chapter 46

646 84 1
                                    


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 46

Wajajen shida saura na yamma zarah ta farka a wahalallen baccin dayayi awon gaba da ita jitayi duk jikinta baya mata dadi,ga wani irin axaban tsamin da gabobin jikintan ta suke mata ta ciki ciki tanajin wani irin gajiya har cikin kasusuwan bayanta da cinyoyinta, bata iya yin komi ba wankan kawai ta sake fadawa ta dade a bathrum tana gasa jikinta cikin ruwan zafi wanda hatta wata nai jegon ma bata samu irinshi ajikinta ba..

rurin wayarta dayaki ci yaki karewa daga daki shi ya dameta wanda yasata fitowar dole daga bathrum din daure da karamin towel a kirjinta,gaban mirror tawuce direct ta dau wayar tahau dubawa as expected miscal din master kawai tacikaro dashi kwafa tayi dan tasan bazai wuce akan maganan su ba kiransa itama tahau yi ba a daga ba saita hakura.

Wani tafkeken ajiyar xuciya ne ya kwace mata cikin sanyin jiki batako yi yunkurin nemo man shafawar bama ta nemi waje agefen gado ta zauna ta kuma rabza uban tagumi acikin tsananin nisan tunani ta jefa kanta wani ajiyan zuciyar ta sauke sannan hummmmm kanaji kasan tayi nitso mai zurfi haka kawai ta soma sumbatu ita kadai tana cewa"Shegiya duniya, garin nemanki dole ne asha baqar azaba,Yo Mezai hanna in akasameki ayi yadda akaga dama dake..?gani take in Allah ya bata duniya kamar irin na Ainau toh wallhy sai dai ayi kallo dan ita kanta batasan kalar tsiya da tijarar da zata shinfida a doron qasa ba.

bataba kanta ansar tambyar ba ta miqe tsaye,kan screen din wayarta ta kalla a hnkli,snn taja wani kasalliyar tsaki wai mutumin da kake hauka akansa kenan shiru bai nemeka Ba?tsaki ta kumaja tuna yau ko nemanta ma imad baiyi ba bayn ko jiya cikin dare ma saida ta kirashi amma ya kashe mata waya.

Maida wayar gefe tayi kamar zata ajiye sai caraf ta kuma daukar waya tayi scrolling cikin contact cikin sauri har tazo dede kan number imad datayi serving da LOML. dialing ta shigayi kamar zaiyi ringing sai kuma ta katse cikin sauri ta aje wayar acan gefe,
Ajiyar zuciya ta sauke cikin tunani tace wakanta yau bazata ma fita ba dan bataso taje ta same imad adaidai lokacin da master zai iya kiranta agabansa cos she dont eva want to look suspicious gaban sa.

Bayan nan ta miqe tsaye ta isa gaban madubi mai kawai tashafa ta dan kikmtsa kanta xuwa shigar bacci dama can bata damu dayin wani ibada ba  bokayen zee da suke bi kaf sun hanata yin sallah da azumi.

An riga an dasa mata aranta cewa yin ibada shi yake kara mata baqin jini da rashin sa'a a rayuwa kuma ta amince da hakan kwarai da gaske dan haka tana kammala  kwaliyyarta tayi keys ma kofar dakinta batayi wata wata ba ta fada kan gadonta ta kwanta tayi lumui da wayarta a hannu dantasan dole ne master ya kira

Sai can around 12 kirar master ya shigo ta farka a gigice sukahau durama juna ashar
nan take tagaya masa cewa ita sai gobe zata iya zuwan masa,tamasa alkwari da sassafe
Abu daya yafada yasata yin murna sosai, da yace ya riga ya kada zee a abuja harta kwashe kayanta kaf ta koma Kano jiya cikin dare.
Tun da suka katse wayar take cikin jin dadi tabbas tasan yau da master bai bata hadin kai ba toh wallhy da tuni kashinsu ya bushe ba ita kadai ba harda Ainau dan babu abunda zai hana zee tayi watsi da sirrukansu waje,dan abu mai mugun saukine awajen xee musammn in ta debo kwaya har gidan nan zata iya zuwa ta tona musu asirinsu tas tass.

Yau Wani irin shiru gidan ya dauka da alamun kowa nata can sashen sa dan bakajin motsin kowa a sararin gidan kafafu ma duk sun dauke

Yau kwata kwata imad bai dawo gidan ba yana kammala tsabgar gabansa ya wuce wajen yaa sheik a cikin federal court Abuja

yawancin ayyukan  documentation dinsa ne da sukaso su sha musu kai yasa basu samu sun kammala komi akan lokaci ba

mufrad ne kawai acikin gidan amma bazaka taba sanin hakan ba dan tun shigowar sa ya nufi dakinsa ya zauna akan couch dinsa yahau yar danne dannen sa a laptop as usual feeling so helpless and lonely sabida wani irin mugun shiru da koina ya dauka

SHADE OF RUFAIDAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora