Page 30(END)

607 54 34
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
'''A True Life Story'''
_Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula tagari]_

Like our page on facebook👉🏻 https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

Follow my group on facebook👇🏻 https://www.facebook.com/groups/961329237791696/?ref=share_group_link

Please SUBSCRIBE our youtube channel 👉🏻https://youtube.com/c/KARAMCITV
Book2

*NOT EDITED*
'''Page 30'''

Da ido ta bishi, dan bama ta fuskanci abinda yake nufi ba.
"Ina ƙaunar Amatul'ahad, kuma na san kece wadda baki taɓa rabuwa da ita ba, duk wuya duk daɗi, idan ina ganinki hakan zai saka naga tamkar ina tare da Amatul'ahad, ina nufin a madadin Amatul'ahad, zan mayar dake makaranta ki cigaba da karatu, sannan za ki cigaba da zaman a gidan nan idan har kin amince"
Hannayenta ta saka ta rufe fuska, wasu zafafan hawaye taji sun kwanta mata.
"Ke nake sauraro?" Ya furta yana kallonta.
"Na yarda, nagode sosai amma ina son zan koma gida na faɗa musu"
"Zuwa gobe ko jibi, ni da kaina zan ɗauke ki na kaiki can dan mu sanar musu, yanzu dai ki zauna anan ki warware kafin muje"
Kai kawai ta gyaɗa tana sauke ajiyar zuciya.

Wayarsa ya ɗauka ya kira Ramlata, tare da faɗa mata ta fito parlour.

Tana fitowa ta samu guri ta zauna tare da faɗin "Gani Yaya"
"Ki kaita ɗakinki, tayi wanka ta ci abinci"
"To shikenan" Ta kalli Zaliha ta ce "Taso muje."
"Ga trolley ɗin ta nan" Ya nuna da hannu.
Ramlat ta ɗauki trolley tayi gaba, Zaliha ta bi ta a baya.

*Few Minutes Later*

"Momma, Daddy dan Allah ina neman alfarku akan wannan yarinyar, ganinta zai saka min ina tunawa da Amatul'ahad."
"To kana nufin kafi so kayi ta tunawa da ita, kana shiga damuwa?" Cewar Daddy.
"Daddy ba ina nufin haka ba, amma ni dai dan Allah ka taimaka, ciyar da ita kawai za kayi, amma ni zan ɗauki nauyin karatunta.
"Wannan Amatul'ahad ɗin da tana raye da taga gata daga Fauwaz, Allah dai ya yi mata rahama"
Ramlat ta amsa da amin.

Sumayya dai tayi shiru, babu abinda take faɗa, sai ƙara jin ɓacin rai take saboda yanda Fauwaz ke fifita mutane sama da ita.

"To batun aurenka fa" Momma ta jefo masa tambayar, sannan ta kalli Daddy ta ce "Ya kamata dai ayi bikin nan, wataƙila ya fi samun kwanciyar hankali"
"Aure kuma? Ni gkiya ba zanyi aure ba, wane jindaɗi ya rage min wanda har zanyi aure Momma? Inyi aure in cigaba da jindaɗi bayan Amatul'ahad ta rasu ba tare da ta samu wani jindaɗi ba."

Duk da kallon mamaki suka bishi dashi, ya cigaba da cewa "Daddy ni gaskiya ba zanyi aure ba, kawai ku barni a haka"
"Ita wadda kake yi dan ita ai bata raye, kuma ko tana da rai tayi maka nisa tunda matar aure ce, ya kamata ka dawo cikin hayyacinka Fauwaz"
Ramlat tayi saurin cewa "Momma dan girman Allah ki daina wannan maganar, saboda..." "Rufamin bakinki, shikenan haka zamuyi ta zuba ido muna kallonshi" Momma ta katseta da wannan maganar cikin ɓacin rai.

"Shikenan sai kawai in sha guba in mutu, sai yafi min sauƙi" Fauwaz ya faɗa tare da miƙewa ya bar gurin.
Da sauri Ramlat ta mara masa baya.
Daddy ya kalli Momma ya ce "Har yanzu Fauwaz bai warware ba"
"Haba Alhaji haka zamu barshi ya gama haukacewa, da ƙyar fa ya warke amma ya ɗauko wani zancen da ban. Kalli Sumayya ita kan ta ramar tsaye take saboda damuwa, ai bashi kaɗai zamu kalla ba, sai mu dubeta itama.

Tsam Sumayya ta ta_hi t bar falon, cike da damuwa.

Yana isa bedroom ɗinsa ya hau saman gado ya kwanta. Ramlat da ɗsn saurinta ta schigo gudun kar wani abu ya sameshi.
"Kayi haƙuri Yaya" Shine abinda ta furta tana daga tsaye.
Ɗagowa ya yi ya kalleta sannan ya ce "Ramlat ɗauko min magani kaina kamar zai tsage"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta gami da nufar side drawer ta buɗe ta binciko maganin.

Du hast das Ende der veröffentlichten Teile erreicht.

⏰ Letzte Aktualisierung: Mar 15, 2022 ⏰

Füge diese Geschichte zu deiner Bibliothek hinzu, um über neue Kapitel informiert zu werden!

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt