chapter 22

886 208 108
                                        

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 22
Back to Nigeria

8pm daidai jirgin su ya sauka a aiport din aminu kano within 40 mins aka gama clearing dinsu suka dau hanyar fitowa waje su ukun atare,kafin Nan already driver yazo da wata mahaukaciyar land cruiser jeep tana Parke tana jiran su
Suna isowa driver ya bude musu kofa dan su shisshiga
Rufaida ce abaya tare da kawun ta yaa sheik,wanda tun shigarsu banda nasiha da wa'azi masu shiga jiki babu abunda yake mata,ahnkli yake bi da ita yana aikin lallabarta cikin son ya kwantar mata da hankali,shikuwa Yaa malam tsayuwar sa yayi awaje baima yiwa motar kallo daya ba,anan bakin airpot din ya dakata harsanda ya same adaidaita sahu snn ya tare shi ya shiga zaune yayi a bayan adaidaita sahun ya buga Wani uban tagumin takaici da izza ta girman kai fuskar Sa a matkr turmushe, mita da bambami kawai yakeyi aransa dan tamkar zaiyi hauka ya zauce haka ya rinkaji acan kasar xuciyarsa,bakin cikin bin umarnin mahaifiyar sa datace masa marmaza ya biyo zaidu dukan su su sameta agida shiyake so ya hallaka sa, shi Allah ya sawwake masa ma ya shiga motar zaidun barema ya hada kafa dasu,in banda bacin rai da konan zuciya Babu abunda yakeji a xuciyarsa,haka
Suka har suka isa kofar gidan yaa malam baice ma kowa uffan ba.
Wani fadi yake yana tsikarar haqwransa da yar tsinke yana takun sa mai cike da nuna alfahari dakansa dayakei yana hura hancin sa cikin tsantsar yanayin bunkasa.

mai gadi ne ya bude gate suka shigo ciki still bai daga idanun sa ya kalle su ba ya Sallame mai adedeta,sashen mahaifiyar sa ya wuce direct sanda ya Wani bangaje labulen ya shigo har tsakar katafaren palon sannan ya doka wata mahaukaciyar sallama da sautinsa kadai ya isa ya ganar da Kai tsananin jahilcin dayake Kan wannan halittar daya shigo.

A lokcin hjy mama tana cikin bayi tana fitsari bata fito ba, Umma hadiexa dake karatun qur'ani akan sallaya ita ta soma tsinkayo sautin muryan san kirjinta ne ya hau bugu ta miqe tsaye a gaggauce,can ya isa har bakin kofar ta bude a hankli ta dada kasa kunnuwanta Jin muryan yaa malam din karara yasa ta juyo cikin sauri,kofar bayi ta je ta dan tsaya cikin rasa abunda zatayi can tace "hajiya mama kamar fa muryan yaa malam nakeji?maganan kawai tayi a Dan birkice dn batada cikakken sanin cewa ko ma anjita caraf saiga hajya maman ta fito durus agaban ta kamar wata fatalwa...
A mugun hargitese ta fito tare da xanin ta a hannunta da alaman ko gama kimtsawa bata yi ba
Ganin daga ita sai yar underwear yasa umma hadiza sauke Kanta kasa ita kuwa sai hamdala take tana kokrin daura zanin tan cikin sauri tace wuce muje da sauri rufaidar mu ta dawo, Alhamdullahi Allah Alhamdullah Allah na gode maka,sai kuma ta barke da Wani sayayyar kuka Jin Hakan ya saka umma hadixa Jin Wani irin sanyi da sabon yanayin kwanciyar hankli a xuciyarta hawayen fargaban ganin yarta da suka cikke mata idanunta already su suka soma gangarowa bisa kuncin ta banda motsi Babu abunda lebbenta yake na tsananin godewa Allah daya nuna mata wannan awanni masu matukar muhimmanci acikin shafukar rayuwar ta Yaune ranar da zata sake Dora idanun ta akan yarta rufaida"..banda hailala da salati Babu abunda take furtawa acikin xuciyarta da bakin ta,cikin sauri hjy mama ta wawushi hijabin ta ta wuce gaba umma hadiza na biye da ita abaya a mugun rikice suka nufo falon

Daga waje kuwa tunda suka sauka a mota yaa sheik ya riko hannun rufaida da kirjinta yake tsananin bugu Dan batasan mezataji aranta inta taji kanta ajikin umman ta ayau ba,Dan tun a jirgi kawu zaidu ya gaya mata Suna Nan gidan sa Suna jiranta ,da mugun dokin hakan aranta wanda shi yasa ta yarda tabiyosa gidan sa Dan ita har Yau gani takeyi kamar kowa yaji abunda ya afku da Ita,za'a ce ta kashe mijin ta ko taci naman mutum wannan maganan na matukar cusa ma xuciyarta da kwakwalta damuwa bana wasa ba

Tafiya kawai sukeyi tana tafe a hankli abayan yaa sheik Jin yadda kirjinta ke  kara tsanan ta bugun sa tamkar zai fado waje,kallo daya zakamasa kasan baiso tahowar su Nan din ayanzu ba,atunanin sa ai yakama abarta ta huta komi sai abisa a hankli,but ya riga ya san dokin ganin ta bazai taba bari subarta ta Dan huta ba,shikuma tausayinta yake ji,duba da long journey da suka sha a jirgi,ga ita kanta rufaidar ba wani karfin kirkine da Ita ba,Sam jikin ta Babu kwari, cikin layi layin ciwon Kai ma take tafiyar ga Wani uban dingishin datakeyi sosai,

SHADE OF RUFAIDAHWhere stories live. Discover now