chapter39

780 96 1
                                        


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 39

Acikin kunnenshi ta bude kofar dakin duk da tunani mai nauyi da zuciyarshi takeyi bai hanasa shaqo yanayin shigowartan ba, waje ta nema ta tsaya durus tana kallonsa dan bazata iya cewa dason ranta ta biyo bayansa awannan lokacin datakeji kamar ba a cikin hayyacinta take ba.
Rashin iya bude idanunsa dayayi ya sa wajen ya dauka da wani irin shiru sam Shigowartan bai katse masa tunanin datazo ta iske shi yanayi ba,tun daga ranar auren sa har izuwa yau inyatuna,wasu sukance sukanji kansu kamar a saman gajimare tsabar kwanciyar hankli da farincikin auren su amma shi haryau baisoma jin wannan ba,aure dai yasan yana cikinshi da wacce yake ganin kamar yana so amma bazai iya cewa zuciyarsa a nitse take da aurensan ba shiyasa ma sam ya kasa gane ma kansa bare ma ajega y fahimce matar sa Ai'nau,alot of times in his heart yakanji matukar dana sanin auren ta,saidaii tabbas akwai wani bangare a zuciyarsan datake hanasa tantance komi saiyaji kamar eh dagasken sonta yake yi kuma bazai taba iya rabuwa da ita ba,shidai yasan acikin Rudani yake rayuwar sa Ko ainau ta fahimce shi ko bata fahimshi ba oho,shikadai yasan abunda yake damun sa aransa yanzu.

Ainau dake tsaye kansa bakinta gumm bata iya ko jan numfashi kwararra, kokowa take da fushinta dan kar zuciyarta tayi bindiga ta fashe ta tarwatse bare ajega ta sauke masa tulin ruwan balain datayi dako tsawon kwanaki dominsa na musamman.

Tura yakai bango,in akwai makurar karshe to tabbas haqurinta akanshi yakai yau,yakamata ya fito fili ya gaya mata shin ita mene ne awajen sa dan bata gane meyake nufi da ita ba.

Karkkarfan ajiyar zuciyar daya kufce mata badon tasoba ya tursasa shi adan dole ya bude limsashu kuma gajiyayyun idanunshi wanda suka so suyi luhu luhu tsabar nauyin magananun zuci da zuciyarsan ta dade tanayi ita kadai.

Ainau Tana daf da bude bakinta ya miqe tsaye cikin sauri mai nanike da jarumtar kasaitar sa dake saurin saka yankewar gaba,a nitse ya karaso har gabanta yana kallon figaggiyar nityn data sakan up and down fuskan sa adan daure, cikin wata girmanmen muryansa data fito da yar tashen masifa har yana lullumshe ido yace
"I have had enough of your nonsense A'inau!tunda ke baki da hankali daga yau kar in kara ganin ki awani waje agidan nan da wannan shigar banxan.
,kaiwa nan ya dakata da maganan yay shiru, sannan yaja numfashi game da sassauto da muryan sa kasa kasa yanai mata kallo mai dauke da tsantsar comand da nuna ya isa,araunane ainau ta sadda kanta can kasa,da gefen idonshi ya kara jefo mata wani kallon aransa yana ta mamakin Yanayin ta yace"ohh ok i think is time for u to go park ur things ..zamu koma can gida kawai..
Adan hargitse Tace what?bai kulata ba yana kkrin juyawa yace "u heard me"..

Abbu is already back in nigeria  bazan so yazo nan ya same mu agidan nan ba..ba amfanin zamanki anan.

Yunkurin juya mata baya yake bayan ya kammala furta hakn sai caraf ya tsince ta agabansa a mugun masife, kwayar idanunta ya kalla yaga wai har sun rine sunyi wani rau rau cike da ruwan hawaye tamkar zasu fashe su watso waje.

Wani irin kallon data watso masa saida yasa gaban sa ta dau sautin bugu ya kara maida hanklin sa yana kallon ta dan yaji me zatace ,a zafafe amma bada muryan fada ba tace mishi
"Daga ina kake,Har kadawo ko?yy saurin dauke kansa akanta,ita kuwa kkrinta ta sarkafe kwayar idanunta anashi maybe in ya kalletan zai iya dawowa hayyacin sa yagane metake ciki dashi,dirin hucinta yasa shi lumshe idanunsa kadan snn ya kara budewa ya juyo sai yanzu ma ya tuna cewa ashe bai sanar da ita tafiya mission din dayaje ba,naw he got why she look dis furious aranshi yay wata malalaciyar kwafa shi baiga ma dalili ba,meye ne dan ya tafi bai sanar mata ba,yaga dai bayau aka fara ba,yasan she hates his job so bai wani dara sa da sai ya mata bayani ko yabata hakuri akan dan yaje ba,
aganin sa ainau tafi kowa fahimtar cewa  baya cikin jerin majajen da zasu sanar da kowa abunda ya shafi hurumin aikin su..its a big mission for god sake,dama can metake so yagaya mata mtsww,ackin dakika ya gama ayyana wayannan zantukar aransa shikadai yanai mata kallon batasan meyake mata ciwo ba.

SHADE OF RUFAIDAHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora