Shafi na 3-4

787 51 8
                                    

[9/3, 8:34 PM] SaNaz_deeyah👄: *ZAFIN HAWAYENA*
    '''A True Life Story'''
    _Written by SaNaz deeyah_👄

*K.W.A📚*

Book 1
'''Shafi na uku'''

Sai da suka shigo cikin asibitin sannan Sani ya kirata.
  "Ban gama ba shiyasa ban kiraka ba" Shine abinda ta faɗa lokacin da ta ɗaga wayar.
   "Eh dama tare muke da Zaliha mun kawo miki abinci ne"
   "Okay! To kuce a nuna muku Emergency cikin Amenity nake, room number 8"
"To gamu nan ƙarasowa" "To" ta furta sannan ta katse wayar.

                   *****
Suna zaune su huɗu akan ƙayataccen dinning area nasu, ƴar ƙwarya-ƙwaryar party Alhaji Ahmad ya haɗa na dawowar Fauwaz.

Suna zaune su huɗu a dinning area ɗin, Alhaji Ahmad, Hajiya Huwaila, Fauwaz da Ramlat.
    Sun gama cin abinci amma kuma anan suke zaune suna ta hira.

Alhaji Ahmad ya kalli Fauwaz cikin kulawa ya ce "To tunda ka dawo aiki anan gida Nigeria, sai kuma a samu ayi aure, zaman tuzurancin ya isa haka."
   Murmushi yayi sannan ya ce "Daddy ai dama ni kam na dawo ne da niyyar inyi aurena, domin na san wadda nake da burin aura yanzu ta kammala karatunta, tana da son karatu shiyasa na jira har ta gama."
    "Kaji Yaya da ƙarfin hali, amma ni kam baka taɓa faɗa min kana da wata wadda kake so ba, ni nayi tunanin ma Aunty Sumayya ce"
  "Sumayya kuma?"
  "Eh dan koni nayi tunanin Sumayya ce, domin kuwa yadda naga kun shaƙu."
    "Mommy Sumayya ai matar manya ce, ni Sumayya kawai na ɗauketa a matsayin ƴar uwa da muke jini ɗaya, tunda da sunan Daddy take amfani, so kunga kuwa wa ai ba zai auri ƙanwa ba"
       Murmushi Daddy yayi yadda yaji Fauwaz na zaro zance.
  "Yanzu dai ya kamata koma wacece, ace zuwa yanzu mun santa, mun kuma samu iyayenta an gama magana."
   "Daddy zan kira Zayyan, ko zuwa gobe ya rakani gidansu yarinyar, daga nan kuma sai in sanar da ita cewar zaku turo, tunda ta gama service yanzu."
    Jin an ambaci Zayyan ya saka Ramlat saurin miƙewa, rai a ɓace ta bar gurin da sauri.
   Kallon Mommy Fauwaz yayi, tare da faɗin "Mommy meke faruwa? Ko dai sun yi faɗa da Zayyan?"
     Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "To ka sameta sai ta faɗa maka komai, shi Zayyan ɗin ba ku waya dashi ne?"
      "Munayi amma bai taɓa faɗa min cewar sun samu saɓani da Ramlat ba."
     Shiru Momma tayi bata sake cewa komai ba, ya kalli Daddy yaga yana danna waya, da alama yayi haka ne dan gudun kar Fauwaz ya tambayeshi.

Miƙewa yayi da sauri ya nufi bedroom ɗin Ramlat.
   Yana tura ƙofar ya ganta kwance a tsakiyar makeken gadonta, ta rungume ƙatuwar teddy tana hawaye.
      
Gefen gadon ya zauna ya ƙura mata ido, ita kuma ta tashi zaune da handky a hannunta tana goge hawayen.
     "Ramlat meke faruwa ne?"
Kallonshi tayi, idanunta har sun fara yin ja, kan hancinta kuwa jajir  kasancewarta fara sol.
   Murya a sanyaye ta ce "Kana nufin shi bai faɗa maka komai ba?"
   Girgiza kai Fauwaz yayi ya ce "Wallahi babu abinda ya faɗa min, kuma muna waya dashi sosai fa, dan ko dana sauka ma munyi waya."
      "Amma kuma duk zuwan da kake Nigeria ai tare dashi ake zama anan ya kai dare, bakayi tunanin abinda ya hanashi zuwa yau ba?"
    "Ya ce aiki yayi masa yawa, so sai nace babu komai nayi masa uzuri, idan ya gama aikin yazo"
       "Hmmm ba zai zo ba, ai rabon da Zayyan ya saka ƙafa a gidan nan, tunda yayi aure"
     "Aure?" Fauwaz ya maimaita cike da mamaki.
     "Kana nufin bai faɗa maka ba kaima?"
     Girgiza kai yayi, sannan ya ce "Bai faɗa min yayi aure ba, amma yaushe akayi auren Zayyan? Domin ni dai a iya sanina Zayyan ba ko wace macece ke burgeshi ba, dan ko da yace yana son ki, nayi mamaki sosai, kuma bayan ke baya da wata wadda yake so, baya daga cikin maza masu kule-kulen mata, tabbas akwai wani abu a ƙasa"
      "Yaya kada ka zartar da hukunci akan abinda baka sani ba, Zayyan yaci amanata, Yaya kawai sai ji mukayi yayi aure fa"
     "Ramlat dole akwai dalili, Zayyan ba zai taɓa yin haka ba"
     "Amma meyasa bai zo ya wanke kanshi ba, nayi ta kiranshi baya ɗagawa, nayi jinya tsawon sati, na fita hayyacina, kaɗan ya hana hawan jini kamani, sai dana bawa zuciyata haƙuri, a ƙarshe kawai na goge duk wani abu da zai tuna min dashi, shiyasa ko maganarsa bana son ayi a gabana."
     "Zayyan yayi aure? Kuma bai sanar dani ba."
     "Ina tunanin yanzu sati na uku da yin bikin"
      "Zamu haɗu, zai faɗa min dalilinsa na yin hakan"
      "Yaudara da cin amana mana, Yaya ba fa halinku ɗaya da Zayyan ba, shi Zayyan m......."
    "Ka da ki faɗi mummunar kalma a kanshi, ki bari na fara jin ta bakinsa" Ya tari numfashinta da faɗin haka.
     Bata ƙara cewa komai ba, shi kuma ya tashi ya fita ya bar ɗakin.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now