BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 8
At d core of my pain.Old maguzawa site:Anguwar bayan gari, kano state.
Kwance take akan tabarma bayanta jingine da Wani motsatssen matashin kai tana maida numfashinta a hankli,daidaikun matar makwabta ne a zagaye da ita ana famar jajantawa ana bata baki,Matar mai anguwar ne ta kara maimaita maganarta tana cewa"Lallai Sannu hadieza,Allah ya kara sauki, Allah yasa ciwon nakin nan kaffara ne.
Da kyar Umman take dago kanta inta dan Kare musu kallo sai tace Ameen sai ta kara maida kallon ta gefe batare da ta kara furta musu uffan ba
Daga ganinta kaga yanayin wacce kwata kwata batajin dadi aranta
,musammn ma yanayin taruwar matan nan agabanta,ita kanta tasan ba Wani abu bane yake kawo matan makwabta gidanta face gulma da son jin kwakwaf kowa dai nason yaji asalin labari game da Auren bazata da akayi ma yarta rufaida..Duk Dama tasan tunanin rufaidar shine silar ragwabewar jikin ta amma tana matukar tsoron wanda zata sake ta tattauna damuwarta da shi
Ayanzu Bata da kowa na kusa da ita Dan haka ta qwammaci ta cigaba da danne abubuwan dake damunta masu Nauyi da kuntatawa acikin xuciya.mijinta Yaa malam ya riga yahana yayansa Koda yin waya da ita inba Wani abu muhimmi bane ya taso musu,ko da ya tason ma yafison su kirashi direct amma ba ita ba,Dalilin sa na cewa ai ana zugasu ne Dan su bar gidan mazajensu suki zaman aure.
Tun da ya rabata da su rufaida take cikin tsananin bakin ciki da damuwa and She have no one to talk to Bare ma ta amayar da kuncin ta waje Kodama zataji dan sauki sauki a zuciyartan dake mata nauyi.
Ta gama lura cewa wayannan mutanen anguwar nasu kusan Duk jirgi daya ya debosu acikin su babu mai isashen karatun arabi bare na boko,su basu San komi ba sai azaban saka Ido da bibiyar rayuwar mutum in tayi tsami suyi ta tsegumi ana dariya intayi kyau sununa tsantsar bakin ciki da hassadarsu a fili.
Hasalima badon an shede rufaidar da tsananin kamun kaiba da tuni an karade gari da cewa cikin SHEGE tayi ko ko ace an kamata tana zina shiyasa akayi mata aure irin wannan babu hidima babu shela kawai agaggauce batare da sanin uban kowa ba.
As usual Tunda suka shigo gidan babu abunda sukeyi sai raha a tsakanin su da kwakwale kwakwalen magana
Kowa dai burin sa baifi ya fadi wata kalman da zaisa hadieza ta harxuka ta shiga bude musu duka sirrikanta ba,burinsu ne su baje kunnuwan su kwasa sirrinta cikin satin nan sai asamu abun bazawa,Ita kuwa hdiza Sam taki kulasu,Koda ma an tambaye ta silar ciwontan saidai tace ciwon zuciyarta ne ya motsa kuma ma yanzu tanajin saukin shi,su Sam ba Hakan suke gani atttre da ita ba,Dan shi magulmacin mutum kusan yafi
Kowani mahalukin Dan adam iya lura da yanayin mutumaganin su tabbas akwai abunda yake tafiya game da Auren rufaida wanda su basu gane ba,kuma koma menene sun san tabbas babu dadinji Dan sun dade basuga hadiza acikin yanayin tashin hanklin irin wanda take ciki yanzu ba
Ana cikin wannan yanayi saiga sallama a kofar gidan sun,bayan kamar minti uku da ansa sallamar can saiga almajiri ya shigo Niki Niki da kayan makulashe ya shigo da su ayar babban leda,wata kyakkwar mata ce ke biye dashi fuskarta babu yabo babu fallasa,tun daga kasar zaninta har tsakar ka suke kallon ta babu kiftawa,"..sallama alaikum..umma hadieza tana ciki kuwa?,Duk yawansun Nan ba a samu wacce ta iya amsawa ba sanda umman ta mike da kyar ta amsa maganan fuskarta dauke da murmushin jin muryan Barister fareesa matazu a tsakar gidan
Lale marhaba fareesatu ce? Ahh sannu da zuwa...
Shigo mana,Umma ta fadi hakan ayayin data Dan mike zaune fuskarta dauke da murmushi"Ina wunin ku?
Barister fareesa ta Dan rusuna kai ta gaishe su duka,sai ayanzu suka farga daga azaban kallon tan da sukeyi,.atare duka suka ce uhmmmm Lapya barkanki da shigowa,tace yawwa,Daf tana shirin zama kusa da umman knan sautin wani magana ya dakatar da ita, wata magulmaciyar ce data kasa hakura azauna,tace hadiza
Wannan kuma fa?

YOU ARE READING
SHADE OF RUFAIDAH
Spiritual"Na rasa ni wata irin baqar mujiyace,Duk wanda yake tare Dani saiyayi Gamo da baqinciki acikin zuciyarsa. Na rasa ni wata irin mace ce da bani da albarka Sam Sam saidai ayita kuka Dani".. "life is full of negative and positive numbers but Not once h...