BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 12
A Moment in hell._Ivy cottage U.S.A_
_Morning 10:30am_Cikin mugun firgici rufaida ta farka jin ta kafe waje guda ko musulmin motsi ta kasayi,Wani dishi dishi take gani a idanunta ayayin da kanta yake juyawa cikin Wani matsanancin zafi da ciwo ga uwa uba yunwa daya gama nakasata,ganin Inda taken wanda baiyi kama da Inda aka ajiyeta daxu ba yasa ta tashi zaune a firgice tana kallon wajen,tamkar bayan gida hake yake babu gado babu kujeru sannan da katako kawai aka zagayeshi,dafe bangon katakon take Koda zata iya lekawa ta waje
Ɗigowar wani abu a saman goshinta kamar ruwa yasa taɗanyi ƙarfin halin aza dan'yatsan'ta guda asaman goshin ta dan lakato abun Sai cin karo tayi da wani irin jiniii da sauri ta ja da baya inda santalelen hannun mutum ya sulalo kasa ya fado ajikinta,Wani irin kara ne ya sufce mata cikin tsananin razana duban gefe da zatayi kenan taga fatima kwance nashe-nashe a cikin jini,babu kafa da hannayenta,an jingene ta a saman katakon har an mata yankan rago
Yankar jiki tayi ta fado kasa Cikin matsanancin tashin hankali ta buga wata irin kafurar kara mai hade da ihu nan take ta zame ta tafadi kasa kwance sumammiya..
Minti biyar mai kyau batayi ba taji ana janta waje da qarfi acikin sauri,da kyar ma ta iya finciko kanta daga suman ta bude idanununta Jin maganganun su takeyi a sama sama da yadda suke ta kwashewa da mahaukciyar dariya suna famar bidiri
Alhaj baturen ne agaba yana Jan rufaidar da kansa yana fadawa thugs dinsa yadda ya kashe Fatima sabida taci amanar sa,bakin sa harna Tara yawun Kwadayi yace yau miyan taushe za'ayi masa da naman cinyoynta Wani irin sheke dariyar su kawai sukeyi tamkar ba mutane ba.Dayan yace boss
Meyasa ba a cire kanta ba?
Ko anfasa dantsawa ne..
Yace a'a,tare da sake wata muguwar Murmushi ya juyo yana kallon rufaida "tukuna,Muje backyard zakuga yadda za'ayi da shi we need to teach her some lesson
Wani Ihu suka kaure dashi Suna ce mai sai oga,by then rfaida ta dawo cikin hanklinta sosai Dan dariya da ihun nasu ma kawai ya isa ya jefa ka cikin Wani mummunan haliHar gaban Wani old dumb dake bayan gidan suka jata isar su keda wuya ya jefata kasa yabi ya kwaso ta ya damke Gashin kanta tana layi ya gurfanar da Ita a rusune.
Hawaye ne kawai suke saukowa daga cikin idanunta dan hatta karfin yin Ihu ko magana ta kasa samun shi atattare da ita,addua kawai take Allah yay gaggawan daukar ranta in Hakan shiyafi mata alheri.
Dan kuwa tabbas ta cire rai ga rayuwa.Wasu manya manyan fatanyoyi da axes taga katten mazajen sun dauko
Kirjinta kamar zai tarwatse da matsanancin tsoro ta gama bari cewa lokacin ta me itama yaxo Hala tunda ya kashe Fatima itama Hakan za'ayi mata Wani kukan ta kara barkewa dashi tana jujjuya kayinta cikin baqar dimauta mai nuna tsantsar rikicewar yanayin da zuciyarta ke cikiBanda Allah babu abunda zuciyarta yake kira,gaba daya tarasa Inda zata aje kanta Wani irin matsanacin rawa jikinta yakeyi,kawai tana gurfane ne Amma ita kanta bata San Wani kalar nau'in gushewa hankalinta yayi ba..
Wani irin gaafffff aka sauke dukan guduma agabanta sanda ta razana tayi tumbul taja da baya,kara fincikota yayi ya tursasa agaba tana kallon abunda sukeyi da alama Rami suke hakawa agabanta
Dan karamin ditch haka wanda tabbas kasan binne abu za'ayi,saide bata San me za'a binne ba shin sauran dead body fatima ne ko ita?cikin wannan tunanin ta kara zautar da kanta..Da Dan fadi suka haka ramin dake basuyi shi yy zurfi sosai ba,Suna kammalawa aljai bature ya juyo ya kalleta yace
"Ki kalla Wannan shine makomar wanda yaci amana ta" Kaiwa nan ya juya yana mai nuni da gangar jikin fatima..Kinsan wannan matar?
Rufaida dake cikin tsananin dimauta gyada kanta kawai tayi Dan bazata iyama Furta kalma ko daya ba,"..Wani dariya ya fashe da shi,"..yace..tun tana yar shekara 5 na samo ta,iyayenta ne suka ban ita da hannun su a kyauta Dan inbasu kudi nikuma nayi mata adalci namaidata yata shine ita kuma yau zata saka min da cin amana.
ESTÁS LEYENDO
SHADE OF RUFAIDAH
Espiritual"Na rasa ni wata irin baqar mujiyace,Duk wanda yake tare Dani saiyayi Gamo da baqinciki acikin zuciyarsa. Na rasa ni wata irin mace ce da bani da albarka Sam Sam saidai ayita kuka Dani".. "life is full of negative and positive numbers but Not once h...