Page 18

465 50 8
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

Book2
            '''Page 18'''

Suna zaune a cikin motarsa, bayan fitowarta daga lecture, dan kiran da tayi masa ne ya saka shi zuwa, amma sam baya da lectures a ranar.
    
Tayi shiru tsawon mintuna, kafin ta ɗago, bata kalleshi ba ta ce "Ina son sanin wacece Amnah, sannan meyasa kake waɗannan abubuwan a dalilinta, tun waccan ranar nake son ka faɗa min, amma sai naga ka watsar da maganar.

Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya jingina bayanshi da jikin kujerar "Amnah...!" Ya furta tare da lumshe idanunsa.
      Ɗan kallonsa tayi sannan ta ɗauke kai ta mayar da kanta ƙasa.
    "Amatul'ahad kenan, duk ƴam matan da nayi babu wacce ta taɓa tambayata wacece Amnah, mene alaƙata da ita, amma ke kin tambayeni, sauran ma a bakina suke jin sunan, amma ke ba a bakina kika fara ji ba, na san a bakin Sabrina ne."
  
Shiru ne ya biyo baya, kafin ya cigaba da cewa "Hakan ce ta saka na gane lallai na samu wadda za ta maye min gurbin Amnah, wallahi har cikin raina nake jin sonki, kuma inaji a raina mutuwa ce kaɗai zata iya rabamu duk runtsi."
    Wasu zafafan hawayene suka samu damar fitowa daga idanunta. Tana murmushi ta saka hannu tana gogewa. _Ashe dama wannan ranar za ta zo a cikin rayuwata, na samu masoyi na haƙiƙa, Allah na gode maka._ Ta furta a ranta sannan ta kalleshi. Har a lokacin idanuwanshi a lumshe suke.

"Amnah a cikin school ɗin nan tayi karatu, ina 200level ita kuma ta samu gurbin karatu, kuma a dalilina ne ta zaɓi wannan makarantar, sai dai ita a ɓangaren Mass Comm take. Amnah kyakykyawar gaske ce, hakan ne ya saka tana zuwa maza suka fara rububinta kowa na sonta, a lokacin ban zama fitinanne kamar haka ba, domin ni ɗin ma ban tsira daga mata ba, mata suna zuwa har gurina suce suna sona, wasu har cewa suke dan Allah inyi soyayya dasu ko ba ta aure ba, amma bana yarda saboda Amnah taƙi kula kowa nima sai naƙi yarda da kowa.
     Nine saurayinta kuma abokinta, komai tare muke kuma ko ina tare muke zuwa, sannan tare muke barin school duk tsawon lecture da za a ɗauka, kuma ko bani da lectures zan shigo school tare da ita in shiga department ɗinsu in ɗau lecture, haka itama.
      Cousin sister ɗina ce, Mamana da Babanta gidansu ɗaya, kuma same parent. Ku san zan iya ce miki rabin rayuwar Amnah tana gudanar da itane a gidanmu kasancewar ita kaɗai iyayenta suka haifa, bata da abokin hira shiyasa rabin rayuwarta ya dawo gidanmu tun kafin ma mu fara soyayya, da iyayenta suka rasu kuma sai gaba ɗaya rayuwarta ta dawo gidanmu.
    Na fara sonta ne tun tana SS1.

Bayan mun gama first semester mun shiga second semester sai tayi wasu abokai, ƴam mata su uku. Da farko naso hanata kulasu dan naga kamar suna da rawar kai, amma daga baya kawai sai na ƙyaleta dan bana so na hanata gudanar da rayuwarta ta hanyar takura, a lokacin an saka ranar bikinmu, muna gama second semester a wannan hutun session ɗin a wannan lokacin za ayi bikin mu.

Amatul'ahad! Wannan ƙawayen sune suka ruguza rayuwarta, sun fara shiga jikinta ne ta yadda ba zata iya ciresu ba. Har ta kai ta kawo za su zo gida su ɗauketa su fita unguwa, duk da haka bata zuwa koma ina ne sai da iznina, ni kuma ina danne zuciyata ne kawai ba dan ina so ba.
    Tana yawan faɗa min cewa sun ce mata tana da kyau amma ta zauna da saurayi ɗaya, kamata yayi tayi amfani da kyaunta ta gwara kan maza. Amma sai taƙi amincewa, iyayenmu suna da kuɗi daga nata har nawa, basu ragemu da komai ba, sannan nima ban rageta da komai ba, to dan me zata kula wasu.
    Sai suke tsiro da faɗa mata ai wallahi ina soyayya a ɓoye ta bincika, amma kai tsaye ta faɗa min. A wannan lokacin nace mata “Amnah ki rabu da wannan ƙawayen naki, ba ƙawayen arziƙi bane” Ta ce min za ta yakice su amma dai idan ta rabu dasu kai tsaye to lallai zasu zargi wani abin, ita kuma bata son tayi gaba ko faɗa da kowa.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now