BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 26
7:am
Anguwar gangareTun bayan ficewar umma hadiza agidan yakumbo take fama da jikin rufaidah wanda Tunda ta farka laulayi kawai takeyi da kyar ma ta Sami tayi sallah tadan kwanta bacci mai Nauyi ya Kara daukarta,Banda juye juye da wangale wangalen cinyoyinta Babu abunda takeyi,har Yau kasarta be dena mata tsami da zugi ba,saidai ata ciki ciki kawai takejin radadin abun, dan Koda taje tsarki ta leka kasarta bata ga komiba sai dan kumburin da wajen yayi,daga Nan bada wani dadewa ba yakumbo ta Sabi mayafin ta itama ta fice ta nufi kasuwa yin musu dan siyayya,dubu sha biyar din da hadizan ta bata ta rabashi gida biyu mai yawan ta boyeshi a gindin setin samiran ta kwalli daya dake tsakar dakin wanda tadanyi jere dashi akas,Wajen masu saida abincin gwari ta nufa direct tadan tarkato musu abunda baza'a rasa ba,yar shinkafar su wanda baifi kwano hudu ba,wake,surfaffen garin masara,da flour,dake ma tanada garin gero da tarkacen sauran ragowar hatsi data samo wajen kale a gida,sai Yan sabulun wanka da wanki da sleepas da Kuma brushi ta hada mata harda man shafawa wanda tasan dai dole Rufaida ta bukace wayannan..
Bayan ta kammala da Nan ta biya har lambun gangare Inda akecema Gidan arha,anan shima ta sissintsinta musu kayan miya da sauran tarkacen su Maggi da manja harda dan kifi da Dan abun sha'awa Abunka da Abincin marar lpya..
Niki Niki ta shigo gidan hannunta dauke da kayan abinci tana tafiya dakyar sabida Nauyi da gajiyar jikin tsufa a kofar daki ta ajesu tayi sallama tare da leka cikin dakin tana mai kallon saman gado,sauke ajiyan xuciya tayi ganin Rufaida Takoma bacci still sai juye juye take da alaman bakin dadin baccin takeyi ba
Kusan minti biyar yakumbo tana tsaye daga wajen cikin rasa ta yadda zata soma tunkarar lamarin rufaida Dan gaba daya yanayin jikin rufaidar na kashe mata jiki..Abunka da believe irin na tsofaffi already ta riga ta gama sawa aranta cewa Rufaida ta riga ta san da namiji by now,ita Sam bata wani gamsu da labrin cewa attempt bane kawai jinsu takeyi aranta tace Wani irin abu kenan namiji zaiyi da jikin rufaida ace haryanzu bata dena dingisawa ba?yarinyar da akace tayi kusan sati a Asibiti?Ance mata wai shigar karfine toh tayaya kenan rufaida zata kufce batare da ta rasa budurcinta ba?,,ita tun jiya da hadiza ta gaya mata abunda ya afku take saka Idonta sosai akan yanayin tafiyar rufaidar tana Kuma lura da Duk Wani motsawarta Wanda har ayanzu bata gamsu da cewa rufaida ta dawo cikin hayyacinta bama bare ajega samun sauki, Kuma tabbas bata cire tsammanin cewa ba a bawa kasarta da jikinta kulawar daya dace ba,yo meye ma asibiti suka iya?ita dama can bata yarda da maganin asibiti ba tafi gane na gida na zallan itatuwa,yo bakaken fatan ma da suka bijire ma na Allah ai yanzu dawowa sukeyi a Hujajan, inaga Kuma ance turawa dama can sume sukasani banda neman kudi da Suna bare har ace sunyi ma rifaida magani?mita kawai take yi aranta Dan Aganinta ko dingishin da Rufaida takeyi aynzu ya isa ya gamsar da kowa yasan cewa bataji ruwan zafin jinya ba.
Bisaga wannan tunanin data dingayi a xuciyarta ta juya ta shiga debar kayan abincin tana kaisu cikin dakin,sanda ta shiryasu tsaf sannan ta taho a gjiye ta zauna bakin gadon kusa daf da rufaida,kallo tabita dashi sannan ta shafa goshin ta daya jike da zufa jin yadda ko inanta ya dau dumi da alaman zafin zazzabin dake jikin tane yake neman tsanantawa,.
Minti biyu bata kara xaune awajen ba rufaida ta soma bude gajiyayyun idanunta data kullesu gam gam suke mata Wani irin Nauyi da duhu kanta na mata Wani irin Azaban ciwo..
Wani malalaciyar ajiyan xuciya ne ya kufce mata ayayin da taja numfashi me qarfi cikin yanayin da bazata iya banbancewa ba, a hankli ta shiga furta Allah acikin zuciyarta tana kokrin samar wakanta nitsuwa
Batayi aune ba taji an dan tallafo kafadun ta,yakumbo tagani tana ta Kallon ta duk tausayinta ya cike kwayar idanunta na tsufa kallo daya zaka mata kasan ta damu sosai,a nutse rufaidar ta maida mata kallo itama, Jin jiri na shirin debarta yasa ta sulale a kasale ta jingina da jikin yakumbo tare da kankameta tana sauke wasu gajiyayyun numfashi dake saukowa daga can kasar xuciyarta a hankli,sun dade a haka batare dasun cewa juna uffan ba harsaida rufaida taji kamar ta Dan samu nitsuwa,idanunta da sukayi Lui sukayi sanyi ta shiga warasu kadan a hankli ta kamo hannu yakumbo ta hada da nata ta rike, cikin sanyin yanayi ta shiga karema lungu da sako na dakin kallo wanda ya zamto mata tamkar mafarki kasancewarta a raye Kuma a Nan kusa da wanda zata taimaketa sabanin kwana biyuncan daya wuce datake kallon mutuwa da azaba agaban ta karara.

YOU ARE READING
SHADE OF RUFAIDAH
Spiritual"Na rasa ni wata irin baqar mujiyace,Duk wanda yake tare Dani saiyayi Gamo da baqinciki acikin zuciyarsa. Na rasa ni wata irin mace ce da bani da albarka Sam Sam saidai ayita kuka Dani".. "life is full of negative and positive numbers but Not once h...