Shafi na 9

516 50 7
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Written by SaNaz deeyah_👄

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

*Not Edited*⚠️

Book1
            '''Shafi na Tara'''

Jin ya daya bugun ƙofar ne ya saka a hankali taja ƙafarta har zuwa jikin mirrow, drawer ta janyo ta sungumi pad tayi toilet.
   Key ta danna a jiki, zuciyarta da sauri take harbawa, ta shiga tsananin tsoro da firgici. Ruwa mai zafi kaɗan ta haɗa, sannan ta shiga ciki tare da lumshe idanunta.
     _Duniya ba tabbas, ni da nayi rayuwa a gidam iyayena, duk rashin ji na bana taɓa sati ba a gidan ba amma gashi ina karɓar sakamako ina ga wanda suka kwashe kaya suka tafi bariki, wane hukunci za su fuskanta bayan sun dawo?_
  Hannu ta saka tana goge hawayen idanunta, a ranta ta sake furta _Daddy ban cancanci wannan hukuncin daga gareka ba, tun tasowata bani da wani masoyi daya wuce kai, kaine hasken idaniyata, kaine ka reneni har na girma, tun ina ƙarama nake shan wahala a gidanmu kuma girmana ma bai hana sun daina ba, Daddy bai kamata ka yanke alaƙa dani ba, bani da kowa a duniyar nan daya fika._
  _Daddy ba zan taɓa daina ƙaunarka ba, kayi min komai a rayuwa,_
_na san kana fushi dani ne saboda rayuwar dana ɗaukarwa kaina, amma na daina a yanzu, dan Allah ka fahimceni._
  Ta fi mintuna talatin sannan ta fita daga cikin ruwan, sake haɗa wani tayi, tayi wanka sannan ta ɗora alwallah, a tsorace ta ɗoro towel ta fito, ƙofa ta fara kalla ta ganta a rufe dan haka ta sauke ajiyar zuciya cikin jindaɗi.
   Gurin da jini ya ɗiɗɗiga ta saka ruwa da hypo ta goge farin tiles ɗin ƙal, sannan ta kunna tabi ɗakin da freshner.
    Kan gado ta haye, yau ta saka a ranta za ta samu tayi bacci ta samu hitu ko ya ya ne.

                            ******

Fitowa yayi daga side ɗinsa ya ganta zaune kan kujera hannunta riƙe da waya tana ta latsawa, a hankali ya ƙarasa inda take ya zare wayar, tayi saurin juyowa ta kalleshi.
   Hasken wayar ya kashe sannan ya koma kujerar gegenta ya zauna, tare da yin murmushi "Yau kuma laifin me nayi kika ƙi nemana da kika dawo"
     Sumayya kam daurewa tayi ta ƙirƙiro murmushin ƙarya ta ce  "Wallahi yau ban dawo da wuri ba, ai nayi tunanin kaji dawowata"
  "No ina ɗaki fa, ban san kin dawo ba, amma nayi tunanin za ki nemeni"
   "Wallahi nima yanzu ba daɗewa na fito, naga parlorn ba kowa shine na hau danna wayana."
   "Amma ya akai yanzu kike daɗewa haka a gurin aiki?"
   "Hmmm wallahi yau dai an kawo mana wasu mata har uku an masi fyaɗe baka ga abin ba babu kyaun gani, ɗaya kam har ta rasu ana kawota"
    "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wai yaushe Nigeria za ta gyaru ne"
    "To addu'a kawai zamu cigaba dayi, amma gaskiya abin ya ɓaci, mutane babu tsoron Allah a ransu, idan baka da ƙanwa kanata ƴa idan babu ƴa kana da mata idan babu mata kana da uwa idan babu uwa kana da dangi, zaka so ayiwa wani naka ne? Yadda in an yiwa wani naka kaji zafi so kaima bai kamata kayi ba"
    "Wannan gaskiya ne, Allah ya shiga cikin lamuranmu, yayi mana maganin ɓata gari"
    "Amin ya rabbi"
  Shiru ya ɗan biyo baya kafin ta ce "Akwai wata yarinya da treatment ɗinta ke hannuna, itama case ɗin fyaɗe ne, kaga ɗinki a jikinta kuwa, abin ba kyau, kuma fa da anyi ɗinkin kafin ya warke ta lalatashi, ni dai kallon karuwa nake mata karuwarma mara galihu, amma a ƙaryarta ta ce wai mijinta ne ke mata"
     "Haba ƙarya take, mijinka yayi maka fyaɗe"
    "Kuma ba sau ɗaya ba, kusan kullum, ni dai na faɗa mata muddin ba za ta bari ta warke ba to za ta lalata private part ɗinta"
    "Allah ya kyauta, amma gaskiya kina ƙoƙari, ni sam ba zan iya wannan aikin ba"
    "Hmmm bata kama ka bane, Allah Fauwaz da zaka je ɗakin mata ɓangaren gynecology wallahi sai ka tausaya, idan kana da rauni ma sai ka zubda hawaye idan ka ga wasu."
   "Allah ya basu lafiya mu kuma da muke da ita Allah ya ƙara mana"
   "Amin."
   Miƙa mata wayar yayi ta karɓa.
   "Bari naje wajen Daddy"
"Okay sai ka dawo"
Wucewa yayi ta bishi da ido, a zuciya ta furta _Ina matuƙar ƙaunarka Fauwaz, ina fatan Allah ya karkato da hankalinka gareni, ka fara sona kamar yadda nake sonka  koma fiye da haka._

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now