Page 6

449 48 2
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like us on facebook https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow me on facebook https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Book2
            '''Page 6'''

Tana buɗe idanunta ta fara kakarin amai, saboda yunwa ce sosai a cikin cikinta.
   Miƙewa tayi zaune, ta ganta anan cikin kitchen ɗin dai.

Tana tashi taga indomie ajje a plate sai tiriri take da gani yanzu aka sauke, ga kuma ƙwai dafaffe guda biyu a kai.

Har duhu-duhu take gani dan yunwa, dan haka da sauri ta ɗauke indomie ɗin ta riƙa loma, ko zafinta ma bata ji saboda yunwa.

Sai ta ta cinye tas, sannan ta buɗe sink ta saka hannu ta wanke tasha ruwa.
   Kallon plate ɗin tayi taga saura ƙwai guda biyu, ita kanta ba wani ƙoshi tayi ba, amma dai ta farfaɗo daga yunwar.

"Bara nayi sauri na dafa wata, kafin na fuskanci matsala" Tana buɗe drawer taga komai wayam.
  "Ko an mayar da kayan store?" Ta furta a fili. Ta san ana ɗebo isassu a ajje a kitchen, kuma basu ƙarewa ake sake ɗebo wasu.

Juyawa tayi da niyyar fita, Islaha ta shigo.
   "Kai kai kai!!!" Ta furta tare da nufar plate ɗin da sauri ta ɗaga.

"Lallai yau za ayi bala'i  a gidan nan"
     "Bala'i ya koma kanki, ai yanzu zan dafa miki wata"
    "Na zo na ganki kin suma baki mana girkin ba, shine na dafa daga inje in zura uniform in fito har kin lashe ta, mayya"
   "Idan ni mayya ce ai da tuni baku raye, wai ke da kike iskancin nan, akwai Amatur'rahman da Salim a tsakaninmu fa, ko kin manta ne?"
    "Idan kin isa Allah ya tsine min, dan kin ga Mommy bata kusa" Ɗaukar ƙwayayen tayi ta jefi Amatul'ahad dasu sannan ta ruga ta fita da gudu.

Dafe kai Amatul'ahad tayi sannan ta ce "Na shiga uku."

Tana nan tsaye a kitchen tana jiran hukuncin da Mommy za ta ɗauka a kanta kawai sai gasu sun taho har da ƙarin Amatur'rahman.

Finciko hannunta Mommy tayi bata direta ko ina ba sai store.

"Dan Allah kiyi haƙuri" Ta faɗa tana kuka.
 
Ai Mommy kwantar da ita tayi, ta ɗaure hannayenta da ƙafafu sannan ɗago buhun fulawa da ƙyar tana nishi ta dire akan cikin Amatul'ahad tare da faɗin "Dan ubanki sai kin amayo indomie da kika ci sannan zan ƙyaleki."

Numfashi kuwa da ƙyar Amatul'ahad ke saukewa, ta fara jin kamar za ta mutu, bakinta gaba ɗaya a buɗe yake.

Islaha kuwa tofe mata guska tayi da yawu tare da faɗin "Mayya"

"Ba Mayya za kice ba, cewa za kiyi ɗiyar karuwa, uwarta ai a kororo aka sameta" Mommy ta faɗa tana juyawa da niyyar fita.

"Mommy duk da dai yarinyar nan ba mutumci ne da ita ba, amma dai kiyi haƙuri ki sauke mata buhun nan kar ta mutu"

"To ta mutu ma mana, ai ni hutu na ne"

"A'a Mommy ko za ta mutu dai kar ki zama sanadi, saboda idan ta mutu dalilinki hukuma ba za ta barki ba"

"Kinyi tunani mai kyau, lallai bamu biya miki kuɗin waec a banza ba"

Murmushi tayi sannan ta ce "Mommy kin manta cewa "Art class nake, kuma kinga ko a jamb ɗina Law na cike, shi nake so na karanta"

"Allah baki sa'a, ai bari ki gama wa'ec ɗin kema dole a fitar dake waje kiyi karatu."

Sauke buhun tayi daga kan Amatul'ahad. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya Amatul'ahad ta sauke sannan ta lumshe ido hawaye na zubo.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now