Page 13

422 57 11
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
'''A True Life Story''' _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Book2
'''Page 13'''

Driving yake amma rabin hankalinsa ba akan tuƙin yake ba. Har wani duhu-duhu yake gani saboda ɓacin rai, a haka ya ƙarasa gidansa.

Yana yin parking ya kira maigadi. Da sauri ya ƙaraso tare da rissinawa.
Zayyan kuwa wayarsa ya fiddo ya shiga gallery inda hotunan Fauwaz suke. "Wannan shine wanda yazo ya ɗauki Amatul'ahad a kwanakin baya?"
"Ƙwarai kuwa, shine Yallaɓai"
"Shikenan! Jeka bakin aikinka."

Kai tsaye ya nufi cikin gidan, bedroom ya wuce ya kwanta, yayinda yaji kansa nayi masa zafi.
Kasa daurewa yayi kawai ya ɗauki waya ya kira Fauwaz.

Ta ɓangaren Fauwaz kuwa yana cikin motarsa, yaƙi ya tada ya tafi, ya dai kwanta jikin kujera kuma ya lumshe idanunsa.
Wayarsa data fara ringing ya janyo, ya buɗe idonshi tare da kallon screen ɗin wayar.
A kunne ya kara tare da cewa "Hello!"
"Fauwaz ina fatan kana lafiya?"
"Lafiya lau"
"Dan Allah idan ba damuwa kazo gidana yanzu, ina cikin damuwa kuma ina da buƙatar ganinka"
"To shikenan, gani nan zuwa"
Katse kiran ya yi, sannan ya tayar da motarsa.

Kai tsaye gidan Zayyan ya wuce.

Bayan yayi parking, yana fitowa daga mota ya ga Zayyan ɗin tsaye a ƙofar main part na gidan.
Da ɗan sauri ya ƙarasa gaban Zayyan ɗin.
"Allah yasa dai lafiya? Naga yanayinka ya canza." Fauwaz ya faɗa, duk da cewa shima yana cikin damuwar.

Zayyan kallon gate yayi sannan ya ce "Yaquba bismillah, zo nan." Ya faɗa da ɗan ƙarfi, yadda Yaquba zaiji
Da sauri Yaquba yazo gurin Zayyan ya rissina.
"Wannan shine wanda yazo kwanakin baya ya ɗauki Amatul'ahad?"
Kallon Fauwaz ɗin yayi sannan ya ce "Eh shine."
"Zaka iya tafiya"
Juyawa yayi ya tafi, shi kuma Zayyan ya mayar da kallonsa ga Fauwaz.

"Ka faɗa min cewa baka san Amatul'ahad ba sai lokacin da ka fara zuwa gidan nan, sannan ka sanar dani cewa baka sake zuwa gidana tun a waccan ranar, to mene ya kawo ka a wancan lokacin? Ka yi min ƙarairayi kala-kala Fauwaz"

"Ban maka ƙaryar komai ba Zayyan" Fauwaz ya faɗa cikin ɓacin rai.
"Idan ba ƙarya ba to mene kayi?" Shima yayi maganar rai a ɓace
"Zayyan duk abinda nayi nayi ne dominka, Amatul'ahad na fara sonta tun lokacin da ta gama secondary school, na dawo nan da niyyar naje neman aurenta. Zayyan kai abokina ne, kuma kai na nema kayi min rakiya zuwa gidansu Habibty, amma sai gashi ina zuwa gidan nan na tarar da ita a matsayin matarka, hakan ya saka na haƙura, ina sonta amma babu yadda na iya domin kuwa ta zama matar aminina, haba Zayyan duk wannan fa na ɓoye maka ne saboda ganin irin muzgunawar da kake mata. Amatul'ahad marainiya ce, kuma tun haɗuwata da ita nayi alƙawarin zame mata uwa data rasa a rayuwa, dan haka aurenka da tayi ba zai hanani na kasa cika wannan alƙawarin ba"
"Ƙarya kake, ai baka taɓa faɗa min kana soyayya da ita ba"
"Baka da wani abu da zan yi maka ƙarya dashi, har sunanta ka sani, sai dai idan ka manta ne"
"Fauwaz kai maci amana ne, ashe kai kake hure mata kunne har ta fara rashin kunya, kuma kana tare da ita ko? Tabbas kai butulu ne, kuma idan ta dawo zan sanar mata taje can ta aureka, tunda kana sonta."
"Wannan shine karo na biyu daka faɗi haka, amma na san ba aikatawa zakayi ba, amma yau na faɗa maka abinda ke raina, ƙaddara ta saka Amatul'ahad ta aikata ba dai-dai ba, kuma ta shiryu shine ba za a tausaya mata ba, ko ba kai ta aura ba, ni ina tare da ita kuma zan bata gudunmawa"

Juyawa yayi zai tafi, yaji Zayyan ya ce "Saboda ba kaine ta gogawa cuta ba, ai zaka faɗi haka"
Juyowa Fauwaz yayi ya kalleshi ya ce "Kaima baka da ita, kawai dai ka kasa fahimta ne."

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now