chapter 31

803 141 13
                                        


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 31

Ba zallan jiki ba hatta muryan yakumbo rawa ykeyi ayayinda ta karaso kusa da ita cikin sauri ta rirriike ta "rifaida Ashe kina Nan aketa magana banji duriyarki ba?dudduba fuskarta ta shigayi a hnkli tace na shigga uku ni A'i Yaya naganki haka?kukan me kikeyi rifaida Wani abu sukayi miki?kifadin waye acikinsu ya zageki yanzun Nan inbi sawunsu in sauke musu buhun rashin mutunci..

Wani matsanancin kukane ya kufce wa rufaida Wanda shi yasa yakumbo Jin nakaso itama sai tabita ta barke da Wani uban kuka kukan kawai sukeyi atare Babu mai kakkautawa da kyar rufaida ta kufce a hannun yakumbo tayi gefe durkushe akan gwiwanta cikin sautin wahalallen kukan dake fitowa da hucin nakasashen numfashi Wanda  take kwaceshi da kyar,cikin wannan yanayi tace
,"..Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun yakumbo nashiga uku,rayuwata ya lalace..yakumbo ya zanyi da rayuwata?
Da sauri yakumbo ta rusuna agabanta tare da dagota daga durgushen ta take Nan take ta manne ta da jikinta ta rungumeta sosai tana shafa mata Kai da jiki.."Yi hakuri rifaidata,Ki saka ma zuciyarki dangana ki yayyafawa ranki ruwan sanyi,kuka ba naki bane rifaida adduan dai shi ya kamata muyi Allah ya fiddake daga cikin wannan lamarin lpya,kul Kar ki bari maganganun su ya dameki,kowa yasansu sune manyan algungumai magulmata a anguwan nan Kar halinsu ya dameki,kaf dinsun Nan basu da alqibla arayuwarsu basuma San abunda yake musu ciwo ba,Dan kuwa da sun sani da kodan albarkacin y'ay'a matan da suka haifa acikinsu ai bazasu aibata naki qaddarar ba..

Kiyi shiru abunki rifaida ki daure ki kwantar da hanklinki,namaki alkwari Dani da Hadiza muna Nan daram tare dake bazamu taba kyale wasu makirai Wanda basusan Kan magana ba suzo suna cuna ma rayuwarki tashin hankli,Sam Sam bazamu yarda ba, damuwa banaki bane,samun saukin ki shine a gaban mu kinji auntagale? Kuka kawai rufaida take tamkar wanda bajin maganan yakumbon takeyi ba Dan ita kadai tasan iya abunda takeji acikin ranta da xuciyarta,already abubuwa dayawa sun riga sun toshe mata kwakwalwa da numfashi suna famar nakasata mata gabobin jiki

Acikin xancen su maman Iman in akwai abunda yafi damunta baifi cewa da sukayi ummanta tayi fada da yaa malam ba,gaba daya sai taji hakan ya daga mata hnklinta sosai Dan kuwa tasan wacece ummanta,Abunda kuma zaisa ta daga hanklinta har tayi fada toh lallai babban al'amari ne bana wasa ba..

Maganan zuci kawai take cikin juya tunaninta akan mekenann yake afkuwa a gida Babu abunda bata shiga kullasa acikin ranta na bakin ciki da damuwa ba..

Banda lallashin ta da kalamai Masu sanyi da karya xuciya Babu abunda yakumbo takeyi har yakumbo ta gaji ta janyeta suka koma ciki bata wani kula ta dawo hayyacinta ba ba tsaban damuwa da jimamin kuka daya Gama rudata ya toshe mata madigar yin tunani

Suna barin tsakar gidan saiga bullowar rahamatu yar gidan malam dalhatu mai shayi Wanda tuntuni take labe ajikin dangar waje tayi luumui acikin duhu tanajin Duk Wani abun da akeyi ata ciki kuma komai da aka zantar anan din a kunnenta ya kare Danta riga da Tasha alwashin saita tonawa Umma hadiza da yayanta asiri..

A rakube ta zame ta falfala da uban gudu cikin sanda ta nufi cikin anguwar  agaggauce

Tafiya take sauri sauri Kuma a karkace,wanda tsabar saurin datake yi daganan zaka iya jiyo sautin bugun zuciyarta gaban ta kawai take kallo damuwarta baifi taje ta fetsa gurmin data debo yanzu ba,aikuwa kamar wacce zata kife taci da kasa haka tayita jefa kafafunta galau galau akan hanya bata tsaya ko ina ba sai a dakin matar mai anguwa rike da cikinta tana yar haki
Assalamu Alaaikum
Sallama alaikum

Dake ma dare ne dakyar ma matar mai anguwa ta fito
Sannan ta kulata .
A tsattsaye ma ta tsaya daga bakin kofar fuskarta a matukar daure murya ciki ciki tace rahamatu lpya naganki a wannan Lokacin,Ina ita talatun? fatan dai bawani gurmi kukaje kuka hada ya afka daku ba?

SHADE OF RUFAIDAHWhere stories live. Discover now