Page 21

413 45 8
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

Book2
            '''Page 21'''

"Na shigo jami'a ne dan inyi rayuwar ƴanci, zanyi soyayya dan inji yadda garɗinta yake, hakan ne ya saka na ɓoye muku ni matar aure ce, kuma yanzu ma da kuka sani ban damu da hakan ba, ban damu da duk tsegumin da mutane za suyi a kaina ba, dole inji daɗin rayuwa kafin in mutu" Ta ƙarasa maganar cikin tsawa, ta zare gaba ɗayan idanunta da suka canza launi, tana kallonsu.
    "Na san kune kuka kira Fauwaz, saboda ku kuka fi sanina, to kun haɗani da ɗan uwana kunji daɗi" Ta ƙarasa faɗa tana fashewa da wani matsanancin kuka, ta riƙe kanta tare da yin zaman dirshan a ƙasa.

"Ai wallahi ba burgewa bace, kina matar aure ko naman jikinki ake yankawa baici ace kin yi soyayya da wani can da ban ba, ai ke kam wallahi kin shiga uku, ta ina zaki samu daɗin rayuwa bayan kin taka dokar Allah, ai kina ruwa tsamo-tsamo" Azizat ta faɗa tana ƙarasawa jikin trolley ɗinta.
    Minal kuwa tsaki taja ta ce "Sai ki cigaba da soyayya dashi mu gani, ai shi ɗin ba mahaukaci bane, kuma yana bin ƴammatane masu taƙama da virginity ɗinsu, bake da tuni babu shi ba"
   Cikin zafin rai Amatul'ahad ta damƙota suka fara kokowa, da ƙyar Azizat da wasu data kira suka rabasu.

Kowa kuwa rashin gaskiya ya bawa Amatul'ahad, a lokacin kuwa wasu wanda basu santa ba, suka fara tururuwar shigowa ɗakin dan su ga wace Amatul'ahad da ta zama topic ɗinsu a yanzu.

Kan katifarta ta koma taja blanket ta rufe fuska tana kuka.
    "Mu bamu ganki ba, dan Allah ki cire muga fuskarki." Wasu matan da  suka shigo ne suke faɗar haka.

"Ina zata buɗe, ai wanda yayi abin kirki shine baya ɓoye fuskarsa"
   Tanajin yadda kowa ke tofa albarkacin bakinsa amma bata iya tanka musu ba, kuma bata buɗe fuskar ta ta ba.

                        ******

Ɓangaren Fauwaz ƙarfe 12:00pm ya isa Kano.
   Gida ya nufa kai tsaye yayi wanka, ya canza kaya sannan ya nufi ɗakin Momma.

A zaune kan dadduma ya sameta da casbaha a hannu tana lazumi bayan ta idar da sallar walha.
   Gefenta ya zauna, cikin kulawa ta kalleshi ta ce "Ka dawo kenan?"
  "Eh ban daɗe da dawowa ba, na fara watsa ruwa ne kafin nayo nan"
   "Amma ya naga fuskarka da alamun damuwa?"
  Murmushin ƙarya ya ƙirƙiro sannan ya ce "Momma gajiya ce kawai"
   "To ya kamata kaje ka samu kayi bacci kafin azahar ko?"
  "Okay" Ya faɗa yana miƙewa.

                        ******

Fuskarta kamar za tayi kuka ta kalli Mommy ta ce "Mommy number ɗinshi sam bata shiga, kuma naje office ɗinshi har sau biyu ban samu ganinshi" Ta ƙarasa maganar tana matsar ƙwalla.
     "In ban da yaran zamani ma, mu lokacinmu ai ba ayin haka, wasu ma auren dole ake musu su zauna"
    "Mommy ai ku zamaninku da ban, kuma ni babban tashin hankalina daya ambaci Amatul'ahad"
  "To kema ki kwantar da hankalinki Amatur-rahman, kuma ki bi a hankali ki daina kiran wannan sunan kafin kema mahaifinki ya turaki inda ya tura ƴar uwarki. Ina so ki gane ita soyayya ƴar lallaɓoce, cikin hikima zaki ja ra'ayinsa ba wai da garaje ba, ina fatan kin fahimceni?"
Kai ta ɗaga alamar eh.

                     ******

"Yaya ya kamata ka manta komai dan Allah, kaga kana neman ɗorawa kanka hawan jini" Sabrina ta faɗa ranta a ɓace tana kallonshi.
     "Kinje gurin nata?"
Girgiza kai tayi sannan ta ce "Yanzu zan shiga school ɗin, Habiba nake jira ta ƙaraso" Ta kalli Marwan dake gefen gadon ta ce "Yaya Marwan dan Allah ka riƙa bashi shawara, ya riƙa yarda da ƙaddara, kaga haka ya saka kanshi a damuwa akan Amnah ma, ga wannan ma yana ƙoƙarin yin haka"
   "Faman da nakeyi dashi kenan"
   "Gaskiya ya kamata this time ka tausayawa iyayenmu, Daddy har ya shiga damuwa, kuma ka san in ciwonshi ya tashi abin ba sauƙi..." Wayarta da ta fara ringing ta kalla.
  "Habiba ce, ina tunanin tana bedroom ɗina, bara naje"
   Har ta tashi, Sultan yayi saurin cewa "Dan Allah kiyi ƙoƙarin haɗuwa da ita please"
   "Insha Allah"

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now