Shafi na 18

499 48 9
                                    

*ZAFIN HAWAYENA*
  '''A True Life Story'''
    _Wattpad@SaNaz_deeyah_

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
  _[Karamci tushen mu'amula tagari]_

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsap

*_Zanyi amfani da wannan dama wajen bawa ɗumbin masoyana haƙuri, a bisa jinkirin posting da aka samu, nayi ƙoƙarin ganin cewar ko wace rana na saki page ɗaya, sai dai kash! Allah bai nufa ba, a ƴan kwanakin nan bana samun lokacin da zan buɗe data inyi chat ma, bare typing, naga saƙonninku da dama, wanda wasu har yanzu ban samu damar amsawa ba, ina son kuyi min afuwa, nagode matuƙa da nuna kulawarku a gareni, Allah yasa ba iya ZAFIN HAWAYENA kuke nuna kulawarku ba, har da SaNaz deeyah, ta yadda ko da na ajje alƙalamina ba zaku manta dani ba._*
  #InaTareDaku

Book1
            '''Shafi na sha-takwas'''

*Waiwaye*
*New York*

Amatul-ahad zaune akan ɗaya daga cikin kujerun dake parlour'n Fauwaz. Yayinda shi kuma yake zaune kan kujerar dake facing ɗin tata, hannunsa riƙe da waya yana latsawa, ita kuma ta kafeshi da idanunta.
      "Tsawon wata biyu da haɗuwarmu, amma har yanzu ban daina samun barazana daga tsohuwar budurwarka ba."
   Ɗago ido yayi ya kalleta, tare da mayar mata da amsa "Manal ba budurwata bace, ban taɓa furta mata kalmar so ba"
    "Amma ita tana sonka, ka san da haka?"
   "Ƙwarai kuwa, amma ni kuma batayi min ba"
   "Kamar yadda ban maka ba ko?"
   Murmushi yayi, sannan ya cigaba da cewa.    "Amatul-ahad kina matakin farko a karatun Degree, kafin maganar soyayya, ya kamata  ki nutsu ki zurfafa a cikin karatun"
     "Shikenan Bloody, ni dama na san ban kai matsayin da zaka ce kana sona ba, kamar dai yadda Manal tayi failing haka nima."
   Shiru yayi bai ce komai ba, ta cigaba da cewa "To yanzu dai faɗa min, wacece kake so kuma a ina take? Ko dan na san ma kamar kai ba zaka rasa ƴammata da yawa ba" Ta faɗa tana murmushi. "Amatul-ahad ba kince min kina da assignment ba, ya kamata kije kiyi"
      "Ni ba zan tafi ba sai ka faɗa min kana so, wai har in cire kunya a matsayina na mace, amma kuma ba zaka ko tausayawa zuciyata ba"
    "Ina sonki..." Murmushi tayi wanda har ya bayyanar da kyawawan haƙoranta.
   "Amma a matsayin ƴar uwa, ƙanwata, wadda nake ganinta a matsayin blood sister, kamar dai yadda take kirana da Bloody" Ai tun kafin ya ƙarasa faɗa ta ƙimtse murmushinta.
   Yana gama maganar ta miƙe tare da faɗin "Na tafi." Ko amsarshi bata saurara ba tayi gaba, dama ya san hakan ce zata faru, da murmushi kawai ya bita, a ranshi ya furta _Ina matuƙar ƙaunarki sosai Amatul-ahad,  amma bana so soyayya ta shagaltar dake, zan bari har ki gama karatu sannan na kai ƙoƙon barata gareki, har gidanku, kuma in fara tambayar izni daga mahaifinki._ Ya kwantar da kanshi a kujerar, ya buɗe hotunan Amatul Ahad yana sake kalla.

Haka dai rayuwarsu ta cigaba da tafiya, yana kula da ita sosai, ya zame mata tamkar wata fitila, domin duk duhun da ta shiga shine ke haskata, kusan kullum maganar soyayya sai ta masa, amma sai ya waske da canza magana.

  A haka har tayi shekara guda da fara karatun Degree, mahaifinta kuwa ya san Fauwaz, domin bata da wani abu sai ambaton sunansa.
  Suna samun hutun session kuwa ta tafi Nigeria, tayi roƙonsa yazo su tafi, amma ya ce shi kam aiki yayi masa yawa ba zai iya komawa ba.

Haka ta tafi cike da kewarsa. Kamar kuwa yadda tayi tsammani, jirginsu na sauka a Nigeria tana fitowa taga Daddynta na jira, da ɗan gudunta taje tayi hugging ɗinsa.
  Yayi murnar ganinta sosai haka ya ɗauketa sukayi gida, step mom ɗinta da step sisters kuwa ba yabo babu fallasa haka suka mata barka da dawowa.

Bayan tayi wanka ta shirya, Daddy ya ɗauketa zuwa restaurant, anan akayi mata ordering na different food, drinks & snacks, taci ta ƙoshi, sannan suka wuce park, anan tayi nishaɗinta kafin su dawo gida.

*Cigaban Labari*

Zaliha dai da ido kawai take bin su, musamman shi da yake ta kallon Amatul-ahad, kamar shine karonsa na farko daya fara ganinta.
    "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya faɗa gami da dafe goshi.
    "Ka ga yadda rayuwata ta koma ko?" Amatul-ahad ta furta, har a lokacin idanunta a rufe suke.
   "Kiyi haƙuri Amatul-ahad na san laifina ne, na kasa yafewa kaina a bisa zaluntarki da nayi"
  Ajiyar zuciya kawai tayi, bata sake cewa komai ba.
  Sallama yayiwa Zaliha, sannan ya fita ya bar asibitin.

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now