Page 28

425 51 3
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like our page on facebook👉🏻 https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow my group on facebook👇🏻 https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Please SUBSCRIBE our youtube channel 👉🏻https://youtube.com/c/KARAMCITV
Book2
            '''Page 28'''

A firgice ya tashi, gami da doka uban salati.
Zufar goshinsa ya saka hannu ya ɗan taɓa.
   Kallon ɗakin ya yi, tare da kai dubansa ga AC da take a kunne, kuma ta karaɗe ɗakin da sanyi.

Ƙafafuwansa ya sauke a ƙasa, kai tsaye toilet ya nufa yayi alwallah, sannan ya fito ya shinfiɗa abin sallah gami da tayarwa.

Sai da yayi nafiloli sannan ya ɗaga hannu sama ya fara addu'o'i.
  "Ya rabbi, na san na zalunci Amatul'ahad, kuma ta rasu ba tare dana samu tabbacin ta yafe min abinda nayi mata. Tabbas nayi aiki da rashin tunani, shiyasa tun bayan rasuwarta na kasa samun sukuni. Ya ubangiji ka yafe min, ita kuma ka jiƙanta da rahama ya rabbi ka sa ƙarshen wahalarta kenan" Hannu ya saka ya shafa sannan ya sauke kanshi ƙasa.
_Rayuwata sai ta fi maka mutuwata daɗi._ Ya ƙara tuno furucin Amatul'ahad na ƙarshe da sukayi.

Lumshe idonsa yayi lokaci guda yaji kansa na sara masa. Yafi mintuna biyar a haka, kafin ya buɗe idanunsa. Gani yayi komai ya fara juya masa.

Wayarsa da ta fara ringing yayi saurin janyowa ya kalla. Bibbiyu yake gani shiyasa ma ya kasa tantance mai kiran.

Yana ɗagawa ya ji muryar Daddynsa.
  Bai ma tsaya yaji abinda zai faɗa ba, kawai ya ce "Daddy mutuwa zanyi." Shine abinda ya iya faɗa, lokaci guda ya faɗi anan ƙasa.

Daddyn Zayyan kuwa, ganin yana ta magana yaji shiru, ya saka hankalinsa ya tashi.

                      ******

Tana buɗe ido ta miƙe zaune. Ƙanwar Mahaifinta ta gani zaune gefen gadon ta riƙe hannunta.

"Aunty Bilki ina Mommy take? Me idona ya gane min, dan Allah karku ce Mommy ta mutu please Aunty"
   "Kiyi haƙuri Amatu ki kwantar da hankalinki"
  "Aunty ni dai ki faɗa min gaskiya?" Ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka.
   "Ki bar kuka, Mamanki na raye, tana asibiti tare da Babanku, amma yanzu ma zasu dawo"
Cikin kuka Amatur-rahman ta ce "Wane asibiti ne?"
  "Kada ki damu, suma fa suna hanya kinji ko"
Ɗora kanta tayi a kafaɗar  Aunty Bilki ta cigaba da shashsheƙar kuka.

                       ******

Shiru kawai Daddy ya yi, ya kasa cewa komai, Alhaji Murtala wanda ya kasance maƙocinsu ne ya ce "Yanzu Likita za'a bamu gawar mu tafi da ita mu suturta?"
   "Eh amma sai mun samu saka hannun jami'an tsaro, saboda case ne na kisa"
  "Ai already muna tare dasu, suna ma waje."
  "Okay to bismillah muje ko?"

Daddy dai bai ce komai ba, bi kawai yake, har aka saka hannu aka basu damar tafiya da gawar, sannan Daddy ya furta salati.

Alhaji Murtala ya kalleshi ya ce "Alhaji sai haƙuri, Allah yayi mata rahma"
  "Amin." Abinda ya iya faɗa kawai.

*Bayan wasu awanni*

"Bana son kowa ya zauna min zaman makoki, ko mace ko namiji, dan Allah ka sallami kowa, mungode" Daddy ya furta sannan ya juya ya shige cikin gida.

Tun daga parlour yake jiyo kukan Amatur-rahman. Kallon ƙannenshi yayi guda biyu da suke zaune a wajen, sai wasu daga cikin dangin Mommy.
  "Ina so a faɗawa kowa ya tafi mun gode sosai, na saka maigadi ya sanar cewa babu zaman makoki, duk wanda yazo zai iya yin gaisuwa ya tafi."
   Hajiya Karima ɗaya daga cikin ƙannensa ta ce "To Yaya amma..."
"Dan Allah Karime ina buƙatar kaɗaici" Yana gama maganar ya wuce bedroom ɗinsa.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now