Shafi na 5

537 45 2
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
'''A True Life Story'''
_Written by SaNaz deeyah_👄

*K.W.A📚*

Book1
'''Shafi na biyar'''

A firgice ta miƙe zaune, kallon ɗakin ta ƙarayi ta tabbatar a ɗakinta take. Miƙewa tayi daƙyar tana mai cije leɓe dan yadda take jin zugin azaba a gabanta.
Fita tayi daga ɗakin ta fara sauka down stairs, a zuciyarta tana furta Allah yasa mafarki take.

Saddiqa ta ɗan zunguri Jamila da suke rashe a falon ƙasan carpet suna kallo.
Kallonta Jamila tayi murya a ƙasa ta ce "Wallahi ta zuge kamar mai gudawa"
"Ke dalla kiyi shiru karta jimu."

Amatul-ahad na ƙarasa saua ta kalli Saddiqa "Ba muyi baƙuwa a gidan nan ba?"
"Au Hajiya dama akwai wadda ta ce za ta zo ne?"
"Tambayarki nake kina tambyata." Amatul-ahad tayi maganar.
"Babu wadda tazo" Saddiqa ta furta rai a ɓace.
Amatul-ahad hamdala tayi a cikin ranta, sannan ta juya za ta koma ɗakinta.

"A haka za ki ƙare" Saddiqa tayi magana ƙasa-ƙasa. Juyowa tayi ta kallesu.
"Wacece ta faɗi wannan maganar?"
"Hajiya wace magana kuma, mu fa babu abinda muka ce" Cewar Saddiqa sannan ta juya ta kalli Jamila "Ko kin ce wani abu?"
"Ni wallahi bance komai ba."
A dai-dai lokacin Zaliha ta shigo, hannunta ɗauke da plate an rufa wani a kansa.
Tsayawa tayi ba tare da ta ce komai ba, Amatul-ahad ta kallesu ta ce "Naji wata tayi magana, kuma naji abinda ta faɗa, kuma ya kamata kuji tsoron Allah, me nayi muku?"
"Aunty dan Allah kiyi haƙuri ki rabu dasu, koma me suka faɗa kansu sukayi wa"
"Lalacewar har ta kai ƴan aiki su riƙa jifana da baƙar magana? Ba kowa bane ya jawo min ba sai Zayyan, da ya mutuntani da baku min haka ba."

Juyawa tayi ta koma upstairs, Zaliha tabi bayanta.
Saddiqa taɓe baki tayi, yayinda Jamila ta ce "Wannan Zalihar munafuka ce"
"Ki rabu da ita cusa kai ne, dan a samu gindin zama"
"Shiyasa wallahi na tsaneta, baza tazo nan mu haɗa kai ba"
"To baki ga maigidan ma ya tsaneta ba, saboda yadda take da shishshigi."

Ta ɓangaren Amatul-ahad tana shiga ta kwanta kan Sofa, duk ƙoƙarin da tayi dan ganin ta hana hawayen idanunta fitowa amma sai da suka zubo.

A kan table Zaliha ta ajje plate ɗin, sannan ta dawo ta zauna ƙasan Sofa tare da faɗin "Aunty ba wai zan zuga ki bane, amma mu ƴan aiki ne, ko da ace maigidan nan gutsurar naman jikinki yake, muna nan a ƴan aiki kuma dole mu baki girmanki matsayinki na matar gidan nan. Aunty ki ɗauki mataki akan Saddiqa da kuma Jamila, koma wane irin matakine tun kafin su fara fitar da sirrinki zuwa maƙotanki."
Tashi tayi daga kan Sofa, ta ƙarasa jikin table ɗin taja kujera ta zauna, sannan ta ɗauki tissue tana goge hawayen idanunta.
"Me suke faɗi game dani?" Sai a lokacin Amatul-ahad tayi magana.
"Maganganu mararsa daɗi, ki gafarceni, amma ba zan iya faɗa miki ba, ni dai ina so ki ɗauki mataki tun kafin abin yayi yawa"
"Ba damuwa, za ki iya tafiya."
Tashi Zaliha tayi ta fita tare da jawa Amatul-ahad ƙofa.
Ajiyar zuciya ta sauke gami da ɗora kanta a table ɗin.

******

Da sauri ya fito yana kallon agogon hannunsa, sanye yake da ƙananan kaya, ya nufi parking lots. Ramlat ce ta fito da sauri ta ƙarasa inda yake.
"Yaya ai nayi tunanin sai next week za ka fara zuwa aiki, naga kana ta sauri"
Juyowa yayi yana kallon Ramlat fuskarshi ɗauke da murmushi, kasancewarsa mutum mai fara'a, da wuya a ganshi fuskarsa ba wannan fara'ar. "Zan je inda bakya so."
Ɗan zaro ido tayi ta ce "Ina kenan?"
"Zanje gurin Zayyan dan na san definitely yanzu yana Office"
Ɗan buga ƙafa Ramlat tayi tana turo baki ta ce "Yaya meyasa ba za ka manta da Zayyan ba, baya so ya faɗa maka gaskiya, sannan kai kuma kace dole sai kaje kaji, is it by force?"
"Yeah it is by force, I'm his best friend, bai isa ya ɓoye min duk wani abu nashi ba"
"Yaya ba fa zakayi forcing na Zayyan ya faɗa maka gaskiya akan abinda baya so mu san gaskiyarsa, Zayyan yayi aure yes yayi aure, ya yaudareni, so kuma ya janye wannan alaƙar dake tsakaninku, so tunda haka ya zaɓa please let it be."
Ɗan murmushi yayi yana kallonta sannan ya ce "Ramlat ni na san auren nan da Zayyan yayi there most be something behind, so zan je inji koma mene dan a samu warwara, dan na tabbatar kunya ce ta hana Zayyan zuwa gidan nan."
"To shikenan tunda haka ka ce, amma dama magana nake so zamuyi kuma gashi za ka fita"
"Okay maganar akan me?"
"Aunty Sumayya mana, maganar kuma tana da maruƙar muhimmanci"
"Idan na dawo sai muyi ko?"
"I hope dai ba daɗewa za kayi ba?"
"Eh insha Allah"
"Saboda ina so muyi magana kafin Aunty ta dawo"
"Ba matsala"
Ita ta karɓi key ta buɗe masa mota ya shiga.
"To Yaya sai ka dawo"
"Allah yasa"
"Amin ya rabbi."

******

A wajen da aka tanada na parking motoci anan yayi parking ɗin tashi.
Yana sauka kai tsaye office ɗin Zayyan ya wuce, tunda dama ya san ko ina a gurin.
Secretary bai hanashi shiga ba kasancewar dama already ya san matsayinsa a gurin ogansa.

Handle ya murɗa ya shiga office ɗin, bakinsa ɗauke da sallama.
Zayyan na tsaye yana duba wasu takardu ya ɗago da niyyar yayi faɗan shigowa ba tare da anyi knocking ba, sai ganin Fauwaz yayi a tsaye.
"Oh Fauwaz ashe kaine, you are welcome"
Ya furta yana shafa kwantacciyar sumarshi.
Fauwaz kuwa bai motsa daga inda yake ba sai ma hannu daya harɗe a ƙirji yana yi ma Zayyan kallon tuhuma.

Da kanshi ya ƙaraso ya jashi ya zaunar, sannan ya zauna a kujerar kusa da tashi.
"Na san nayi laifi da ban zo nayi maka barka da sauka ba, amma aiki ne yayi min yawa ina fatan zaka min afuwa."
"Babu afuwar da zan yi maka, domin kuwa kai mai laifi ne a gurina, ka yi aure ba tare da ka sanar da kowa ba, kuma har dani dana kasance amini a gareka, wannan dalili ne ya hanaka zuwa gidanmu ba wai aiki ba."

Ajiyar zuciya ya sauke, ya hura iska a bakinsa ya furzar, sannan ya kalli Fauwaz cikin yanayi na damuwa, ya fara magana.
"Maganar bikina nayi tunanin ma tuni an faɗa maka, wannan dalilin shine ya hanani zuwa, Fauwaz ba kowa ne zai fahimci halin da nake ciki ba, amma tabbas ina cikin damuwa kuma na san Ramlat ba zata taɓa yarda cewa ban ci amanarta ba, su Momma kuma wallahi kunyar haɗa ido nake dasu shiyasa tun da nayi aure banje ba"
"To ai rashin gaskiyarka za su gani tunda baka je ba, sannan baka faɗa masu komai ba, musamman ita Ramlat ta faɗa min har jinya tayi lokacin da taji kayi aure."
Murmushin takaici Zayyan yayi, sannan ya miƙe ya nufi fridge. Lemo da ruwa ya ɗauko, ya haɗo da cups sannan ya kawo ya diresu gaban Fauwaz.
"Ni ba ruwa ko lemo bane a gabana, nazo ka faɗa min dalilin dayasa kayi aure kaƙi sanar dani"
"Fauwaz ina son Ramlat, har yanzu da soyayyar Ramlat a cikin raina."

Buɗe waya Fauwaz yayi ya danna recording ba tare da Zayyan ya gani ba. Kallon shi yayi ya ce "Idan kana son Ramlat meyasa ka gujeta?"
"Ban guji Ramlat ba, Fauwaz ƙaddarata ce tazo a haka, rayuwa nake amma ina jina kamar ba a duniyar mutane nake ba, Fauwaz ina ɗauke da cutar HIV."

Cikin tashin hankali Fauwaz ya miƙe tsaye, yana ƙara lumshe sexy eyes ɗinsa cike da rashin nutsuwa.
Murmushi Zayyan yayi tare da cewa "Na san kai ba zaka taɓa guduna ba, shiyasa na faɗa maka halin da nake ciki"
Zama Fauwaz yayi a fili ya sauke ajiyar zuciya yana mai ƙarewa Zayyan kallo.
Kwalin lemo Zayyan ya buɗe, ya tsiyaya a cups ɗin, ya ɗauki ɗaya sannan ya miƙawa Fauwaz ma.
Karɓa yayi ba musu ya sha sosai, sannan ya ajje, har a lokacin idanunsa akan Zayyan.

"Zayyan ka sakani a duhu, ni gaba ɗaya ka kwance min tunani"
"Na san za kayi mamaki sosai"
"Amma a iya sanina Zayyan baka neman mata"
"Har yau ban taɓayi ba, to dame ma zanyi, wa ce zata yarda tayi sex da mai HIV"
"Ka daina faɗin haka, ni na san baka da HIV"
Cikin yanayi na mamaki Fauwaz ya sake faɗin "To waye ya goga maka? A ina ka samu tunda baka neman mata?"
"A gurin mahaifina na samu"
Gaba ɗaya Fauwaz ya zaro manya idanunsa cike da mamakin furucin Zayyan.

Kuyi mana SUBSCRIBE a youtube channel ɗinmu mai suna KARAMCI TV

Kuyi following ɗina a Wattpad @SaNaz_deeyah

Sadeey S Adam✍️

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now