Shafi na 17

456 45 2
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Book1
            '''Shafi na sha-bakwai'''

Not edited

*Bayan Kwana Biyu*

Tana kwance akan sofa, ta lumshe idanunta, kanta na sara mata sosai, ba bacci take ba, amma idan ta buɗe idon ji take tamkar kanta zai fashe, sam bata son ganin haske.
    Turo ƙofar Zaliha tayi ta shigo, sannan ta durƙusa gabanta. "Aunty na gama shiryawa"
   "Zaliha..."
  "Na'am Aunty"
    "Ina so dan Allah ki sanar dani, shin wane irin yanayi karuwai suke shiga yayinda suka tuba?"
  Shiru Zaliha tayi, ta kasa cewa komai.
   "Zaliha shin idan mutum yana aikata abinda ba dai-dai ba, kuma yazo ya shiryu bai cancanci sassauci  ba? Me nayiwa rayuwa? Meyasa ni ba zan samu sassauci da kuma jindaɗin rayuwa ba?"
   Da sauri Zaliha ta dafa ƙafafun Amatul-ahad "Aunty kiyi haƙuri, komai da kika gani a rayuwa dole idan yayi farko zaiyi ƙarshe, kuma insha Allahu nan ba da daɗewa ba, za ki samu sassauci"
    Tashi tayi a hankali ta zauna, sannan ta goge hawayen da bai bar zuba ba. "Nima addu'a nake a koda yaushe, ina so in samu sassauci kafin na koma ga mahalicci"
   "Za ki samu Aunty, insha Allah wannan hawayen naki, wata rana zai koma hawayen daɗi"
  "Allahu yasa"
    "Amin ya rabbi"
    "Ki ɗauko min hijab ɗina, sannan ki faɗawa Sani ya fito da mota muje asibiti, naji kamar jinina na neman ƙarewa, ga zazzaɓi inaji"
  Da sauri Zaliha ta miƙe ta nufi closet.

                     ******

Daga kan kujerar da take zaune tayi saurin sauke ƙafafunta ƙasa. "Yaya dan Allah kayi haƙuri akan maganganun dana faɗa maka ɗazu raina ne ya ɓaci, kumaban san haka abin yake ba, ka san har yanzu ina son Zayyan, kuma naji zafin abinda ya faru dashi, amma kuma babu yadda za ayi na cireka daga sunan ɗan uwa, domin a ƴan uwan ma kai na da ban ne"
   Murmushi yayi sannan ya ce "Babu komai, kada ki damu"
  "Amma Yaya dan Allah....." Da hannu ya dakatar da ita sannan ya ce "A yanzu bani da nutsuwa dan haka dan Allah kada kiyi min wata magana"
   Shiru tayi tana kallonsa, shi kuma ya cigaba da faɗin "Ki tashi kije kiyi abinda za kiyi, nima zanje gurin Sumayya dan na san tana jin hsushina, amma kafin nan zan fara zuwa....amm...." Kallonta yayi yaga tana murmushi.
   "Ki je kawai, na gama dake"
  Tashi tayi ta bar gurin da ɗan saurinta, shi kuma ya ɗauki key ya fita.

Kai tsaye gidan Zayyan ya nufa, bai kirashi a waya ba, bai kuma san me zai faɗawa Zayyan ba,shi dai kawai so yake yaje ya kuma ga Habibty'nsa, ya kuma bata haƙuri akan abubuwan da suka faru.

                      *******

A fusace ta fito daga ɗakin, da sauri nurse ɗin ta biyota. "Ranki shi daɗe ya naga kin fito ba tare da kin ce komai ba?"
   "Indai wannan ce, ba zan duba ta ba, bata san ciwon kanta ba, dan haka a samu wani wani ya dubata, ko kuma su nemi wani asibitin" Tana gama faɗa ta wuce abinta, ita kuma nurse ɗin ta koma cikin ɗakin cike da tausayawa"
   Da sauri Zaliha ta ƙaraso gurin ta ce "Dan Allah ku taimaka mata, tana jin jiki wallahi"
   Kallon inda Amatul-ahad take sukayi, tana zaune kan gado, ta daddafe hannayenta  kan gadon, tana cije ƙeɓe yayinda take sauke numfashi ɗaya bayan ɗaya.
    "Idan har nace zan haɗa Dr Sumayya da wani, to zan iya samun matsala a aikina, dan  haka zan nuna miki office ɗinta, kije ki ƙara roƙonta"
    "To ki nuna min dan Allah"
  Da sauri za ta ƙarasa gurin Amatul-ahad ta ce "Sannu Aunty, za tazo yanzu ta dubaki insha Allah."

                        *******

A ƙofar gate yayi parking yayi horn, da sauri maigadi ya buɗe ƙaramar ƙofa ya fito.
    Sauke glass yayi suka gaisa sannan ya ce "Zayyan baya nan?"
    "Eh gaskiya ya fita tun safe"
    "Matar gidan fa?"
  Shiru yayi har sai da Fauwaz ya sake cewa "Tana ciki?"
  "A'a yallaɓai itama yanzu nan suka tafi asibiti,ni kaɗai ne a gidan"
    "Ko za ka san asibitin da suka tafi?"
    "Eh to, wallahi na manta sunan, amma dai bari na baka lambar Sani dan shine ya kai su"
    "To babu matsala bani number tashi"
  Miƙa masa yayi ya saka number sannan ya bashi wayar.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now