Page 9

408 62 6
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

*Zafin Hawayena Fans Page ina godiya sosai, a gaskiya kuna ƙoƙari wajen suburbuɗo sharhi. Wannan shafin na sadaukar dashi gareku.*

_*Dan Allah duk wacce ta san sticker ko thanks za ta bini dashi idan nayi posting to bana so, ai dama na san kun gode, amma inga sharhi shine zan gane kuna karanta novel ɗina*_

_*Ku kuma ƴan Wattpad kuji tsoron Allah, kaɗan daga cikinku ne suke yin vote da comment amma dana ɗaura kuke viewing, gaskiya ku riƙa voting da comment idan ba haka ba ko nayi posting zan riƙa ɗaukar lokaci kafin na ɗora maku, masu comment da voting ɗin cikinku ina godiya sosai, kuma wannan page ɗin sadaukarwa ne gareku.*_

Book2
            '''Page 9'''

Yana shigowa ɗakin ya tarar da Zaliha tsaye jikin gadon, ta ƙurawa Amatul'ahad ido.
   Shi ma gaban gadon ya tsaya yana kallonta, a lokacin ne Zaliha ta ɗan koma gefe, saboda tana mugun ganin girmanshi a idanunta.

"Insha Allah kin daina kuka Amatul'ahad, Allah ya baki lafiya"

"Amin dan Alfarmar annabi Muhammad(SAW)" Zaliha ta amsa kanta a duƙe.

"Ko ta tashi in bana nan, kada ki barta ta fiya surutu" Ya furta yana kallon Zaliha.

  "To insha Allahu"

"Zan je na dawo, akwai abinda kuke buƙata?"
    Girgiza kai tayi alamar a'a.

                      *****

Yana fita kai tsaye office ɗin Zayyan ya wuce, dan ya san a nan kaɗai zai iya samunsa a yanzu.
 
Kai tsaye ya shiga office ɗin, domin sakataren ya san matsayin Fauwaz a wajen uban gidansa.

Glass ɗin dake fuskarsa ya cire lokacin da Fauwaz ɗin ya shigo.

Murmushi kawai Fauwaz yayi kafin ya samu guri ya zauna.

"Banyi tunanin za ka sake zuwa inda nake ba, a yanda muka rabu"      Zayyan ɗin ya furta idanunsa a cikin na Fauwaz.
   Murmushi Fauwaz ya sake yi, kasancewarsa ma'abocin murmushi.
   "Nima nayi mamaki matuƙa, da ka amshe ni, ba tare da ka wulaƙantani ba"
   "A waccan ranar ma raina ne a ɓace sosai, saboda maigadi ya tabbatar min da kaine kazo ka ɗauki Amatul'ahad"
   "Maigadi kuma ya fini matsayi shiyasa baka ko tambayi ba'asi ba kawai ka yanke hukunci"
   "I made a mistake, wallahi sai bayan dana huce kawai naji sam ban kyauta ba, kuma naji kunyar zuwa na baka haƙuri"
   "Hakan ya nuna kana son matarka sosai"
   "Ko kaɗan, nayi hakane dan ina tsoron karka faɗa tarkonta, ta shafa maka muguwar cuta"
   "Har kana tunanin zan fara rayuwar da banyi ba a lokacin da nake tashe"
   Murmushi Zayyan yayi.

Fauwaz ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa "Ka ce matarka a New York tayi karatu, haka nima a can nake gudanar da rayuwata, amma a yanzu na zo in cire maka shakku ne"
   Zayyan gaba ɗaya hankalinsa ya mayarshi kan Fauwaz. Yayinda Fauwaz ya cigaba da cewa "Zayyan kamar a Nigeria ne, kai yanzu zaka ce min ka san kowa a cikinta?"
     "A iya faɗin garin nan ma ba kowa na sani ba"
  "To bare New York da tafi nan. Ni gaskiya ban san matarka ba, ban kuma taɓa ganinta ba sai ranar da naje gidanka ka nuna min ita, sannan tun daga wannan ranar har yau ban sake ganinta ba."
     "Wani shashashan maigadi na samu da baya gane mutane, amma ina kyautata zaton tana asibiti dan bata da gurin zuwa sai can"
    "To me zai hana ka bincika?"
   "Na damu da ita kenan, ai wallahi ba bincikar da zanyi, kuma daga zarar ta dawo zan mayar da aikin sabo"
   Ɗan runtse ido Fauwaz yayi, sannan ya buɗe "Wai dan Allah kai kuwa yaushe ka koyi mugunta?"
    "Hmmm ba zaka gane bane, cutar HIV fa ba abar wasa bace"
    "Amma kai ka gwada, ka kuma tabbatar da haka?"
    "Wai wani gwaji ga gaskiyar lamari, dan ma har yanzu a matakin farko nake, sawa nake a kawo min magunguna masu tsada su nake sha, dan bana son ma ta fara nunawa a jikina, har in mutu"
   "Amma yana da kyau kaje kayi gwajin"
   "Tonan asiri kenan, to ai ko Family Doctor ɗinmu ba zan iya cewa ya gwadani ba"

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now