai tsaye gaban gate ɗin ta dosa, tare da yin knocking.

Yaquba ne ya buɗe ƙaramar ƙofar ya leƙo "Ikon Allah, yau a gari, inji maƙi baƙo"
Murmushi tayi sannan taja trolley ɗin ya matsa ta shiga.

Sani dake zaune, ya yi saurin tasowa, jikinsa a sanyaye ya ce "Zaliha, yau a gari? Ina ta neman numberki bata shiga"
"Wallahi kuwa, wayata ai matsala ta samu shiyasa"
"Saukar yaushe?" Yaquba ya faɗa yana ƙarasowa.
"Yanzun nan. Allah yasa Aunty ta dawo, dan naji shirun ya yi yawa shiyasa na dawo, ko ita ƙila ta kira wayata a kashe"

Yaquba ya kalli Sani sannan ya yi gyaran murya tare da cewa "Na bar radio a kunne a ɗaki, bari naje na kashe ko?" Bai ma jira abinda Sani zai ce, ya yi saurin wucewa.

"Ko Auntyn bata dawo bane?" Zaliha ta tambaya tana kallon Sani.
  "Wato abinda ke faruwa shine..." Sai kuma ya yi shiru.
"Ya kayi shiru kuma?"
"Am... Dam..dama..." Shiru ya sakeyi bai ce komai ba.
"Dan Allah ka faɗa min abinda ke faruwa mana"
Sai daya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce "Allah ya yiwa Hajiya rasu kusan wata biyu kenan..."
Tun kafin ya ƙarasa maganar Zaliha ta zube ƙasa tare da kurma salati.

Idanunta tuni sun fara zubda hawaye, ta kalleshi ta ce "Idan wasa kake min ka bari bana so dan Allah"
"Zaliha sai haƙuri, ba zan taɓa miki ƙarya da mutuwa ba, tun da akayi rasuwar nake kiranki bata shiga."

"Aunty....." Sai kuma ta rushe da kuka ta cigaba da faɗin "Aunty dama wannan ita ce haɗuwarmu ta ƙarshe, Aunty shikenan ba zan sake ganinki ba... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Hannu ta ɗora aka tana ta kuka kamar ƙaramar yarinya. A haka Zayyan ya fito daga cikin gidan.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now