chapter 20

1K 227 148
                                        

IN BAKU GANNI BA NETWORK NE COS IM NOT IN TOWN PRESENTLY.

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 20
Fear...


By 7.30am imad ya dawo cikin asibitin hannun sa dauke da ledojin abincin daya siyo yana famar tafiyar sa cikin sauri batare daya kula kowa ba ya wuce direct har cikin dakin datake kwancen samu yay bakowa anan face rufaidan datake kwance ita kadai akan gadonta yau ko respirator ma ba asakaya mata ba da kallo daya yabi lumsashen idanun ta wanda suka bada alamar cewa yanzun Nan aka kullesu,ajiye ledar abincin Yayi  a saman table sannan ya karaso har Gaban ta ya tsaya Daga gefe haka yana ta kallon rufaffen Idanuntan dayake famar shaking Duk ta kasa aje hanklinta waje daya,ko Wani motsin kirki bata son taga tayi hatta numfashinta ma da kyar tabarshi yake fitowa,Wani irin nauyin sa ta soma ji aranta Sanin cewa bata taba sanin sa  arayuwarta ba she is a bit confused about him, kunyarsa da tsoron halin datake ciki shiyake bala'in son ya rikita mata hankli da tunaninta ayanzu

Suna Cikin haka wayarsa yay kara Babu jira ya dauka ya sa akunnen sa ya fara magana, jin ya amsa kamar wasu ne zasu taho yasata Kara Lumshe idonta Dan haka kawai taji aranta kamar bata son hakan ya afku,she wish dat shikadai ne zaina kulawa da Ita basai wasu sunzo ba Duk tunanin ta ko wayanncen polisawan ne zasu Kara dawowa su isheta da tambaya gashi ko kadan bata son jin Sunan Alaji Bature a kusa da ita bare ma aje ga jefa ta cikin halin tuno da kanta acikin mummunar rayuwar datayi a kwanakin Nan.

Sosai take kokarin binne damuwarta
Aranta,tadai San bata cikin hayyacinta Sosai Amma Duk da Haka saida ta kasa ta tsare wajen hana kwakwalnta tuno mata da komi
Gani take kamar inta kuskura ta tuno Alaji Bature to Babu shakka zata farka agaban sa ace mata gamowarta da su imad mafarki ne.

Itadai Bata San meya afku ba bata San ya akayi taxo nan ba Amma tabbas jikin ta na bata cewa tsira tayi,Wani lumshe idanunta tayi cikin gode ma Allah daya kawo ta cikin wannan yanayin da bata taba tsammanin zata ci Karo da shi ba har abada,bata hankara ba taji kamar ana kokrin dagota,cikin  sauri ta bude idanunta wanda suke da haske,Nan take suka hade ido dashi,saurin sauke nata idanun kasa tayi ganin murmushi mai mugun sanyi  a fuskar sa,sirraran yatsun hannun ta ya riko cikin tsareta da sautin muryan sa mai taushi yace "hey..I'm back"..a hnkli ta dan dago kadan ta kalle sa,Kara hade ido sukayi saiya Kara yi mata murmushi yace "bari na shirya miki abincinkin ki ko sweetie?tun bata amsa shi ya juya ya shiga bubbude ledojin daya shigo dasu,nan ya hau ciro abincin komi ya shirya mata su in a clean disposable plates,wanda yasan daga taci zaa iya yarwa hardashi,
awaje daya ya saka mata duka abincin sabida ya fahimce cewa ba lallai ne ta fahimce abunda tafi sha'awar ci ayanzu ba,Dan haka ya debo shinkafar kadan ya xuba ya jejjera ganyen ya Dora chicken wings akai yabi ya zagaye jikinsu da namomin cikin pepper soup din komi daidai misali

Spoon ya Dora akai lokacin harta miqe zaune bayanta jingine da pillow Dan har cikin ranta take balain mararin qamshin abincin daya cikke iskar dakin da Wani nauin qamshn Dadi,a lokcin Idanun ta a lumshe suke Dan bata ma San harya kammala zuba mata abincin ba.

Tahowa yay da abincin har Gaban ta sannan ya zauna,ganin batayi motsi ba yasa shi yin gyaran murya atake ta bude idanun ta ta kalle sa tagan sa yana Murmushi,yace ur food is here,Tashi ki taba kiji..Wani kallo tamai sannan ta sauke idanunta kasa kan abincin ta kalla,ganin namomi ne kaca kaca asaman abincin yasa ta kulle Idanunta agaggauce,Wani zuttttttt Idanunta sukeyi, kanta ya shiga bugawa atake atake,Nan da nan kirjinta shima ya amsa da Wani irin bugu mai tsananin karfi, hotunan naman mutum dataci ranar shine ya soma bijiro mata a cikin kwayar idanuntan,tuni kwakwalta ya shiga maimaita mata Duk abunda ya afku da Ita,hatta ihu da Marin da Alaji Bature ya rinka falla mata a lokacin sanda ya shiga dawowa mata sabo
Wani buff buff kirjinta yake bada sauti,ta shiga tuna yadda ta rinka kwaxa amai tana kwakwale cikin ta tana kuka,gaba daya ta rikice agaban imad akabar sa da binta da kallo cikin tsantsar mamakin yadda ta rikice ta birkiice a lokaci guda,daf yana shirin daga abincin zai aje shi gefe rufaida ta razana ta daka Wani uban tsalle ta bangaje plates din komi ta tarwatse

SHADE OF RUFAIDAHOù les histoires vivent. Découvrez maintenant