Page 22

471 52 37
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on Facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on Facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

SUBSCRIBE to our youtube channel👇https://youtube.com/c/KARAMCITV

Book2
            '''Page 22'''

Kwanciya yayi kan gadonshi, ya lumshe ido tare da faɗawa duniyar tunani.
   _Zuciyata taƙi yarda tayi sati ɗaya ba tare da nayi unblocking Amatul'ahad ba, amma gaskiya ni ba zan iya bari haka ta cigaba da faruwa ba, idan ta fahimci cewa zan iya yafe laifinta a koda yaushe, to kuwa zata cigaba dayi ne, amma idan taga na ɗauke mata ƙafa, to nan gaba ko wani abun za tayi dole sai da sanina._
  Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke sannan a zuciyarshi ya sake furta _Ta ya zan amince da soyayyar Amatur-rahman? Ai ko ina hauka ba zan taɓa ƙaunarta ba._

Idanunsa ya buɗe ya janyo wayarshi, sannan yayi dialing ɗin number Minal. Tana shiga ta ɗaga.

"Hello!"
"Hi! Ya kake?"
"Lafiya lau, ya karatu?"
"Karatu muna ta fama, an kusa fara exams"
"To Allah ya taimaka ya kuma ba da sa'a"
"Amin ya rabbi"
"Amm...ya Amatul'ahad ina fatan tana lafiya?"
"Eh lafiya lau, tana nan, yanzu ma ta fita"
"Batayi magana ta ba?"
"Tayi mana, ai tana ta cewa wai mu muka haɗata da ɗan uwanta"
Murmushi yayi sannan ya ce "Ai kun kyauta, wannan shine zaman tare, idan ɗan uwanka yana ba dai-dai ba, ka faɗa masa bai gyara ba, sai ka samu wani nasa ka faɗa masa, ni naji daɗi da kuka faɗa min tun kafin abu ya lalace"
"Ai amfanin zaman tare kenan"
"Ina fatan zaku cigaba da kula min da ita"
"Insha Allah"
"Madallah! Allah ya baku sa'a akan abinda kuka je nema"
"Amin ya rabbi."

Tana ajje waya ta doka uban tsalle, tare da faɗawa kan katifar Salma, ta rungumi teddy ɗin Salma.
  "Ikon Allah, ni dai ban ga alamar da saurayi kike waya ba, amma gashi kuma kin shiga shauƙi" Azizat ta faɗa tana kallonta.
Salma ta ƙara da faɗin "To kika sani ko haukan nata ne ya motsa"
Tashi zaune tayi, tare da ɗaukar pillow ta saka kan cinyarta.
  "Yayan Amatul'ahad ne ya kirani, wallahi hausar shi ma daɗi kamar balarabe, kai gayen ya haɗu"
   "Taɓ kin wahala kuwa, dan kin san Amatul'ahad ba zata taɓa yarda ba, musamman da kika je kika haɗa mata cakwakiya"
   "To ai ba Yayarshi bace, bare taƙi yarda kuma a ƙyale, shine a samanta, idan ya ce yana sona wallahi bata isa ta hana ba, sai dai tayi ta jin haushina"
   "To ke da kika tsaneta mene na son Yayanta?"
  "Ni fa ban tsani Amatul'ahad ba, haushinta kawai nake ji akan Sultan, domin mun faɗa mata gaskiya ta mayarmu ƴan iska"
   "To ai da sai ku ƙyaleta ina ruwanku, ku da ba ku kuka kawota makarantar ba, kuma ba kune kuke biyan registration fee ɗin ta ba"
     "Amma ai tare muke, yanzu ba gashi nan ba kinji tana da aure, tare muke dan haka ko mene ya sameta mu za a zarga."
 
                       *******

Marin da Mommy ta kwaɗawa Amatur-rahman har sai da ta kusa kifawa.
    Sosai ta riƙe kuncinta ta ɗago tana kallonta.

Cikin ɓacin rai ta ce "Wallahi! Kin ji na rantse miki, muddin kika sake kawo min irin wannan maganar sai na saka ya kaiki can china, kuma ba zaki dawo ba sai kin gama karatu tas"

"Mommy mene laifina akan abinda na faɗa? Mommy kefa kika ce dan mu kike komai a gidan nan, amma na kawo miki matsalata kika mareni"

"Na mareki ko za ki rama ne in baki kumatuna?" Ta furta a fusace.

"Shikenan!" Abinda Amatur-rahman ta faɗa kenan tare da yin side ɗinta.

Kan gadonta ta zauna tare da haɗe fuska, har a lokacin ranta a ɓace yake sosai, wai Mommy ta mareta dan kawai ta faɗi buƙatar Fauwaz a gareta.
   _Wallahi ina son Fauwaz, ba zan taɓa zama ina ji ina gani na rasa shi akan abinda zamu iya solving ɗinsa._
Saitin zuciyarta ta taɓa, ta lumshe ido, sai a lokacin wasu siraran hawaye masu zafi suka zubo mata.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now