Shafi na 20

516 46 8
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Book1
🔚
            '''Shafi na ashirin'''

"Babu abinda za ka iya yi, baka da wata mafita da ta wuce addu'a, nima ita nakeyi a koda yaushe, da ace ina da wata mafita bayanta, da tuni na nemowa kaina ita. Fauwaz har yanzu ban cika wata guda a gidan Zayyan ba, amma azabar da nake sha ji nake kamar nayi shekara ɗari a gidansa, ban san yadda azabar lahira take ba, sai dai ana kwatanta mana, to misalin haka ne rayuwata a gidan mahaifina da kuma gidan Zayyan, har yanzu dai ban yanke ƙauna da samun rahamar ubangiji ba, har yanzu dai bana jin cewa ina ma in mutu in huta, a'a ina son in samu soyayyar gaskiya kafin mutuwata Fauwaz." Ta ƙarashe maganar muryarta na sarƙewa.
   Hannu ya saka ya ɗan rufe fuska, ji yake kansa na sarawa, yayinda zuciyarsa take raɗaɗi, meyasa bai sanar da ita ba tun a farko, meyasa yayi wannan kuskuren.
  "Ni ne sila, da ace na furta miki kalmar so a lokacin da kike ta biɗa, da duk haka bata faru ba, dan Allah ki yafe min"
     "Fauwaz... Ban taɓa kawowa haka zata faru da rayuwata ba, ban taɓa tunanin cewa abinda nake ƙyamata nima za azo a ƙyamaceni dashi, na ɓata rayuwata ta yadda babu wanda zai tausaya min, babu wanda zai yadda cewa ba cikin hankalina nake ba. Amma Fauwaz nayi rayuwar da ko da ance inada HIV babu wanda ba zai yarda ba" Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka, shi kuma ya kafeta da ido kawai.
   Kanta a ƙasa ta cigaba da faɗin "Amma ban taɓa tunanin dan nayi wannan rayuwar na tuba zan fuskanci wannan matsalolin, wanda suka aikata abinda yafi nawa muni ma ba a ƙyamace kamar ni ba, bani da kowa Fauwaz, ka san bani da dangin uwa, dangin uba gaba ɗaya sun gujeni, haka ƙannena, da kuma mahaifina, wanda shine katanga a gareni."

Shiru ne ya biyo baya tana ta shashsheƙar kukanta har tayi ta gama, ta share hawayenta sai kuma ta kalleshi, taga ita yake kallo har a lokacin.
    "Fauwaz a yanzu ina cikin damuwar da bana iya ɓoyewa."
   "Amatul-ahad insha Allah za kiyi murmushi, kuma zakuyi rayuwa cikin jindaɗi kamar kowa, in Allah ya yarda ni zan saka mahaifinki ya dawo da soyayyar da yake miki ta ninka ta baya, kuma zan shawo kan mijinki ya fara sonki kamar bai taɓa wulaƙantaki ba."
      "Taya hakan za ta faru? Bayan aikin asiri ne?"
   "Insha Allah zan san abinyi"
Kai kawai ta gyaɗa, shi kuma ya tashi ya fita.

Da nurse ya dawo, ita dai Amatul-ahad ido ne kawai nata.
  "Ga ta nan sai ki ɗauka ko?"
    "Okay" Ta faɗa sannan ta ƙarasa jikin gadon.
  "Zamu ɗauki jininki"
  Kai kawai ta gyaɗa, ta buɗe hannu tare da lumshe ido.

Bayan an gama ɗauka nurse na fita ya bita, dan haka bata samu damar yin magana dashi ba.

*Few Hours Later*

Tana zaune bisa gado hannunta riƙe da counter tana dannawa bakinta na motsawa, babu kowa a ɗakin, Zaliha ta fita zuwa gida dan ta canzo mata wasu kayan.

Da sallama Fauwaz ya shiga, tunda ta ɗaga kai taga shine tayi saurin sauke ƙwayar idanunta ƙasa.
  Kan kujera ya zauna sannan ya miƙa mata takardar hannunshi. Kallon shi tayi ta kasa magana kuma taƙi karɓa.
  "Ki karɓa ki duba result ɗinki ne da akayi gwajin HIV"
Gabanta taji ya faɗi, ta kalleshi taga fuskarshi babu fara'a.
  Jikinta gaba ɗaya karkarwa yake, tsoro kuwa tuni ya bayyana a fuskarta.
   "Amatul-ahad ki karɓa"
Girgiza kai tayi ta saka hannu ta rufe fuskarta.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ajje takardar kan cinyarsa, kallonta yayi yaga yanda tabi ta firgice.
  "Har yanzu wannan tsoron naki yana nan ko? Ba za ki daina ba, naga abin ma ƙaruwa yayi"
   Bata ko ɗago ta kalleshi ba bare ta bashi amsa.
  "Amatul-ahad idan har kina son farin cikinki to dole sai kin cire tsoro kinyi yaƙi da abinda ya tunkaroki, ni zan shige miki gaba, wannan sakamakon gwaji ne, da yake nuna baki da cutar ƙanjamau, da kaina zan ɗauka in kaiwa mijinki ya gani sannan in kaiwa mahaifinki"
  Ɗagowa tayi ta kalleshi sannan ta kalli takardar, wasu zafafan hawaye ne suka sauka a kuncinta.
   "Da yardar Allah wannan sakamakon shine zai samo miki sassauci daga gurin Zayyan da kuma Daddy"
   "Nag..." "Kada kiyi min godiya Amatul-ahad, zan iya komai dan ganin na faranta miki, tunda ni ban sameki ba,  insha Allah ni zan zamo silar  farin cikinki, ina Zaliha?"
   "Taje gida ta dawo"
  "To bari ta dawo sai in tafi, dan kada mu barki ke kaɗai"
   "Yaushe za'a sallameni?"
  "Kin gaji da zaman asibitin?"
  "Na taho ba da iznin Zayyan ba, na san zan fuskanci mummunan hukunci daga gareshi"
   "Babu abinda zai miki, kin san mene?"
  Girgiza kai tayi alamar a'a
  "Daga nan gurinshi na nufa, zan sameshi har office, kuma tare zamu dawo dashi nan, ya baki haƙuri ki fara ganin soyayyarsa a gareki"
   "Allah yasa"
"Allahumma Amin."

                 *****

Yana fita daga cikin asibitin ya kira number Zayyan lokacin ya hau titi.
  Tana fara ringing Zayyan ya ɗaga tare da yin sallama. "Ina son mu haɗu yanzu akwai muhimmiyar magana da zamuyi, a ina zan sameka?" Shine abinda Fauwaz ya faɗa lokacin da Zayyan ya ɗaga wayar.
   "Ina office Allah yasa dai lafiya?"
  "Lafiya lau, gani nan zan zo office ɗinka na sameka.
   "Okay to sai ka zo."

                           *****

Da hannu ta tarar da napep, bayan ta shiga ta zauna har sai daya tambayeta inda zai kaita, sannan ta tuna cewa bata ma san taƙamaimai inda za taje ba.
     Waya ta zaro a jaka sannan tayi dialing number Amatul-ahad, gabanta na faɗuwa dan tana tunanin bama lallai ta ɗaga ba.
    "Malam dan Allah bari nayi kira a waya sai mu tafi"
   "To ba matsala"

Ta ɓangaren Amatul-ahad kuwa tana daga kwance kan gado wayar na gefenta ta fara ringing.
  A hankali ta ɗauka, ta duba taga baƙuwar number ce, a hankali ta ɗaga tare da cewa "Hello"
   Daga ɗayan ɓangaren Islaha ta ce "Hi, Amatul-ahad ya kike?"
  "Lafiya lau"
  "Baki gane mai magana ba ko?"
  Ajiyar zuciya tayi a hankali ta ce "Na gane mana, ya gida"
  "Lafiya lau, ya jikin naki?"
  "Da sauƙi"
   "To Allah ya ƙara sauƙi, yanzu kina asibiti ko an sallamoki?"
   "A'a ina asibiti"
   "Idan babu damuwa ki faɗa min address ɗin"
   "Okay bari nayi miki text ɗin gurin"
     "Okay."

                       ******

Zayyan murmushi sosai yayi sannan ya kalli Fauwaz ya ce "Surprise na me?"
   "Yanzu ai za ka gani, kuma na san abin zai matuƙar baka mamaki"
   "To ina jira"
  Miƙa masa takardar yayi sannan ya ce "Ka duba ka gani wannan sakamakon gwajin da aka yiwa Amatul-ahad ne, ka duba result ɗin."
   Tuni fuskar Zayyan ta koma ɓacin rai, ya haɗe rai kamar bai taɓa fara'a ba.
   "Zayyan na san ka tsani matarka saboda tana da cutar HIV amma wannan shi zai share maka tantama"
  Tura masa takardar yayi gabansa sannan ya ce "Yana da kyau ka duba"
  Kallon Fauwaz ya tsaya yi kafin ya ɗauki takardar ya buɗe.
   Fauwaz kallonshi kawai yake yadda yaga yana ƙara haɗe rai.
  Ɗagowa yayi ya kalleshi sannan ya ce "Fauwaz meyasa za ka kawo min abinda na daɗe da sani"
    "Ban fahimta ba?"
  "Eh wannan result ɗin ai na daɗe da sanin yadda yake"
  "Oh kenan ka san bata da HIV amma kake gana mata azaba?"
   "Fauwaz ko dai kasha wani abu? Ko kuma dai idanunka basu gani" Miƙa masa takardar yayi tare da cewa "Zaka iya ƙara dubawa ka gani"
  Ya miƙa masa sannan ya zura masa manyan idanunsa.
 
Fauwaz miƙewa yayi tsaye, ya kafe takardar da ido, abin ya matuƙar bashi mamaki.
   "Ban sauka a ko ina ba bare nace wani ya canza min wannan result, daga asibiti, direct nan nayo, meke faruwa ne?" Ya faɗa idanunsa akan takardar da result ɗin gaba ɗaya ya juye daga negative zuwa possitive.
    "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
   Shine abinda yake ta nanatawa.

"Na san komai, duk abinda ke faruwa da Amatul-ahad DA SANINA." Zayyan ya faɗa yana kallon Fauwaz.

*Wannan shine ƙarshen Book1 mu haɗu a book2 domin jin cigaba labarin. Kada ku manta da wannan labarin, domin book2 zai iya zo muku a ko wane lokaci da zarar na zama less busy, ba lallai sai dec ba*

_*Labarin nan ya faru a gaske, labarin nan yanzu aka fara, labari ne mai taɓa zuciya, akwai wasu darussa a cikin labarin da nakeson gaba ɗaya muyi amfani dasu, so ina fatan idan kuna bibiya zaku fahimci darussan, ina godiya da yadda kuka nuna soyayyarku ga wannan littafi nawa, nagode sosai*_

Youtube channel- KARAMCI TV
Wattpad- SaNaz_deeyah

Facebook- KARAMCI WRITERS ASSOCIATION

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now